Asibitin da ya cika da jariran da ke fama da yunwa a Afghanistan

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
- Marubuci, Yogita Limaye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jalalabad
- Lokacin karatu: Minti 8
Gargadi: Wannan labarin na ɗauke da bayanan da ka iya tayar da hankali
''Wannan ba ƙaramin tashin hankali ba ne a gare ni. Ina cikin matuƙar baƙin ciki. Kun san irin halin da na shiga yayin da nake ganin ƴaƴana suna mutuwa? in ji Amina.
Ta rasa ƴaƴa shida, waɗanda dukkansu babu wanda ya wuce shekara uku da haihuwa. Yanzu kuma ga wata tana kwance rai a hannun Allah.
Bibi Hajira, da ke mai bakwai da haihuwa ba ta wuce girman jaririyar da aka haifa yanzu ba.
Tana fama da matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki kuma tana kwance a gado a asibitin yankin Jalalabad da ke lardin gabashin Nangarhar a ƙasar Afghanistan
''Ƴaƴana suna mutuwa saboda tsananin talauci. Babu abin da nake iya ba su, sai busasshen burodi da ruwa wanda nake ɗumamawa ta hanyar shanyawa a rana.'' in ji Amina, muryarta cike da baƙin ciki.
Abu mafi tashin hankali shi ne labarinta ya yi kama da na sauran mutane da dama- kuma za a iya ceto wasu rayuka masu ɗimbin yawa idan har aka ɗauki matakai a kan lokaci.

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
Bibi Hajira na ciki yara sama da miliyan uku da ke fama da matuƙar ƙarancin abinci mai gina jiki wanda ya yi wa ƙasar dabaibayi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan yanayi ne da aka kwashe shekaru da dama ana fama da shi da Afghanistan, sakamakon yaƙin da aka yi na shekara 40, da tsananin talauci da kuma sauran al'amura da suka kunno kai cikin shekara uku da dawowar Taliban karagar mulki.
Amma yanzu yanayin ya kai wani irin mummunan mataki.
Zai yi wahala mutum ya iya kintata yadda yawan mutane miliyan 3.2 ke rayuwa, amma bayanai da ke fitowa daga wani ɗakin asibiti guda ɗaya na iya nuni da irin mummnan halin da ake ciki.
Akwai yara 18 da ke kwance a gadaje bakwai. Wannan ba yanayi ne ɗa lokaci ba, haka lamarin ya ke a kullum. Babu ƙarar koke-koke, babu hayaniyar yara, ƙarar da ake ji kawai ita ce ta n'urorin da ke auna numfashin yaran.
Mafi yawan yaran na kwance ne kawai sanye da na'urar shaƙar iska. Ba barci suke yi ba amma ba su da ƙarfin da za su yi motsi ko magana.
Sana, mai shekara uku tana kwance a kan gado ɗaya da Bibi Hajira. Mahaifiyarta ta rasu yayin da ta ke haihuwar ƙanwarta a watannin da suka gabata.
Ƴar uwar mamanta Laila ce ke kula da ita. Laila ta ɗaga min hannayenta biyu, tare da ware min yatsunta bakwai, tana nuna adadin yaran da ta rasa.
Iham mai shekara uku ne ke kwance a gadon da ke makwabtaka da su, girmansa bai kai na yaro mi shekaru irin nasa ba.
Shekara uku da suka gabata, ƴar'uwarsa mai shekara biyu ta rasu.
Ba ma za ka iya kallon Asma ba. Kyakyawar yarinya ƴar shekara ɗaya, idanunta na buɗe amma ko ƙyaftawa ba ta iya yi yayin da ta ke numfashi sama-sama, sanye da na'urar shakar iska.

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
Dokta Sikandar Ghani, wanda ke tsaye a kanta, ya girgiza kansa. ''ba na tunanin cewa za ta rayu,'' in ji shi. Rashin lafiyar na ta ya yi muni.
Duk da halin da ake ciki, har yanzu, ma'aikatan asibiti da iyaye na ta kai komo, don yi wa yaran hidima. Amma komai ya tsaya cak yanzu, gwiwar kowa ta yi sanyi.
Mahaifiyar Asma, Nasiba ta fashe da kuka. Ta ɗaga lulluɓinta ta duƙa domin ta sumbaci 'yarta.
Ina ji kamar fatar jikina na narkewa. Ina jin zafin wannan mawuyacin halin da take ciki.'' in ji ta.
Nasiba ta rasa ƴaƴanta uku. ''Maigidana lebura ne. idan ya samu aiki ne muke iya cin abinci.''
Dokta Ghani ya faɗa mana cewa, Asma na iya samun bugun zuciya a kowane lokaci. Cikin ƙasa da sa'a ɗaya bayan ficewarmu daga ɗakin, ta rasu.
Yara 700 sun mutu a asibitin cikin wata shida da suka gabata - sama da guda uku kowace rana, a cewar ma'aikaytar lafiyar Taliban a yankin Nangarhar.
Kuma da lamarin zai fi haka taɓarɓarewa idan Bankin Duniya da Unicef suka dakatar da tallafinsu a wannan asibitin.
Har ya zuwa watan Agustan 2021, kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta samu daga ƙasashen waje ne kawai ake amfani a su wurin tafiyar da al'amuran kiwon lafiya na Afghanistan.
Lokacin da Taliban suka karɓi ragamar mulki, an dakatar da samun kuɗaɗe daga ƙasashen waje saboda takunkumin da ƙasashen duniya suka ƙaƙaba wa ƙasar.
Wannan ya janyo taɓarɓarewar al'amuran kiwon lafiya. Hukumomin ba da agaji sun sanya hannu domin samar da abin da aka kira matakin gaggawa na wucin-gadi.

