Shin China ce ke da riba a rikicin Indiya da Pakistan?

Shugaban Pakistan Shehbaz Sharif na gaisawa da shugaban Chana Xi Jinpin suna murmushi a gaban tutocin ƙasashen biyu.

Asalin hoton, X/Shehbaz Sharif

Bayanan hoto, Shugaban Pakistan Shehbaz Sharif na gaisawa da shugaban Chana Xi Jinpin suna murmushi a gaban tutocin ƙasashen biyu.
    • Marubuci, Anbarasan Ethirajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, South Asia Regional Editor
  • Lokacin karatu: Minti 7

Rikicin na kwana huɗu da ya ɓarke tsakanin ƙasashen Indiya da Pakistan a wannan wata na Mayu, ya ƙare bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta – amma a yanzu ga alama ba ma'aikatar tsaron Chana ce za ta ciri tutar samun nasara ba.

Rikicin baya-bayan nan ya soma ne a ranar 7 ga watan Mayu lokacin da ƙasar Indiya ta ƙaddamar da abin da ta kira fatattakar "matattarar 'yan ta'adda" da ke cikin ƙasar Pakistan a wani matakin mayar da martani ga kisan gillar da aka yi wa mutum 26 waɗanda galibin su 'yan yawon buɗe ido ne da masu tayar da ƙayar baya suka yi a garin Pahalgam a ranar 22 ga watan Afrilu.

An kashe galibin su a wani kwari da ke yankin Kashmir a gaban iyalansu. Indiya ta zargi Islamabad da hannu a taimakawa ƙungiyoyin ta'addanci da ke da hannu a kisan, zargin da Pakisatan ɗin ta musanta.

Bayan da Indiya ta mayar da martani ta hanyar harba roka zuwa Pakistan - a wani abin da ta kira na ramuwa, hakan ya haifar da yaƙi tsakanin ƙasashen biyu, inda suka harbawa juna rokoki da kai farmaki da jiragen yaƙi da ma jirage marasa matuƙa.

Rahotanni sun bayyana cewa Indiya ta yi amfani ne da jiragen da yaƙi ƙirar Faransa da Rasha, yayin da Pakistan kuma ta yi amfani jiragenta samfurin J-10 da J-17 da ta samar da haɗin kai da ƙasar Chana. To sai dai sassan biyu dai sun musanta shiga harabar juna inda suka ce sun harba makamansu ne daga nesa.

Islamabad ta yi iƙirarin cewa jiragen yaƙinta sun harbo aƙalla jiragen Indiya shidda, ciki kuwa har da sabbin da Indiya ta saya daga Faransa na yaƙi ƙirar Rafale. Abin da har yanzu Delhi ba ta musanta wannan kalami ba.

Lokacin da wakilin BBC ya tambayi Air Marshal AK Bharti na rundunar sojojin saman Indiya a makon jiya akan ko me zai ce, sai ya ce, " ai fafatawa ta gaji samun faɗuwa" , amma ya ƙi yin cikakken game da wannan iƙirarin cewa Pakistan ta kakkaɓo jiragen Indiya.

"Ai mun samu nasarar akan muradin da muke son cimma, kuma duka matuƙa jiragenmu sun da gida" in ji shi.

Indiya dai ta ce ta kashe "aƙalla 'yan ta'adda 100" yayin da ta ke son ai farmaki akan maɓoyar dakarun Lashkar-e-Taiba and Jaish-e-Mohammed da ke da sansani a Pakistan.

Har yanzu dai babu takamaiman bayanan dukan abubuwan da suka faru a fagen daga lokacin fafatawar. Sai dai wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa an samu rahotannin faɗuwar jiragen saman yaƙi a yankin Punjab da Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya kusan a lokaci ɗaya lamarin ya faru, kuma har yanzu gwamnatin Indiya ba ta ce kome akan waɗannan rahotanni ba.

