Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kiran gwamnatin Najeriya ta gaggauta shawo kan matsalar lantarki - Gwamnonin Arewa
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta nemi gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gaggawar shawo kan matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a mafi yawan yankin.
Ƙungiyar ta yi kiran ne yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin da suka dabaibaye yankin.
Sama da kwana takwas kenan da jefa yankunan arewa maso yamma, da arewa maso gabas, da wani ɓangare na arewa ta tsakiyar Najeriya cikin duhu sakamakon abin da hukumomi suka ce aikin "maɓarnata ne".
"Ƙungiyar na kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin da suka dace da su gaggauta shawo kan matsalar lantarki da mafi yawan jihohin arewaci ke ciki saboda masu ɓarnata layukan wutar," a cewar wata sanarwar bayan taro da suka fitar.
"Wannan lamari ba wai yana nuna girman haɗarin rashin ababen more rayuwa ba ne kawai, yana kuma fito da buƙatar gina wasu hanyoyin domin faɗaɗa samun wutar da zimmar ƙara yawan lantarkin."
Taron, wanda da aka gudanar na kwana biyu ya samu halartar sarakunan yankin, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad III, da babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar C.G Musa, da sauran su.
Yayin jjawabinsa, shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Gombe ya ce: "Zan fara ne da miƙa jajenmu zuwa ga waɗanda ambaliyar Maiduguri ta shafa, da sauran jihohin arewa, da kuma waɗanda fashewar tanka a Jigawa ta shafa, da kuma waɗanda rashin tsaro ya shafa ta hanyoyi daban-daban.
"Manyan matsalolin da muke fuskanta a yanzu su ne rashin tsaro da garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya da ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi da matsalar almajiri da talauci da rashin aikin yi da yawaitar yara waɗanda ba sa zuwa makaranta, sai dai duk da haka, haɗin kanmu ne babban makaminmu na fuskantar waɗannan matsalolin," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana samun nasara a yaƙi da rashin tsaro da ake yi a yankin.
"Sai dai ya kamata a ƙara ƙaimi ne a kan wannan nasarar da ake samu domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
"Zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a watan Agusta ta zama wata manuniya ga dukkan jagororin arewa. Lallai akwai buƙatarmu ƙara dagewa wajen biyan buƙatun matasan domin hana su shiga harkokin assha. Dole mu fita da hanyoyin rage talauci da samar da aikin yi da sauran abubuwa."
Ya ƙara da cewa, "yanzu haka da muke zaune, jihohinmu na arewa babu wutar lantarki saboda wasu ɓata-gari sun lalata tare da sace wasu turakun lantarkin, wanda hakan ke ƙara bayyana halin da matasan yankin suke ciki. Lallai ana rayuwa cikin matsin tattalin arziki musamman a yankin Arewa. Don haka dole mu yi wani abu cikin gaggawa."
Ya ce arewacin Najeriya na da ƙasar noma, wanda a cewarsa idan aka haɓaka, zai rage talauci da haɓaka tattalin arzikin yankin.
"Idan muna so mu ci nasara, dole mu tallafa wa manoma sannan mu samar da dabarun noma na zamani, sannan mu tabbatar da tsaro a yankin," in ji gwamna Yahaya Bello.