An sayar da dutsen duniyar Mars da ya faɗo a Nijar kan dala miliyan 4.3

A grey-coloured Mars rock sits on podium

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Ana Faguy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 1

Wani dutse na musamman daga duniyar Mars kuma mafi girma da aka taɓa gani a duniyarmu ta Earth, an sayar da shi kan dala miliyan 4.3 a birnin New York na Amurka ranar Laraba.

Dutsen wanda ake kira NWA 16788 na da nauyi 54lb (ko kuma kilogiram 245), kuma yana da kusan tsawon inci 15, a cewar gidan ajiye kayan tarihi na Sotheby's.

An gano shi ne a wani ƙauye da ke Jamhuriyar Nijar a watan Nuwamban 2023. Gidan tarihin ya ce dutsen ya fi na biyu da aka gano girma da kashi 70 cikin 100.

Dutsen meteorite ɓurɓushi ne na duwatsun da suka faɗo sakamakon wucewar tauraruwa mai wutsiya ta sararin dunyar Earth.

Sotheby's ya siffanta dutsen a matsayin baƙi mai launin jaja-jaja kuma "wanda wuya ake samun sa. Kusan dutsen Mars 400 kawai aka taɓa samu a duniyar Earth zuwa yanzu.

"Wannan ne dutsen Mars mafi girma a duniyar Earth. Samun wannan abin a can kuma har a kawo shi nan ba abu ne mai sauƙi ba," in ji Cassandra Hatton, mataimakiyar shugaba a fannin tarihi a cibiyar ta Sotheby's cikin wani bidiyo.

"Ku tuna kusan kashi 70 na duniyar Earth ruwa ne. Saboda haka mun yi farin ciki sosai da wannan ya faɗo a kan dandariyar ƙasa maimakon teku."

Babu tabbas game da hannun da dutsen zai faɗa saboda ba za a bayyana yadda aka yi cinikin ba.

Ƙarin tsarabe-tsarabe sun sa jimillar kuɗin dutsen ya kai dala miliyan 5.3, in ji Sotheby's.

Yayin gwanjon na ranar Laraba, an sayar da ƙwarangwal ɗin wata dabba da aka samu tun a miliyoyin shekaru kan dala miliyan 26, da kuma ƙoƙon kan dabbar Pachycephalosaurus kan dala miliyan 1.4.