Dakarun sojin saman Pakistan a tsaye kusa da jirgin yaƙi samfurin Rafale a lokacin wani atisayen haɗin gwiwa na 'Cope India 2023' a helkwatar sojin saman da Kalaikunda, mai nisan kilomita 170 a yamma da birnin Kolkata a ranar 24 ga watan Afrilun 2023.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pakistan ta yi iƙirarin harbo ɗaya daga jiragen yaƙin Indiya samfurin Rafale
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani rahoton kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ruwaito wasu jami'an Amurka na cewa akwai yuwar Pakisatan ta yi amfani da jiragen yaƙin da Chana ta ƙera samfurin J-10 domin ƙaddamar da farmaki akan jirage yaƙin Indiya. Duk da ƙasar Pakistan dai ta bayyana cewa ita ce ta samu galaba a wannan gajeren yaƙin da ta fafata tsakaninta da Indiya bayan da ta yi amfani da makaman da Chana ta samar, abin da ƙwararru ke bayyanawa da cewa wani gagarumin ci gaba ne ga ma'akatar tsaron Chana, duk da an samu waɗanda ke da tababa akan wannan batu.

Wasu daga cikin waɗannan ƙwararru sun ce masana'antar makamai ta chana na samun bunƙasa sakamakon ci gaban fasahar zamani na AI da ta ke da, suna kwatanta hakan da abin da ya faru a watan Janairun wannan shekara, lokacin da fasahar ta AI da Chana ta yi amfani da ita ta girgiza manyan kamfanonin Amurka, musamman .

Zhou Bo wani babban jami'in kanal na rundunar tsaron ƙasar Chana mai ritaya, ya shaidawa BBC cewa " Idan aka zo maganar masana'antar makaman Chana to ta ƙware a fannin tallata amfani da jiragen sama a fagen yaƙi. Sai zuwa yanzu a baya Chana ba ta da damar gwada wannan ƙwarewar da ta ke da ita a fagen yaƙi".

Wani mai sharhi akan lamurran da suka shafi Chana da ke zaune Beijing, ya ce idan aka kwatanta sakamakon na nuna cewa, "Chana na da wasu tsare-tsaren da suka fi na kowa". Misali kamfanin ƙera jiragen sama na Avic Chengdu wada ke samar da jiragen yaƙi irin su J-10 ya samu bunƙasar da ta kai ta kashi 40 cikin ɗari a makon da ya gabata bayan da ya yi zarra a lokacin yaƙin da ya gudana tsakanin Indiya da Pakistan.

Duk da haka wasu ƙwararrun kuma na ganin ya yi wuri a iya bayyana makaman Chana a matsayin gagararru.

Farfesa Walter Ladwig daga Kwalejin Landan, ya ce an yi gaggawar bayyana ko jiragen Chana ne suka yi fi na Indiya zama ƙwarewa musamman ma idan aka kwatanta su da Rafale.

"A tsarin aikon soji, kana iya cin galabar ta hanyar kai hari ga abokan gaba ta sama. A maimakon haka, ba wai dakarun sojin saman Indiya na da manufar takalar sojojin Pakistan ba ne ta hanyar mayar da martani. in ji shi.

Mista Ladwig na da ra'ayin cewa an ba matuƙa jiragen saman Indiya umurnin su tuƙa jiragen duk kuwa da cewa na'urorin tare makamai na Pakistan na kan aiki kuma jiragensu tuni suna shawagi. Ba a kuma ba sojin saman Indiya cikakken bayani game da yanayin farmakin ko tsarin yadda take tafiyar da hari ta sama ba.

Ita kanta Chanar ba ta yi wani bayani game da waɗannan rahotannin da aka yi ta yaɗawa game da harbo jiragen saman yaƙi na Indiya ba, cikin su har da samfurin Rafale. Amma wasu rahotannin da ba a kai ga tabbatarwa ba akan yadda jiragen ƙirar J-10 suka kakkaɓo makaman na ƙasashen sun haifar da murna tare da jan hankalin kafafen sada zumunta na Chana da ke bayyana hakan a matsayin babbar nasara.

Carlotta Rinaudo mai bincike ne ɗan ƙasar a ɓangaren tsaro, ya ce kafafen sada zumunta na na Chana sun yayata labarin da ya ke ya shafi ƙasar ne duk abu ne mai wahala a iya tantance sahihancin duka saƙonnin.

