Za a yi bikin gwarazan Afrika a birnin Marrakesh na Moroko

Asalin hoton, CAF
Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ta sanar da cewa za a gabatar da bikin kyautar gwarazan Afrika ta 2024 a birnin yawon buɗe ido na Marrakesh da ke Moroko.
An tsara za a gudanar da kyautar ne a ranar 16 ga watan Disambar 2024.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, CAF ta sanar da cewa lokaci ya sake zagayowa.
"Shekara ta ƙara zagayowa. #CAFaward2024. Disamba 16 ga wata a Marrakesh Maroko. Kusa a kalandarku."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wannan ne karo na biyu a jere da ake gudanar da bikin a birnin na Marrakesh, karo na uku kuma da ake yi a Moroko.
CAF za ta tabbatar da lokacin da za a fara kyautar ta 2024 da zarar lokaci yayi.
Wanda ke rike da kambun kyautar ta ɓangaren maza shi ne ɗan wasan Najeriya na gaba, Victor Osimhen.
A ɓangaren mata kuwa takwararsa da Najariya Asisat Oshoala ce ke riƙe da kyautar.
Kyautar tana mayar da hankali ne kan ƙoƙarin da 'yan wasa ke yi a ƙasarsu da kuma ƙungiyoyin da suke bugawa ƙwallo, domin bayar da wannan kyauta mai daraja ta gwarazan Afrika ɓangaren maza da mata ta shekara.











