Taron baje-kolin fasaha da tarbar korarren jakadan Afirka ta Kudu a Amurka cikin hotunan Afirka

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata:

+234 Art fair

Asalin hoton, Olympia de Maismont / AFP

Bayanan hoto, Wani matashi ya halarci taron baje-kalin kayayyakin fasaha na +234 Art fair da aka yi a cibiyar Ecobank Pan-African Center da ke Legas a Najeriya a ranar Larabar da ta gabata
Ambasadan Afirka ta Kudu a Amurka Ebrahim Rasool

Asalin hoton, Esa Alexander / Reuters

Bayanan hoto, Korarren Ambasadan Afirka ta Kudu a Amurka Ebrahim Rasool lokacin da ƴan ƙasarsa suke masa tarba ta musamman a birnin Cape Town bayan an sallame shi daga Amurka
Ambasadan Afirka ta Kudu a Amurka Ebrahim Rasool

Asalin hoton, Ibrahim Mohammed Ishak / Reuters

Bayanan hoto, Wasu ƴan ƙasar Sudan suna murnar yadda sojojin ƙasar suka ƙwace iko da birnin Khartoum a titin Port Sudan
A arewa maso gabashin Dimokuraɗiyyar Jamhuriyat Congo kuma Laraba ce ta baƙin ciki, inda masu jimami suka raka gawar tsohon fitaccen mawaƙin Congo, Delphin Katembo Vinywasiki

Asalin hoton, Gradel Muyisa Mumbere / Reuters

Bayanan hoto, A arewa maso gabashin Dimokuraɗiyyar Jamhuriyat Congo kuma Laraba ce ta baƙin ciki, inda mutane da suka yi jimami tare da halartar jana'izar tsohon fitaccen mawaƙin Congo, Delphin Katembo Vinywasiki
Yadda aka jana'izar cikin ƙayatarwa a garinsa a Congo

Asalin hoton, Gradel Muyisa Mumbere / Reuters

Bayanan hoto, Yadda aka jana'izar cikin ƙayatarwa a ƙauyensa a Congo
Spider-Man ɗin Najeriya ke nan. Wannan wani magidanci ne da ke fafatikar kare gurɓacewar muhalli a birnin Osogbo da ke kudu maso yammacin jihar Osun a Najeriya.

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye / EPA

Bayanan hoto, Spider-Man ɗin Najeriya ke nan. Wannan wani magidanci ne da ke fafutikar yaƙi da gurɓacewar muhalli a birnin Osogbo da ke kudu maso yammacin jihar Osun a Najeriya.
Magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal suna farin cikin nasarar Senegal kan Togo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a filin wasa na Abdoulaye Wade da ke Diamniadio.

Asalin hoton, Patrick Meinhardt / AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal suna farin cikin nasarar ƙasarsu a kan Togo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a filin wasa na Abdoulaye Wade da ke Diamniadio.
A ranar Lahadin makon jiya, sabon shugabar kwamitin gasar Olympic ta isa filin jirgin Robert Mugabe da ke birnin Harare na ƙasar Zimbabwe

Asalin hoton, Philimon Bulawayo/ Reuters

Bayanan hoto, A ranar Lahadin makon jiya, sabon shugabar kwamitin gasar Olympic ta isa filin jirgin Robert Mugabe da ke birnin Harare na ƙasar Zimbabwe
A Afirka ta Kudu, wasu suna kwatan jaruman shirin Michael K a lokacin da suke gwajin shirin Life & Times na Michael K a birnin Johannesburg a ranar Wednesday.

Asalin hoton, Wikus De Wet / AFP

Bayanan hoto, A Afirka ta Kudu, wasu suna kwaikwayon jaruman shirin Michael K a lokacin da suke gwajin sake shirin Life & Times na Michael K a birnin Johannesburg a ranar Wednesday.