ASUU: Abin da ya sa aka kasa kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami'oi

Watanni shida ke nan tun bayan da ƙungiyar malaman jami'oi a Najeriya ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani kuma har zuwa yanzu, ba a cimma matsaya tsakaninta da gwamnati ba.

Yajin aikin dai ya durƙusar da harkokin karatu a jami'oin gwamnati tare da tilastawa ɗalibai zaman dirshan a gidajensu sai dai wasu sun fara sana'oin hannu domin rage wa kansu raɗaɗin rashin zuwa makaranta.

Toh ko me yake kawo ƙiƙi-ƙaƙa game da batun cimma matsaya? Wani ƙusa a Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya, Barista Abdullahi Jalo dai ya ce wannan matsala ta yajin aikin tana da tushe - ta samo asali ne tun daga yadda aka ƙulla yarjejeniyar farko tsakanin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo da ƙungiyar malaman jami'oin.

A hirarsa da BBC Hausa, Barista Jalo ya bayyana cewa tun a shekarar 2009 ne aka ƙulla yarjejeniya ta naira triliyan biyu da miliyan ɗari biyar kuma a cewarsa, yarjejeniyar da ta shafi biyan albashi da gyran jami'oi, "an daidaita cewa za a aiwatar da ita domin a samu karatu ingantacce a Najeriya.

"Da aka yi wannan, ya kamata a sa wani bayani yadda idan abin ba zai yiwu ba, za a dubi abin, idan za a samu cikas, za a sake zama a sake duba ta a sake sabuwar yarjejeniya, toh wannan Obasanjo bai yi ba saboda yana gab da tafiya ."

"Na san an yi wannan, har aka zo Ƴar'adua ya hau, har Jonathan ya zo ya hau, har wannan gwamnati ta zo ta gada , wanda yake ba su ne suka yi wannan yarjejeniya ba - wannan ne ya taho har aka zo wannan matsayi da ake ciki, wanda kuɗaɗen da suke nema yana da yawa,"

"Akwai lokacin Jonathan da aka biya malaman jami'a wajen biliyan ɗari biyu da hamsin." in ji Barista Jalo.

Abin da ya kawo cikas wajen aiwatar da yarjejeniyar...

A cewar Barista Jalo, babban abin da ya kawo naƙasu wajen aiwatar da yarjejeniyar shi ne yadda tattalin arziki ya taɓarɓare sannan baya ga ilimi, akwai sauran ɓangarorin da ke buƙatar agaji kamar tsaro.

"Ya kamata mu faɗawa kanmu gaskiya, a wancan lokacin ana sayar da dala kan N180, yanzu dala tana kan N650. Da a ce akwai sharaɗin gyara, da sai a dawo a gyara, ya kamata a sake duba yarjejeniyar domin a yi gyara.

Ya ƙara da cewa, "a yanzu babu wata gwamnati da za ta zo, ta ce za ta ɗauki wannan kuɗi wanda kuɗin nan ya kai kusan triliyan masu yawa a ce za a iya biya a halin da ake ciki."

Mafita

Tsohon ƙusan na PDP ya ce matuƙar ana son a kawo ƙarshen yajin aikin nan shi ne a samu daidaito tsakanin ɓangaren gwamnati da na Asuu.

A cewarsa, kamata ya yi a zauna a sake duba yarjejeniyar da aka ƙulla tun a zamanin Olusegun Obasanjo sannan "ASUU su zama ƴan ƙasa masu haƙuri, yadda za a samu abubuwa su daidaita a samu ƴaƴanmu su koma makaranta a ci gaba da karatu,"

"Saboda gwamnati ba za ta samu yadda take so ba, ASUU ba za ta samu yadda take so ba, sa a haɗu a tsakiya don a samu a danne zuciya a samu maslaha." kamar yadda Barista Jalo ya shaida.