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
Wannan mataki ne da ba zai ɗore ba, kuma a halin yanzu da abubuwa suka yi yawa a duniya, tallafin da ake bai wa Afghanistan ya ragu.
Sannan manufofin gwamnatin Taliban, musamman takunkuman da take ƙaƙaba wa mata ya sa masu ba da agaji suna shakkar sanya kuɗaɗensu a ƙasar.
''Mun gaji matsalar talauci da yunwa, wanda suka ƙara ta'azzara sakamakon al'amura irin su ambaliyar ruwa da kuma sauyin yanayi.
Ya kamata ƙasashen duniya su ƙara yawan taimakon jin-ƙai da suke bayarwa, kada su alaƙanta shi da batutuwan siyasa da na cikin gida,” in ji Hamdullah Fitrat, mataimakin kakakin gwamnatin Taliban.
A cikin shekaru uku da suka gabata mun je cibiyoyin kiwon lafiya fiye da goma a ƙasar, kuma mun ga yadda lamarin ke taɓarɓarewa cikin sauri.
A duk ziyarar da muka yi a asibitocin baya, mun ga yadda yara ke mutuwa.
Amma kuma abin da muka gani shi ne cewa amfani da magungunan da suka dace na iya ceton rayukan yara.
Bibi Hajira wacce ta kasance cikin rauni a lokacin da muka ziyarci asibitin, yanzu ta samu sauƙi sosai kuma an sallame ta, kamar yadda Dakta Ghani ya shaida mana ta waya.
"Idan muna da ƙarin magunguna, da kayan aiki da ma'aikata za mu iya ceton yara da yawa. Ma'aikatanmu suna da himma da jajircewa. Muna aiki ba tare da gajiyawa ba kuma a shirye muke mu yi abin da ma ya fi hakan,” in ji shi.
“Ni ma ina da yara. Idan yaro ya mutu, mu ma abin yana girgiza mu. Na san yadda iyayen ke ji a zukansu."

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
Rashin abinci mai gina jiki ba shi ne kaɗai abin da ke janyo rasa rayuka ba. Sauran cututtuka da za a iya warkarwa ma na kashe yara da dama
A sashen kula da cututtuka masu tsanani da ke makwabtaka da masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, mun haɗu da Umrah, mai wata shida wanda ke fama da cutar sanyi ta pneumonia.
Tana sharɓar kuka yayin da ma'aikaciyar asibiti ke ƙoƙarin ɗaura mata ledar ruwa a jikinta. Uwarta Nasreen na zaune a kusa da ita hawaye na kwarara a idanunta.
''Dama zan iya mutuwa a madadinta. ina cikin matuƙar fargaba,'' in ji ta. Kwanaki biyu bayan mun ziyarci asibitin, Umrah ta rasu.
Wannan labarin mutanen da suka sami kai wa asibiti ke nan. Akwai da dama da ba su ma kai ga isa asibitin ba. Kashi ɗaya cikin biyar na yaran da ke buƙatar kula ne kawai ke iya samun hakan a asibitin Jalalabad.
Matsin da ke kan asibittin ya yi tsanani, jim kaɗan bayan Asma ta rasu, sai ga wata jaririya, ƴar wata uku, Aaliya, an kawo ta gadon da Asma ta bari.
Babu kowa a ɗakin da ya sami lokacin tunanin abin da ya faru. Akwai wani yaro mai fama da tsananin rashin lafiya da za a fara ƙoƙarin yi masa magani.
Asibitin Jalalabad yana kula da al'ummar larduna biyar, wanda gwamnatin Taliban ta kiyasta kusan mutane miliyan biyar ne.
Kuma yanzu matsin lamba a kansa ya ƙaru. Galibin ƴan gudun hijirar Afganistan sama da 700,000 da Pakistan ta kora tun ƙarshen shekarar da ta gabata na ci gaba da zama ne a Nangarhar.
A cikin al'ummomin da ke kewaye da asibitin, mun sami bayanan wata ƙididdiga mai ban tsoro da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a wannan shekara: cewa kashi 45 cikin 100 na yara ƴan ