Juventus na son Sancho, Bournemouth ta yi wa Zabarnyi farashi

Lokacin karatu: Minti 2

Juventus a Serie A na sha'awar ɗanwasan Manchester United Jadon Sancho a wannan bazara yayin da zakarun Italiya - Napoli ke cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗanwasan Ingilan mai shekara 25 wanda ya shafe kakar da ta gabata yana matsayin aro a Chelsea. (Sky Sports, external)

Zarin Liverpool na musayar ƴan wasa bai kai ga neman ɗan wasan Newcastle Alexander Isak, mai shekara 25 ba inda ake ganin za a iya cimma yarjejeniya da ɗan asalin Sweden ɗin nan kusa. (Telegraph - subscription required)

Sai dai kocin Liverpool Arne Slot na zawarcin ɗanwasan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 24. (Talksport)

Guehi zai koma Anfield ne idan ya samu tabbacin cewa zai kasance cikin ƴanwasan sahun farko da za su taka leda a filin wasa. (Sky Sports)

Monaco ta Ligue 1 na zawarcin golan Manchester United da Kamaru Andre Onana. Ƙungiyar tana duba ƙa'idojin yarjejeniya ga ɗanwasan mai shekara 29. (Sky Sports, external)

Idan Onana ya bar Old Trafford, Manchester United za ta karkata ga golan Atalanta ɗan asalin Italiya Marco Carnesecchi mai shekara 24 domin ya maye gurbinsa. (Gianlucadimarzio - in Italian, external)

Manchester City ta shirya sakar wa Ilkay Gundogan marar barin ƙungiyar a wannan bazara yayin da Galatasaray ta Turkiyya ke duba yiwuwar sayen ɗanwasan tsakiyar Jamus ɗin mai shekara 34. (Guardian, external)

Paris St-Germain da ta lashe Gasar Zakarun Turai ta gabatar da tayi karo na biyu kan ɗanwasan Bournemouth Illia Zabarnyi da jumullar kuɗi fam miliyan 55 sai dai ƙungiyar ta kimanta darajar ɗanwasan na Ukraine mai shekara 22 kan sama da fam miliyan 70. (Sky Sports)

Tottenham ta tuntuɓi Bournemouth kan ko akwai sararin sayen ɗanwasan gaban Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25 sai dai ba su kai ga batun kwantiragi ba zuwa yanzu. (The Athletic - subscription required)

Fulham na nazarin zaɓin dawo da Joao Palhinha, mai shekara 29, shekara guda bayan cefanar da ɗanwasan tsakiyar na Portugal ga Bayern Munich kan fam miliyan 48. (Mail, external)

Sunderland ce ta fi yin nisa a zawarcin ɗanwasan Dynamo Kyiv, Vladyslav Vanat, daidai lokacin da rahotanni ke cewa ƙungiyar ta Ukraine na neman fam miliyan 21 kan ɗanwasan mai shekara 23. (Express, external)