‘Matsin rayuwa ya tursasa mini sakin uwargidata don samun saukin dawainiya’
Daga Halima Umar Saleh, BBC Hausa, Abuja

"Ba don ba na sonta ba, ba don na gaji da zama da ita ba, na sake ta ne kawai don samar wa kaina sauki daga halin tsadar rayuwar nan da muka samu kanmu a ciki," a cewar Amiru Sani, wani magidanci a jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.
Mutumin mai shekara 27, ya shaida wa BBC cewa ya saki uwargidansa a lokacin da yake neman mafita kan matsin tattalin arzikin da ya shiga sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
Mutane da dama ne a fadin duniya ciki har da a kasashe irin su Birtaniya da Amurka da Jamus da Faransa, ke kokarin fitar da hanyoyin rage kashe kudade wajen sayen abinci da kayan amfanin yau da kullum don taimakon kansu, a yanayin da duniya ta samu kanta a yanayi na tsadar rayuwa.
Najeriya ma tana cikin kasashen da al'ummarta ke fama da wannan lamari.
Sai dai baya ga dalilai kamar na tasirin annobar cutar korona da yakin Ukraine, ƙwararru na ganin rashin tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa masu kyau na daga cikin abubuwan da suka ƙara jefa Najeriya cikin wannan yanayi.
A wani tsarin jin ra'ayin jama'a da BBC ta nema dangane da tsadar rayuwa a fadin duniya, kusan mutum 400 ne suka aika wa BBC Hausa ra'ayoyinsu da labaran halin da suka shiga sanadin lamarin a Najeriya.
End of Wasu labaran masu alaka da za ku so ku karanta
Zaƙi da maɗacin auren mace fiye da ɗaya
Shekara uku zuwa hudu da suka gabata a lokacin Amiru Sani yana da mata daya, amma sai ya ga abin da yake samu a wata yana isarsa yin duk hidimominsa da iyalinsa har ma ya yi na wasu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amiru wanda ma'aikaci ne a wani gidan mai a garin Dandume, kuma albashinsa ya kai N15,000 a wata, ban da wasu kudaden da yake samu a 'yan buge-bugensa, sai ya ga zai ma iya ƙara aure tare da riƙe matan biyu ba tare da aljihunsa ya girgiza ba.
Wasu maza a arewacin Najeriya na ƙara aure ko da kuwa ba su da makudan kuɗin da za su yi hakan a wadace.
Ba a dauki lokaci da yin auren ba sai ya samu matsala da matarsa ta farko har ya sake ta. Amma da yake saki ɗaya ne, manya sun shiga lamarin an daidaita ya mayar da ita a watan Agustan 2021.
Ckin rashin sa'a tun daga farkon shekarar nan ta 2022 sai abubuwa suka fara rincaɓe masa, ta yadda abin da za su ci shi da iyalan nasa ya fara neman gagararsu.
"Ba wai aikina na rasa ba. A hankali ne rayuwa ta fara tsada, lamurra suka rincaɓe min ta yadda abin da nake samu na kashe wajen hidimar iyalina a da, ya zama kudin tamkar takardu nan da nan sun ƙare ba tare da na sauke dukkan nauyin da ya hau kaina ba," in ji Amiru.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai kamar yadda alkaluma suka tabbatar, an fara fuskantar matsalar tsadar rayuwa ne a Najeriya tun a shekarar 2019, amma ta fara ƙamari ne a shekarar 2020 lokacin annobar korona.
Lamarin da masu suka ke dangantawa da gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen kasa fitar da matakan inganta tattalin arzikin kasar, duk kuwa da cewa hakan na daga cikin alkawuran da ya dauka tun a yaƙin neman zaben da ya yi nasara a karon farko, wato 2015.
Sai dai a nata bangaren, gwamnatin ta sha cewar tana iyaka kokarinta domin ganin abubuwa sun kyautatu a fadin kasar.
Dokoki
Amiru ya ce ba niyyarsa ba ce rabuwa da kowacce daga cikin matansa, amma yanayi da faruwar abubuwa da dama suka sa dole ya shimfida wa matan wasu dokoki da ya ce ko dai su bi ko kuma duk wacce ta ƙetare to a bakin aurenta.
"Ga halin yau na tsadar rayuwa ga iyali kullum cikin son fitina da ɗaga min hankali bayan ina ta fafutukar yadda za mu rayu cikin mutunci.
"Da na ga lamarin nasu babu sauki sai na saka dokoki ciki har da cewa duk wacce ta fara takalar wata da rigima ko kuma mace ta fita ba izinina to a bakin aurenta.
"Na yi hakan ne don duk wacce na kama da laifi to gara na sallame ta don na sama wa kaina sauƙi biyu, da na kashe kudi da na tashin hankali," kamar yadda Amiru ya shaida min a waya.
Tsautsayi an ce ba ya wuce ranarsa, rannan sai uwargida ta ƙetare waɗannan dokoki na Amiru, ciki har da sanya ƙafa ta fice daga gidan ba da izininsa ba.
Amiru bai ɓata lokaci ba wajen tabbatar da hukunci kan ƙetare sharuɗɗan da ya gindaya.
"Har ga Allah ba wai ba na son matata ba ne, kawai dai na ga matsalolin sun yi yawa ne, ga na tsadar rayuwa ga na rashin zaman lafiya, kawai sai na sake yi mata saki ɗaya, igiyar aurenmu ta zama saura ɗaya kenan.
Uwargidan Amiru tana da ɗa ɗaya da shi, wanda ya karɓe ya kai wa mahaifiyarsa riƙo. Ita kuma amarya sau biyu tana haihuwa 'ya'yan na mutuwa.
Ya ce duk da dai ya kan ji kewarta da ta ɗansa a wasu lokutan, amma bai shirya mayar da ita dakinta ba, duk kuwa da cewa iyayenta da ita kanta suna ta yi masa sintirin a yi kome.
"Na gaya mata iyakar gaskiyata cewa idan na mayar da ita a yanzu, ɗaukar dawainiyarta zai min wahala, ba lallai na dinga tabbatar da adalci ba.
"Ba na so na zalince ta ta hanyar tauye hakkokinta da suka rataya a wuyana shi ya sa na ga gara kawai na haƙura da mayar da ita," ya nanata.
Ba inda albashina ke kai ni yanzu

