Sallar tarawi da mai tallar tufafin kwalliya cikin hotunan Afirka

    • Marubuci, Natasha Booty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zaɓaɓɓun hotuna masu ƙayatarwa na wannan mako daga faɗin nahiyar Afirka da ma wasu wuraren.

Wani mutum sanye da gilashi a wajen bikin alfahari da kasantuwar birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a ranar Asabar.

Asalin hoton, Esa Alexander / Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum sanye da gilashi a wajen bikin alfahari da kasantuwar birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a ranar Asabar.
Wata yarinya yar shekara hudu sanye da kayan al'adar Mardi a ranar Talata a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.

Asalin hoton, Luc Gnago / Reuters

Bayanan hoto, Wata yarinya yar shekara huɗu sanye da kayan al'adar Mardi a ranar Talata a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.
Wasu yara dake fareti a wajen bikin Luanda a Angola a ranar Asabar.

Asalin hoton, Marco Longari / AFP

Bayanan hoto, Wasu yara dake fareti a wajen bikin Luanda a Angola a ranar Asabar.
Taken bikin na Luanda na Angola shine murnar cika shekara 50 da kafuwar kasar Angola.

Asalin hoton, Julio Pacheco Ntela / AFP

Bayanan hoto, Taken bikin na Luanda na Angola shine murnar cika shekara 50 da kafuwar kasar Angola.
Wani mutum riƙe da kan bujimi da aka sassaƙa da katako

Asalin hoton, Hector Quintanar / Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum riƙe da kan bujimi da aka sassaƙa da katako
Masanin tarihi kuma mai zane Olushola Olajobi a lokacin da yake nuna kayan da ya kera daga abubuwan da aka samu cikin shara a birnin Ibadan na Najeriya.

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye / EPA

Bayanan hoto, Masanin tarihi kuma mai zane Olushola Olajobi a lokacin da yake nuna kayan da ya kera daga abubuwan da aka samu cikin shara a birnin Ibadan na Najeriya.
Mai tallar tufafin kwalliya, Florentina Agu, a lokacin da take nuna wasu daga cikin kayan da ta samar a Lagos, Najeriya.

Asalin hoton, Olympia de Maismont / AFP

Bayanan hoto, Mai tallar tufafin kwalliya, Florentina Agu, a lokacin da take nuna wasu daga cikin kayan da ta samar a Lagos, Najeriya.
Omobolaji Oyeleye, matar da ke gudanar da wani kamfani mai zaman kansa na tsaro, tsaye a bakin kofar daya daga cikin wuraren aikinta da ke cikin kasuwar Ikoyi a Lagos.

Asalin hoton, Olympia de Maismont / AFP

Bayanan hoto, Omobolaji Oyeleye, matar da ke gudanar da wani kamfani mai zaman kansa na tsaro, tsaye a bakin kofar daya daga cikin wuraren aikinta da ke cikin kasuwar Ikoyi a Lagos.
Masu sana'ar achaba a birnin Monrovia na kasar Liberia a yayin da suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da matakin da hukumomi suka dauka na haramta sana'ar a birnin.

Asalin hoton, Abdul Bah Jalanzo / EPA

Bayanan hoto, Masu sana'ar achaba a birnin Monrovia na kasar Liberia a yayin da suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da matakin da hukumomi suka dauka na haramta sana'ar a birnin.
Yan kasar Namibia a lokacin da suke bankwana da tsohon shugaban kasar na farko, Sam Nujoma, gabanin rufe shi a ranar Asabar.

Asalin hoton, Siphiwe Sibeko / Reuters

Bayanan hoto, Yan kasar Namibia a lokacin da suke bankwana da tsohon shugaban kasar na farko, Sam Nujoma, gabanin rufe shi a ranar Asabar.
Wata yar kasar Congo sanye cikin tufafi masu kalar tutar kasar a lokacin da yake addu'ar samun lafiya ga Fafaroma Farancis a birnin Rome na Italiya.

Asalin hoton, Tiziana Fabi / AFP

Bayanan hoto, Wata yar kasar Congo sanye cikin tufafi masu kalar tutar kasar a lokacin da yake addu'ar samun lafiya ga Fafaroma Farancis a birnin Rome na Italiya.
A Nairobi babban birnin kasar Kenya, mabiya darikar Katolika yayin gudanar da bukukuwan jajibirin azumin Kiristoci.

Asalin hoton, Simon Maina / AFP

Bayanan hoto, A Nairobi babban birnin kasar Kenya, mabiya darikar Katolika yayin gudanar da bukukuwan jajibirin azumin Kiristoci.
Wata mata a lokacin da take gudanar da sallar tarawi a lardin Gauteng na kasar Afirka ta Kudu a ranar Asabar, rana ta farkon azumin wata ramadan.

Asalin hoton, Robert Ciuccio / AFP

Bayanan hoto, Wata mata a lokacin da take gudanar da sallar tarawi a lardin Gauteng na kasar Afirka ta Kudu a ranar Asabar, rana ta farkon azumin wata ramadan.
Muslimai a fitataccen masallacin Massalikoul Djinane, na Senegal a lokacin da suke buda baki na farko cikin watan Ramadan.

Asalin hoton, Cem Ozdel / Getty Images

Bayanan hoto, Muslimai a fitataccen masallacin Massalikoul Djinane, na Senegal a lokacin da suke buda baki na farko cikin watan Ramadan.
Bullowar rana a ranar Alhamis a madatsar ruwa ta Emmarentia dake birnin Johannesburg, na kasar Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Kim Ludbrook / EPA

Bayanan hoto, Bullowar rana a ranar Alhamis a madatsar ruwa ta Emmarentia dake birnin Johannesburg, na kasar Afirka ta Kudu.
Hoton wani biri dake dajin Bijilo na kasar Gambia a ranar Laraba.

Asalin hoton, Cem Ozdel / Getty Images

Bayanan hoto, Hoton wani biri dake dajin Bijilo na kasar Gambia a ranar Laraba.