Karrama tsohuwar shugabar Liberia da girkin buɗe-baki a Masar cikin hotunan Afrika

.

Asalin hoton, CHRISTOPHER PIKE/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Forbes ta karrama tsohuwar shugabar ƙasar Liberia Ellen Johnson ranar Asabar a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
.

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Mabiya Addinin Islama sun fara ibadar Azumin watan Ramadan bayan ganin wata, kamar yadda ya faru a birnin Cape town da ke Afrika ta Kudu.
.

Asalin hoton, SAYED HASSAN/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kunafa wani abinci ne da ake yi da garin alkama don buɗe baki lokacin Azumin Ramadan a Masar.
.

Asalin hoton, MEHMET EMIN YOGURTCUOGLU/getty

Bayanan hoto, Goggon Biri na hutawa a ɗaya daga cikin gidajen ajiyar dabbobi da ke Uganda.
.

Asalin hoton, ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Bayanan hoto, Kashe gari fasinja sun shiga mota don zuwa Dakar babban birnin ƙasar Senegal.
.

Asalin hoton, ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Bayanan hoto, A Dakar ɗin, riga ɗauke da hotunan jagoran adawa Ousmane Sonko da wanda ya zaɓa a matsayin wanda zai maye gurbinsa Bassirou Diomaye Faye, waɗanda suke tsare gabanin zaɓen da za a gudanar.
.

Asalin hoton, CARMEN ABD ALI/AFP

Bayanan hoto, Mace ta farko da ta tsaya takarar shugabancin ƙasar Senegal, Anta Babacar Ngom yayin da take gaisawa da magoya baya a babban birnin ƙasar ranar Litinin.
.

Asalin hoton, EDWIN NDEKE/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Membobin Cocin Africa Roho Msalaba a Nairobi da ke ƙasar Kenya, su na gudanar da al'adar jefa jariri sama da cafke shi a gaban jama'a.
.

Asalin hoton, MARVELLOUS DUROWAIYE/REUTERS

Bayanan hoto, Wata mai yin takalma, yayin da ta ke yin takalmi a shagonta da ke jihar Lagos ranar Juma'a.