Ko ya dace a bai wa Trump lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel?

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na miƙa wa Shugaba Donald Trump wasiƙa

Asalin hoton, Washington Post via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya zaɓi Shugaban Amurka Donald Trump, domin a ba shi kyautar bajinta ta zaman lafiya ta Nobel kamar yadda aka ce wannan shi ne burin da Shugaban Amurkan ya daɗe yana son.

Netanyahu ya ce dalilinsa na zaɓar Trump shi ne : "A yanzu haka da muke magana yana ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a ƙasashe da dama da kuma yankuna.

Firaministan na Isra'ila ya faɗi hakan ne yayin da yake miƙa wa Trump wasiƙar da ya aika wa kwamitin zaɓen.

Ba lalle ba ne Netanyahu shi kaɗai ne ke da wannan ra'ayi domin ko a watan Yuni, pakistan ma ta sanar da cewa tana son ganin an ba wa Trump wannan lamba, tana mai bayar da misali da rawar da ta ce ya taka wajen dakatar da buɗe wuta a rikicinta da India a watan Mayu.

Sai dai wannan ra'ayi ya janyo suka sosai a shafukan sada zumunta da muhawa bayan da Trump ɗin ya kai harin bama-bamai kan cibiyoyin nukiliya na Iran, a washegari.

Kyautar ta Nobel wadda ake ɗauka ɗaya daga cikin lambobin yabo masu daraja a duniya, na ɗaya daga cikin lambobi shida da fitaccen masanin kimiyya, ɗankasuwa kuma mai ayyukan jinƙai Alfred Nobel, ɗan Sweden ya ƙirƙiro.

Kwamitin mutane biyar, wanda majalisar dokokin Norway ta zaɓa shi ne ke zaɓar waɗanda za a ba wa kyautar.

Idan har Trump ya ci wannan lamba, to hakan zai janyo ce-ce-ku-ce sosai da cewa bai cancanta ba.

To amma saboda yadda lamarin ya zama na siyasa, lambar yabon ta zaman lafiya ta kasance cike da taƙaddama fiye da sauran lambobin biyar.

ga shida daga cikin waɗanda aka bai wa lambar da aka yi ta taƙaddama a kan cancantarsu.

Barack Obama

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama

Asalin hoton, AFP

Mutane da yawa sun yi mamaki lokacin da tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya ci kyautar ta zaman lafiya ta Nobel Peace a 2009 - har shi kansa Obaman ma ya yi mamaki.

Shi kansa Obaman ya rubuta a ciki littafin tarihinsa a 2020 cewa - abu na farko da ya ji bayan sanarwar shi ne, ya tambayi dalilin ba shi lambar, ''Saboda me?".

A lokacin watansa tara da fara mulki kawai, saboda haka masu suka suke ganin ya yi wuri a ce ya cancanci samun wannan lamba. Hasali ma wa'adin miƙa sunayen waɗanda za a zaɓa a ciki ya ƙare ne kwana 12 da rantsar da Obama a kan mulki.

A 2015, tsohon darektan cibiyar bayar da lambar - Nobel Institute, Geir Lundestad, ya gaya wa BBC cewa kwamitin da ya yi wannan zaɓin ya yi nadamar yin haka daga baya.

A lokacin mulkin Obama biyu, sojojin Amurka na yaƙi a Afghanistan, da Iraqi da kuma Syria.

Yasser Arafat

Yasser Arafat, da ya samu kyautar a1994 riƙe da hoton tsohon Firaministan Isra'ila Yitzhak Rabin

Asalin hoton, Sygma via Getty Images

An bai wa tsohon jagoran Falasɗinawa lambar bajintar ta zaman lafiya ta Nobel a 1994 tare da tsohon Firaministan Isra'ila na lokacin Yitzhak Rabin da kuma ministan harkokin wajen Isra'ila na lokacin Shimon Peres a kan ƙoƙarin da suka yi kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo (OsloPeace Accords), yarjejeniyar da a shekarun 1990, ta samar da fatan cimma zaman lafiya a rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

Matakin bai wa Yasser Arafat, wannan lamba ya janyo ce-ce-ku-ce a Isra'ila da wasu wurare, musamman ganin cewa Arafat ɗin a baya ya shiga gwagwarmaya da makamai.

Hasali ma hatta a tsakanin 'yan kwamitin zaɓen nasa ya janyo taƙaddama

In fact, Arafat's nomination caused a stir within the Nobel Committee itself.

Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Kare Kristiansen, wanda ɗansiyasa ne na ƙasar Norway ya fice daga kwamitin cikin fushi.

Henry Kissinger

Sakataren harkokin wajen Amurka Henry Alfred Kissinger ya ci kyautar a 1973

Asalin hoton, Gamma-Rapho via Getty Images

A shekarar 1973, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger ya ci kyautar.

