Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Explainers, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 7

Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan wata 15 ana gwabza yaƙi a Gaza.

Firaiministan Qatar - ƙasar da ta zamo mai masaukin baƙi ga tattaunawar tsagaita wutan - Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya ce yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi.

Mataki na farko na yarjejeniyar (cikin kwana 42) dakarun Isra'ila za su janye daga yankuna masu yawan al'umma na Gaza.

Yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Hamas za ta miƙa wa Isra'ila mutanen da ake garkuwa da su a Gaza, yayin da ita ma Isra'ila za ta miƙa wa Hamas wasu Falasɗinawa da ke tsare a Isra'ilar.

Dama tun farko a yau, masu shiga tsakani a birnin Doha na Qatar sun bayyana cewa ana gab da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60.

Sai dai har yanzu akwai sauran abubuwan da ba a samu matsaya a kai ba domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.

Mene ne yarjejeniyar ta ƙunsa?

Amurka ce ta tsara manyan sharuɗɗan yarjejeniyar zaman lafiyar a watan Mayun 2024. Masu shiga tsakani daga ɓangaren Isra'ila da Hamas sun tattauna ba ta kai-tsaye ba a biranen Paris da Alkahira da Doha a inda jami'an diflomasiyyar Qatar da na Masar da kuma Amurka ke aiki a matsayin masu shiga tsakani.

A daren ranar Litinin, shugaban Amurka Joe Biden ya ce an kai ''matakin ƙarshe'' na cimma matsaya kan daftarin da ke da matakai uku kuma ya ƙunshi abubuwan da ya zayyana a watan Mayu.

Mataki na farko: Tsagaita wuta na kwana 42

A cewar jami'in Falasdinawa da ya zanta da BBC, a ranar farko ta tsagaita wuta, Hamas za ta sako wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun ce bayan haka Isra'ila za ta fara janye dakarunta daga yankunan Gaza da ke da yawan jama'a ciki har da mashigar Netzarim.

Bayan mako ɗaya, an bayar da rahoton cewa za a buƙaci Hamas ta sake sakin wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, sannan Isra'ila za ta bai wa mazauna Gaza da suka yi gudun hijira daga gidajensu a arewacin yankin damar komawa gida daga kudanci.

Dole mutanen da ke tafiya da ƙafa su bi ta hanyar da ke bakin teku. Mutanen da ke tafiya da ababen hawa ko amalanke za su iya bi ta tsakiyar zirin Gaza, a kan hanyar da ta yi hannun riga da titin Salah al-Din.

A wannan matakin, sojojin Isra'ila za su ci gaba da kasancewa a mashigar Philadelphi, da ke kan iyakar Gaza da Masar da ke kudancin yankin.

Za a janye wasu sojojin daga sassan yankin a cikin ƴan kwanakin farko na tsagaita wutar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Za a buɗe mashigar Rafah tsakanin Masar da Gaza sannu a hankali domin marasa lafiya da waɗanda suka jikkata su samu damar barin yankin.

Isra'ila za ta ci gaba da kula da yankunan da ke da faɗin mita 800 a gabashi da kuma arewacin Gaza, waɗanda ke da iyaka da Isra'ila.

A wannan matakin, rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar Hamas da kawayenta a Gaza, Palestinian Islamic Jihad, za su saki jimillar mutane 33 da aka yi garkuwa da su.

Ana sa ran cewa Isra'ila za ta saki fursunonin Falasdinawa sama da 1,000, ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa saboda samun su da hannu a kitsa munanan hare-hare. Jami'in Falasdinawan da ya yi magana da BBC ya ce adadin ya kai 1,000.

Rahotanni sun ce ba za a sako mayakan Hamas da suka shiga harin da aka kai Isra'ila a ranar 7 ga Oktoban 2023 ba.

A rana ta 16 ta tsagaita wuta, ana sa ran Isra'ila da Hamas za su fara tattaunawa kan cikakkun bayanai kan matakai na biyu da na uku na yarjejeniyar zaman lafiyar.

Mataki na biyu: Sakin sauran waɗanda aka yi garkuwa da su

A mataki na biyu kuma, za a sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su - sojoji maza da kuma matasan fararen hula- sannan a dawo da gawarwakin waɗanda suka rasu a cikinsu.

Isra'ila ta ce 94 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun kasance a Gaza, inda 34 daga cikinsu ake kyautata zaton sun mutu. Akwai kuma wasu ƴan Isra'ila huɗu da aka sace kafin yaƙin, biyu daga cikinsu sun mutu.

Mataki na uku: Sake gina Gaza

Ana sa ran mataki na uku na shirin tsagaita wuta shi ne sake gina Gaza, inda manyan sassansa suka koma tamkar kufai.

Me ya rage a cimma matsaya a kai?

Babu wata yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas kan mataki na biyu da na uku na yarjejeniyar tsagaita wutan. Za a fara tattaunawa game da wadannan ne a rana ta 16 bayan an tsagaita wuta a matakin farko.

Amma har yanzu akwai batutuwa masu sarƙaƙiya. Ɗaya shi ne: waye zai tafiyar da mulkin Gaza.

Isra'ila ta ƙi barin Hamas ta ci gaba da mulkin Gaza. Har ila yau, ba za ta yarda Gaza ta kasance ƙarƙashin hukumar Falasdinawa (PA), wadde ke kula da wasu yankunan da Isra'ila ta mamaye a gaɓar yamma da kogin Jordan.

Kuma Isra'ila na son ci gaba da riƙe ikon tsaro a Gaza bayan an kawo ƙarshen rikicin.

Duk da haka, tana aiki tare da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa a kan wani shiri na kafa gwamnatin wucin-gadi don tafiyar da al'amura a Gaza yayin da ake yi wa hukumar PA garambawul. Sannan sabuwar gwamnati za ta karbi ragamar mulki a matsayin gwamnatin dindindin.

Hamas dai na fargabar cewa Isra'ila za ta yanke shawarar zamewa daga kulla yarjejeniyar dindindin bayan matakin farko na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Ko da kuwa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da shirin zaman lafiya da Hamas, mai yiwuwa ba hakan ba zai gamsar da sauran ƴan majalisar ministocinsa ba.

Ministan kuɗi na Isra'ila Bezalel Smotrich da ministan tsaron ƙasar Itamar Ben-Gvir sun kasance masu sukar yarjejeniyar.

Smotrich ya rubuta a shafukan sada zumunta cewa yarjejeniyar za ta zama "mummunan bala'i" ga tsaron ƙasar Isra'ila kuma ba zai goyi bayanta ba.

Yaƙin dai ya samo asali ne sakamakon harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda aka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da 251 a Gaza.

Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da farmakin soji a Gaza da niyyar wargaza Hamas.

Ya zuwa ranar 14 ga watan Janairu, ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce sama da mutane 46,640 aka kashe a faɗan.