Abin da ƙaruwar hauhawar farashi da kashi 19.64 ke nufi ga ƴan Najeriya

Asalin hoton, JELILAT OLAWALE
Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce hauhawar farashi ta ƙaru a ƙasar da kashi 19.64 cikin 100 a watan Yulin 2022.
Wannan ita ce hauhawar farashi mafi yawa da aka taɓa samu a ƙasar tun shekarar 2005 - shekara 17 da suka wuce.
Yawan ya wuce wanda ƙasar ta samu a watan Yuni na kashi 18.6 cikin 100.
An samu bayanan hauhawar na baya-bayan nan ne ta yin la'akari da ma'aunin farashin kayan masarufi da NBS ta fitar.
Amma wani ƙwararre kan harkokin tattalin arziki ya ce wannan sabon rahoton na NBS na nuna cewa ƙasar tana cikin matsala.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
'Lamarin ya munana'
Dr. Muda Yusuf, shugaban cibiyar bunƙasa harkokin kasuwanci a Najeriya ya ce abin da wannan rahoto yake nunawa shi ne rayuwa na ƙara tsada.
Ya ce talakawa za su ƙara talaucewa "saboda tsananin tsadar kayayyaki da hauhawar farashi."
Ƙwararren ya ce rahoton na nuna cewa ya kamata mutane su farga su gane halin da ake ciki a Najeriya ya wuce hankali."
"Farashin kayayyaki ya ruɓanya a Najeriya a shekara ɗaya da ta gabata.
"Kun dai sa irin wahalar da mutane ke sha wajen fafutukar neman abinci.
"Wannan kaso 19.64 cikin 100 ɗin na nuna cewa lallai al'amura sun lalace sosai," in ji shi.
Yusuf ya ƙara da cewa "Lamarin ya munana. Mutane da yawa abinci yana musu wahalar samu saboda hauhawar farashi."
Me ya jawo hauhawar farashin?
Ƙwararre kan harkar tattalin arzikin ya ce wannan ƙaruwar hawan farashin zai yi mummunan tasiri a kan mutane.
Shugaban cibiyar bunƙasa harkokin kasuwancin ya lissafa waɗansu dalilai da ya ce su suka jawo matsalar tattalin arziki.
"Kun san me ake nufi ai idan aka ce da ƙyar mutane ke samun abin da za su ci."
- Matsalar rashin tsaro ya taimaka wajen jawo hauhawar farashi
- Tsadar lantarki da man fetur da ake amfani da su wajen sarrafa abinci da sauran kayayyaki
- Tsadar kuɗaɗen waje
- Gaza samar da kuɗaɗen da za a cike wasu giɓin tattalin arziki daga Babban Bankin Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ya yi bayanin cewa "Matsalar tsaro ta sa mutane ba sa iya zuwa gona. Mutanen da ke samar mana da abin da za mu ci suna can a sansanonin gudun hijira saboda hare-haren da ake kai musu.
"Shi kuwa tsadar lantarki da man fetur da ake amfani da su wajen sarrafa abinci da sauran kayayyaki na sa mutane suna kashe fiye da kuɗin da suke samu.
Sannan ga tsadar man fetur da dizel da man jirgi.
"Tsadar kuɗaɗen ƙasashen waje ma a wajen musaya wata babbar matsalar ce da ke durƙusar da darajar naira," ya ce.
Me ya kamata gwamnati ta yi?
Dr. Muda Yusuf ya ce ya kamata gwamnati ta saka ido a kan harkar tattalin arzikin nan.
"Ba abin da gwamnati take yi, kuma jagoran lura da harkokin tattalin arzikin ƙasar mataimakin shugaban ƙasar ne da kansa.
"Shi ma shugaban tawagar gyaran tattalin arzikin Doyin Salami kamar ba ya nan."
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta dinga sauraron abin da ƙwararru suke cewa da shawarar da suke bayarwa.
"Gwamnati ta tattara mutanen da suka fahimci wannan batun. Wataƙila ma shugaban ƙasa bai san halin da ake ciki ba," ya ce.
Akwai waɗanda suka ƙware a fannin tattalin arziki a Najeriya da za su iya samo mafita ga matsalar.
Amma ƙwararren ya ce matakin farko na magance matsalar shi ne a fara magance matsalar rashin tsaro.