Asalin hoton, Getty Images
Magidancin ya ce a naira dubu goma sha biyar ne albashinsa da sauran 'yan kudaden da ke shigo masa, a yanzu haka da mace dayar ma ko rabin wata ba sa kaiwa.
Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 22 cikin 100 a watan Yuli, kuma 'yan kasar na kashe kashi 59.1 cikin 100 na yawan kuɗin da suke samu a wajen sayen abinci kawai," kamar yadda hukumar kididdiga ta fada a wani rahotonta.
Amiru mai kwalin difloma a karatun boko, ya ce bayan nauyin matarsa daya a yanzu, akwai na mahaifiyarsa da ɗansa da ke hannunta duk a kansa.
"Gashi ina so na ci gaba da karatuna a matakin digiri, amma ba ma zan iya ba saboda nauyin zai sake min yawa", ya jaddada.
Na yi kokarin tuntubar matar Amiru don jin ko yaya ta ji da sakin da aka yi mata don ana fargabar ci gaba da daukar nauyinta, amma hakana ba ta cimma ruwa ba.
Sai dai tsohon mijin nata ya tabbatar min har yanzu ba ta yi wani auren ba, kuma daga farko ba ta san cewa sharuddan da ya sanya don yin saki, ya yi ne da nufin lalubo hanyar ragewa kansa wahala ba.
"Sai daga baya ta gane dalilin. Saboda ta yi ta roƙona na mayar da ita dakinta amma na gaya mata cewa ba zai yiwu ba don a yanzu ba ni da ƙarfin riƙe ta," ya ce.
Amma magidancin ya ce yana fatan idan har abubuwa suka warware samunsa ya karu, to la shakka zai mayar da ita dakinta.
"Idan dai har zuwa lokacin da na samu budi ba ta yi wani auren ba to zan koma mu daidaita don ina son ta. Kuma yanzun ma ba wai gaba muke yi ba, muna gaisawa idan an hadu."
End of Karin labaran da za ku so ku karanta

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya, mafi yawan mutane masu matsakaicin hali a jihohin arewacin kasar shinkafa ce abincinsu.
Amma ga marasa ƙarfi irin Amiru waɗanda su ne suka fi yawa, sun fi cin abinci dangin su gero da masara da dawa, wadanda a da ba sa yi wa talaka wahalar samu.
A yanzu kuwa, irin wannan abinci na neman ya gagari masu ƙaramin ƙarfin saboda tsadar da suka yi. Wata matsala da ta sake uzzura lamarin ita ce ta rashin samun isasshen amfanin gona.
Hakan na faruwa ne sakamakon matsalar rashin tsaro inda ayyukan 'yan bindiga da suka addabi manoma a yankunan karkara har suke hana su noma tare da kashe su.
Wannan rashin tsaro na ayyukan 'yan bindiga da masu satar mutane don kudin fansa sun fi addabar jihohin arewa maso yammacin Najeriya, ciki har da Katsina, jihar da Amiru ke zaune.
Farashin kayayyakin abinci da na amfani sun nunka a cikin shekaru biyu da suka wuce inda hukumomi na kasa da kasa kamarsu bankin lamuni na duniya International Monetary Fund da Babban Bankin Duniya World Bank sun nuna cewa talauci ya karu sosai a tsakanin ‘yan Najeriya.
A yayin da tasirin annobar korona ya sanya mutane masu matsakaicin samu a faɗin duniya shiga halin tasku na tsadar rayuwa, gwamnatoci kuwa suna jadda cewa sun duƙufa don samo mafita.












