Abin da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Lokacin karatu: Minti 5

Israila da Hamas sun cimma yarjejeniyar da za ta dakatar da yaƙin da ake yi a Gaza, wanda za ta kuma bayar da damar sako ƴan Israila da ake tsare da su da kuma fursunoni Falasɗinawa, a cewar masu shiga tsakani daga Amurka da Qatar.

Yarjejeniyar ce nasarar da ta fi kowanne tasiri a yaƙin da aka shafe watanni 15 ana gwabzawa wanda ya soma a lokacin da ƙungiyar Hamas ta kai hari kan Israila a watan Oktoban 2023.

Mene ne yarjejeniyar ta ƙunsa?

Har yanzu ba a bayyana a hukumance ba bayanan da ke ƙunshe a cikin yarjejeniyar, wadda rahotanni suka nuna cewa ɓangarorin biyu sun amince da ita ba.

Abin da ake ciki a yanzu, samun cikakkiyar yarjejeniyar za ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza, da musayar mutanen da ake tsare da su da kuma fursunoni, da janyewar dakarun Israila da kuma bayar da damar Falaɗinawan da aka ɗaiɗaita komawa gidajensu.

Ƙungiyar Hamas ta kama mutane 251 a lokacin da ta kai hari Isra'ila a watan Oktoban 2023. A yanzu haka tana tsare da mutane 94, duk da dai Isra'ila na ganin cewa mutane 60 ne kawai ke raye.

Ana sa ran Isra'ila za ta saki fursunoni Falasɗinawa su 1,000, wasu daga ciki an kulle su a gidan yari na tsawon shekaru, domin a yi musayarsu da ƴan Isra'ila da ake tsare da su.

Ta yaya yarjejeniyar za ta yi aiki?

Ana sa rai yarjejeniyar za ta yi aiki ne a matakai uku.

Duk da dai ana ganin ɓangarorin biyu sun yarda da yarjejeniyar, akwai kuma buƙatar majalisar tsaro da gwamnatin Isra'ila su amince da ita kafin a iya aiwatarwa.

Firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani ya ce yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga ranar lahadi idan har an amince da ita.

Ga abin da muka fahimta game da yarjejeniyar:

Matakin farko

Matakin farkon zai shafe tsawon makonni shida kuma zai kasance ''cikakken tsagaita wuta ne'', Shugaban Amurka Joe Biden ne ya faɗi hakan a lokacin da yake tabbatar da cimma yarjejeniya a ranar Laraba.

Za a saki waɗanda ake riƙe da su a Gaza da kuma fursunoni Falasɗinawa da ke Isra'ila, kuma ƴan Gaza da suka rasa muhallansu za su fara komawa gida.

''Wani adadi na mutane'' waɗanda Hamas ke riƙe da su, ciki har da mata, da tsofaffi da marasa lafiya, za a sake su domin musayar su da ɗaruruwan fursunoni ƴan Falasɗinu, in ji Biden.

Biden bai tabbatar da adadin waɗanda za a sako ba cikin waɗanda ake riƙe da su a matakin farkon, sai dai firaministan Qatar Al Thani ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa mutanen 33 ne.

Mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila, David Mencer tun a baya ya ce ana sa ran akasarin mutane 33, ba dukansu ba - cikin har da yara- suna nan a raye.

Nan take za a saki mutane uku da ake tsare da su, a cewar wani Jami'i a Falasdinawa, wanda ya shaida wa BBC tun da farko, inda ya ce musayar sauran za ta faru ne cikin mako shida.

A cikin wannan matakin, dakarun Israila za su janye daga dukkanin yankunan Gaza da ke da mutane da yawa, in ji Biden, a yayin da ''Falasɗinawa za su iya komawa unguwanninsu a duk faɗin Gaza''.

Kusan duka mutane miliyan biyu da dubu ɗari uku da ke Gaza an tilasta musu barin gidajensu saboda umurnin ficewa da Israila take bayarwa, da hare-hare ta sama da Isra'ilan ke kaiwa da kuma faɗa ta ƙasa.

Za a kuma ƙara adadin kayan agaji da ake kaiwa Gaza, inda za a bai wa ɗaruruwan manyan motoci damar shiga a kullum.

A baya hukumomin Falasɗinawa sun ce cikakkun tattaunawa kan mataki na biyu da na uku za su fara ne a ranar 16 na tsagaita wutar.

Biden ya ce tsagaita wutar za ta cigaba ''matuƙar za a cigaba ta tattaunawa''.

Mataki na biyu

Mataki na biyu zai kasance "kawo ƙarshen yaƙin na dindindin,'' a cewar Biden.

Za a saki sauran waɗanda ake riƙe da su da suke raye, ciki har da maza, domin musayar su da ƙarin fursunonin Falasdinawa.

Cikin fursunonin Falasdinawa 1000 da ake hasashen Isra'ila ta amince ta saki, aƙalla 190 cikinsu na fuskantar ɗaurin shekara 15 ko fiye.

Wani jami'i a Isra'ila ya shaida wa BBC cewa ba za a saki waɗanda aka yanke musu hukunci saboda kisa ba.

Dakarun Israila za su kuma fice baki ɗaya daga Gaza.

Mataki na uku

Mataki na uku kuma na ƙarshe zai kasance sake gina Gaza - wani abu da zai ɗauki gomman shekaru - da kuma dawowa da duk wasu gawarwakin waɗanda ake riƙe da su da suka rage.

Me ya sa rikicin ya ƙazance?

Ɗaruruwan ƴan bindiga waɗanda Hamas ke jagoranta sun ƙaddamar da harin ba-zato ba tsammani a kudancin Isra'ila, inda suka kai hari kan garuruwa, ofisoshin ƴansanda da kuma sansanonin sojoji.

Aƙalla mutane 1,200 aka kashe yayin da kuma aka yi garkuwa da mutane fiye da 250 waɗanda aka tafi da su zuwa Gaza. Hamas ta kuma harba dubban rokoki cikin Isra'ila.

Isra'ila ta mayar da martani da manyan hare-hare, da farko ta kai hari ta sama, daga bisani kuma mamaya ta ƙasa.

Tun daga nan Isra'ila ta kai hari kan wurare da dama a Gaza ta ƙasa, ta ruwa da kuma ta sama, yayin da Hamas ta kai wa Israila hari da rokoki.

Hare haren Isra'ila sun ɗaiɗaita Gaza, wanda hakan ya kai ga matuƙar ƙarancin abinci, yayin da ake fama wajen kai kayan agaji ga waɗanda ke buƙatar su.

Fiye da mutane 46,700- akasarinsu fararen hula- aka halaka a hare-haren Isra'ila, a cewar hukumar kula da lafiya ta Gaza da Hamas ke jagoranta.