Yadda za ku tantance, mura ke damun ku ko Korona?

Lokacin karatu: Minti 4

A wannan lokacin da ake ciki ana batun mura da kuma tari a yawancin wurare.

Amma me ya sa ake samun haka a wannan lokacin? ta yaya za ka san mura ce ko kuma korona - ba wai wata ƙwayar cuta ba, da aka fara gani a farkon wannan shekara.

Don haka ta yaya za ka gane bambancin don kare kanka?

Shin yanayin sanyi ne ke janyo mura?

Har yanzu bincike ya nuna babu takamaimen bayani kan yadda yanayin sanyi ke yin tasiri a jikinmu.

Sai dai yanayin duhu na nufin cewa akwai yiwuwar samun yanayi na ɗumi da kuma zama a cikin gida.

Kuma wannan muhalli ne da ƙwayoyi za su iya watsuwa.

Makarantu suna kasance tamkar wuraren da ƙwayoyi ke yaɗuwa, kuma yara za su iya ɗaukarsu zuwa gida.

Haka batun yake a ɗakunan karatu ga sabbin ɗalibai da suka shiga jami'a - inda haɗuwa tare ke yaɗa cutuka.

Mece ce murar?

Shugabannin hukumar lafiya ta Birtaniya sun fara yin gargaɗi cewa za a iya fuskantar matsanancin mura a bana.

Murar ta zo da sauri ƙasa da wata ɗaya da ta saba zuwa, inda take sauyawa da kuma yaɗuwa.

Har yanzu allurar riga-kafi na aiki kan irin waɗannan mura da ake kira "subclade K".

Shin mura ce ko kuma korona?

Yanayin murar

  • Alamominta na bayyana sannu a hankali
  • Yana shafar hanci da maƙogoro
  • Alama ta farko - jin wani abu a kunnenka
  • Tari mai zafi

Wane lokaci kuma alamomin na:

  • Zuwa nan take
  • Ciwon jijiyoyi, gajiya da tari
  • buƙatar hutu
  • Busasshen tari

Korona

  • Rashin jin ɗanɗano ko wari
  • Amai da gudawa ko ciwon ciki

Yawancin alamomi tsakanin mura da korona na kasancewa har na wani lokaci, a cewar Dokta Oscar Duke.

Sai dai akwai hanyoyi da za ka gane me ke damunka.

Idan mura na zuwa, to tana zuwa ne sannu a hankali.

Zai shafi hancinka da kuma bayan maƙogoro, yayin da wani lokaci kuma baki zai riƙa yin zafi.

Wata alama ita ce jin zugi a kunnenka.

Idan ƙwayar cuta ta ƙara yaɗuwa, za ta kai cikin huhu da janyo yawan tari.

Sai dai, so tari waɗannan alamomi ba su hana mu yin mu'amala ta yau da kullum.

Tun zuwan annobar korona, abubuwa sun ƙara rincaɓewa, inda alamominta suke kama da na mura.

Sai dai wani abu da zai bambanta su shi ne idan korona ce za a daina jin ɗanɗano da kuma wari.

Sannan maƙogoro yana yin tsananin zafi, ga yawaitar amai da gudawa.

Shawara da aka bayar ita ce zama a gida don hutawa da kuma murmurewa.

Sai dai, idan kana ɗauke da wasu cutuka, kamar rashin numfashi yadda ya kamata ko rashin tafiyar alamomi bayan makonni uku, to kada ka yi kasa a gwiwa wajen zuwa ganin likita.

Zan iya taimakon kaina domin zama cikin lafiya?

Jikinmu na da ƙarfin yaƙar ƙwayoyin cuta da kuma wasu cutuka, sai dai za mu iya taimaka masa wajen shan maganin da ya kamata.

  • Paracetamol: Idan ya kasance kana da damar shansa, to paracetamol da ibuprofen abu ne na farko da ya kamata ka sha. Dukkansu suna da kyau wajen taimakawa mura da ciwon kai ya ragu, har da rage raɗaɗin da ake ji.
  • Vitamin C: Ana tunanin cewa wannan yana taimako wajen kare kai daga mura. Sai dai babu kwararan hujjoji kan haka. Abin da ya fi dacewa shi ne komawa cin abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki.
  • Vitamin D: Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ba da shawarar cewa yana da kyau shan Vitamin D saboda alfanunsa wajen kare kai daga mura. Saboda ba a samun isasshen hasken rana a Birtaniya a irin wannan lokaci.

Yaya batun allurar riga-kafi?

Dokta Duke ya ce yana da muhimmanci a karɓi riga-kafi a kowace shekara idan aka samu damar yin haka.

Idan kana da yara waɗanda suka kai shekara biyu ko uku daga Agustan bana, to sun cancanci a yi musu riga-kafi. Yaran da suka balaga kuwa za su karɓi tasu a makarantun su.