"A yanzu dai hasashe ya fi tasiri fiye da zahiri. Idan muka kalle shi a haka, to zamu iya cewa Chana ce wadda ta yi galaba" in ji shi.

Ga Chana kuma, Pakistan na da tsare-tsare tana kuma da ƙarfin tattalin arziki. Ta kashe fiye da dala biliyan 50 wajen gina ɓangaren tsaronta a matsayin wani haɗin gwiwa da Chana.

Hotunan jiragen yaƙi samfurin J-10 ƙirar Chana a sama

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rundunar sojin Pakistan na amfani da jiragen yaƙi samfurin J-10 ƙirar Chana

Wannan yaƙi tsakanin Pakistan da Indiya dai ya fito da ƙasar Chana a sarari, inda ta raba gardama. Imtiaz Gul, wani mai sharhi ne kan lamurran tsaro game da Pakistan, ya ce, "Lamarin ya ba ƙwarraru a Indiya mamaki. Ba su farga da irin ci gaban kimiyya da aka yi amfani da shi a yaƙin Indiya da Pakistan ba", in ji shi.

Chana kan sayar da makamai ga galibin ƙasashen masu tasowa kamar Myanmar da Pakistan. A baya an sha sukar makaman na Chana saboda rashin ingancinsu da matsalolin da suke bayar wa.

Rahotanni na cewa mafi yawan jiragen da ƙasar Bama ta daina amfani da su ƙirar JF-17 waɗanda ƙasashen Pakistan da Chana suka ƙera – sakamakon matsalolin da suke nunawa.

Haka ma sojojin Najeriya sun sha bayar da rahoton cewa su na yawan samun matsala da jiragen F-7 da Chana ta ƙera.

A lokacin da aka taɓa samun wani gajeren yaƙi tsakanin sassan biyu a 2019 bayan wani harin da Indiya ta kai wa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne a Pakistan, an harbo wani jirgin saman yaƙi ƙirar Rasha samfurin MiG-21 a wani yanki na Pakistan, har ma aka kama matuƙinsa, wanda aka sai bayan wasu 'yan shekaru.

Har ila yau, Indiya ta ce matuƙin ya riga ya tsallake bayan ya yi nasarar harbin jiragen saman yaƙin Pakistan cikin su har da F-16 ƙirar Amurka. Amma Pakistan ta ƙaryata hakan.

Duk da rahotanni game da harbo jiragen Indiya a makon jiya, masana irin Mista Ladwig ya ce ita ma Indiya ta samu gagarumar nasarar harbo wasu wurare a ranar 10 ga watan Mayu, sai dai kuma kafafen watsa labarai na duniya ba su kai ga ganin labarin ba bale su wallafa.

Rundunar sojojin Indiya ta fitar da sanarwar cewa ta ƙaddamar da hare-haren makamai mai linzami har goma sha ɗaya a sansanonin sojin saman Pakistan da suka haɗa da na Nur Khan da kuma Rawalpindi, waɗanda ba su da nisa da babbar helkwatar sojin Pakistan, harin da kuma ake ganin ya girgiza Islamabad. Ɗaya daga wurare masu nisa da Indiya ke harara na a yankin Bholari mai nisan kilomita 140 daga kudancin birnin Karachi.

Jiragen na Indiya na iya amfani da nau'in makamai masu linzami daban-daban da kuma jirage marasa matuƙa duk da cewa Pakistan ta yi amfani da na'u'rorin tare makamain HQ 9.

Kujeru da tebura a warwatse

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani ɓangare na yankin Pahalgam inda 'yan tayar da ƙayar baya suka kashe fararen hula 26

Ƙwarru dai sun bayyana cewa Indiya na da buƙatar ƙara samar da kuɗi domin inganta masana'antar ƙera makamanta da kuma ƙara samar da hanyoyin cininkin makaman tsakaninta da sauran ƙasashen duniya cikin sauri.

A yanzu dai, ga alama ma'aikatar ƙera makaman Chana na alfahari tare da nuna farin ciki akan iƙirarin da ake yi cewa jiragen saman da ta ƙera na yaƙi sun yi zarra a lokacin fafatawar ƙasashen Indiya da Pakistan.