Bayar da wannan lamba ga mutumin da yake da hannu a wasu daga cikin manufofin Amurka masu taƙaddama - kamar kai harin bam a Cambodia da goyon baya ga gwamnatocin soji na yankin Latin Amurka masu hallaka jama'a, ya janyo ce-ce-ku-ce.

An bai wa Kissinger wannan lamba da haɗin gwiwa da shugaban ƙasar Vietanam ta Arewa Le Duc Tho, a kan rawar da suka taka a yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a yaƙin Vietnam.

A bisa wannan dalili mutum biyu a kwamitin zaɓen waɗanda ake ba lambar suka ajiye aikinsu saboda rashin yarda da hukuncin ba mutanen biyu.

Bugu da ƙari jaridar New York Times ta yi martani da kiran lambar - Lambar Nobel ta Yaƙi.

Abiy Ahmed

Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed Ali

Asalin hoton, Getty Images

A 2019, an bai wa Firaministan Ethiopia lambar yabon a kan ƙoƙarinsa na sasanta rikicin iyaka da aka daɗe ana yi tsakanin ƙasarsa da maƙwabciyarta Eritrea.

To amma bayan shekara kacal sai aka fara nuna tababa kan cancantarsa da lambar - kan cewa, anya an yi abin da ya dace kuwa?

Ƙasashen duniya sun riƙa sukar matakin da Abiy Ahmed ya ɗauka na tura sojojin ƙasarsa yankin arewacin Tigray.

Matakin ya janyo yaƙin basasa da ya jefa miliyoyin mutane cikin matsalar rashin abinci da magani da sauran abubuwa na jin daɗin rayuwa. Kuma ana ganindubbai sun mutu.

Aung San Suu Kyi

Tsohuwar jagorar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi na magana lokacin da ta karɓi lambar yabon a ɗakin taro na birnin Oslo

Asalin hoton, Getty Images

'Yarsiyasar ta Burma ta samu wannan lamba ne a 1991 saboda fafutukarta cikin ruwan sanyi wajen hamayya da mulkin soji a ƙasar ta Myanmar.

To amma bayan shekara 20 da ba ta wannan lamba sai matar ta samu kanta cikin taƙaddama inda aka riƙa sukarta a kan ƙin fitowa fili da ta yi ta nuna rashin yarda da cin zarafi da kisan tarin al'ummar Musulmi 'yan Rohingya a ƙasar tata - kisan da majalisar ɗinkin duniya ta kira - kisan-kiyashi.

Wasu har ma kira suka yi da a karɓe lambar, to amma dokar bayar da kyautukan shida na Nobel ba ta bayar da damar hakan ba.

Wangari Maathai

Mai fafutukar kare muhalli kuma mai rajin siyasa 'yar Kenya Wangari Maathai

Asalin hoton, Corbis via Getty

Marigayiyar mai raji 'yar ƙasar Kenya ita ce mac ta farko daga Afirka da ta ci wannan lambar yabo ta Nobel a 2004.

Ta samu wannan kyauta ne saboda shirinta na dasa miliyoyin bishiyoyi.

To amma bayan da ta yi wasu kalamai a game da cuta mai karya garkuwar jiki - HIV da Aids, sai aka fara ce-ce-ku-ce a kan ba ta lambar.

Maathai, wadda masaniyar kimiyya ce ta nuna cewa an ƙirƙiri ƙwayar cuta ta HIV ne a matsayin wani makami don ƙarara da baƙaƙen fata.

Ba dai wata sheda ta kimiyya da ta tabbatar da wannan zargi nata.

Wanda ya cancanta aka ƙi ba shi - Mahatma Gandhi

Mutumin da ake girmamawa a India - Mahatma Gandhi ya ƙi cin abinci domin nuna adawa da mulkin Birtaniya

Asalin hoton, Keystone/Getty Images

Wannan lamba ta Nobel ta kuma yi ƙaurin suna a kan ƙin ba wa mutanen da ake ganin sun cancanta a ba su ita.

A ɓangaren zaman lafiya, ana ganin babban misalin mutumin da ya cancanta a ba shi ita, amma ba a ba shi ba , shi ne Mahatma Gandhi.

Duk da cewa sau biyar ana gabatar da sunansa cikin waɗanda za a zaba a ba wa, ɗan siyasar na India wanda ya yi fice a ƙarni na 20 bai taɓa samun wannan lamba ba.

A shekara ta 2006, masanin tarihi Geir Lundestad, ɗan ƙasar Norway wanda shi ne shugaban kwamitin da ke zaɓen waɗanda za a ba lambar ta zaman lafiya ya ce, rashin ba wa Gandhi lambar shi ne babban giɓin da aka samu na wannan lamba ta Nobel a tarihi.