AFCON 2025: Nigeria da Tunisia sun yanki tikitin shiga gasar baɗi

Lokacin karatu: Minti 2

Najeriya wadda ta taɓa lashe kofin nahiyar Afirka har sau uku tana cikin ƙasashe biyar da suka samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025 a zagayen kusa da na ƙarshe da aka buga ranar Alhamis.

Ƴan wasa 10 na Tunisia sun zura ƙwallo a minti na 93 a wasan da suka yi nasara kan Madagascar da ci 3-2 sannan kuma suka kafa tarihi a gasar inda za su buga gasar a karo na 17 a jere.

Gabon da Afirka ta Kudu da Uganda duk sun samu nasu tikitin ba tare sun take wasa ba bayan da sauran sakamakon wasannin rukunan suka dace da abin da suke buƙata.

Nasarar da Libya ta samu akan Rwanda da ci 1-0, ya sa Najeriya ta samu tabbacin ta zama ta ɗaya a rukunin D tun ma kafin a fara wasansu da Benin.

Victor Osimhen ya zura ƙwallo a raga yayin da Super Eagles ta yi kunnen doki da ci 1-1 – sakamakon da ke nufin Benin da Rwanda da Libya duk za su buga wasannin ƙarshe na rukuni da damar zuwa gasar a Morocco.

A halin da ake ciki dai fatan Ghana na neman shiga gasar na nan daram bayan da Sudan ta sha kashi a gidan Nijar da ci 4-0, waɗanda suka farfaɗo da nasu yaƙin neman tikitin.

Ghana wadda ta lashe gasar ta Afcon har sau huɗu yanzu ya zame mata dole ta doke Angola wadda ta riga ta samu nata gurbin a Luanda ranar Juma'a domin ci gaba da farautar tikitin zuwa gasar ta 2025.

Ƙasashen da suka kama hanyar zuwa gasar baɗi

Ya zuwa yanzu ƙasashen da suka samu tikitin fafatawa a gasar ta baɗi a Morocco sun haɗa da:

  • Morocco
  • Algeria
  • Angola
  • Burkina Faso
  • Cameroon
  • DR Congo
  • Egypt
  • Equatorial Guinea
  • Gabon
  • Ivory Coast
  • Nigeria,
  • Senegal,
  • South Africa
  • Tunisia
  • Uganda

Sakamakon wasannin da aka fafata ranar Alhamis

Madagascar 2-3 Tunisia (Rukunin A)

Lesotho 1-0 Central African Republic (Rukunin B)

Rwanda 0-1 Libya (Rukunin D)

Benin 1-1 Nigeria (Rukunin D)

Equatorial Guinea 0-0 Algeria (Rukunin E)

Niger 4-0 Sudan (Rukunin F)

Sudan ta Kudu 3-2 Congo-Brazzaville (Rukunin K)

Burundi 0-0 Malawi (Rukunin L)

Burkina Faso 0-1 Senegal (Rukunin L)