Yadda karin kudin dizel ya jefa ‘yan Nijar cikin kunci

Asalin hoton, Others
'Yan Jamhuriyar Nijar sun fara nuna damuwa bayan da gwamnatin kasar ta kara kundin man dizel.
Karin ya shafi farashin kayayyaki da dama lamarin da ya jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali.
Gwamnatin kasar ta kara kudin man na dizel da kashi 10.
Yaki tsakanin Rasha da Ukraine ya shafi fitar da man dizel zuwa kasashen duniya wanda kuma hakan na daga cikin ababen da suka kara farashin.
Sai dai ita gwamnatin cewa take ba da sonta ba ta kara kudin man amma kuma za ta duba matakan magance matsalar hauhawar farashin kayayakin.
‘Yan kasuwa na tsauwala farashin kayayyki ba bisa ka’ida ba’
Shugaban kungiyar Muryar Talaka a kasar, Nasiru Sa’idu, yace karin farashin ya jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin hali.
Ya dora laifin hauhawarar farashi kan ‘yan kasuwa yana mai cewa hukumomi za su tattauna da su domin shawo kan matsalar.
"An bai wa ministocin Kasuwanci da na Sufuri damar su tattauna da ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyin fararen-hula saboda daidaita kayan abinci da ‘yan kasar za su iya saya," in ji Nasiru Sa’idu.
Shugaban kungiyar ta Muryar Talaka ya kuma kira ga ‘yan kasuwar da cewa su yi duk abin da ya kamata domin daidaita farashi da kuma daina daga shi ba tare da hujja ba.
‘Wannan kari ya zama dole’
Minista Kassim Mukhtar, shugaban jam’iyyar CPR Inganci kuma mamban kawancen jam’iyyu masu mulki ya ce karin ya zama tilas.
Ya ce: "Masana sun ce kamfanin mai na kasarmu da kuma kamfani da ke tace mai za su iya rufewa idan ba a dauki mataki ba sannan matsaloli za su dabaibaye kasar wanda zai saka ta kara farashin sauran abubuwa har ma da na wutar lantarki," a cewar Kassim Mukhtar.
Har ila yau, Kassim Mukhtar ya yi kira ga ‘yan kasar na cewa su taimaka wa gwamnati don ganin ‘yan Nijar sun samu sa’ida da kuma yin rayuwa ingantacciya.
Shi kuma wani shugaban kungiyar FASCN, mai fafutukar kare hakkin ‘yan kasa, Alhaji Idi Abdu ya ce suna son shugaban kasar ya dauki matakai da ya kamata da kuma tabbatar da cewa ‘yan kasuwa suna bin dokoki da gwamnati ta gindaya musu.
Nijar mai arzikin ma'adinin Uranium, na cikin kasashen da ke fama da talauci a duniya.











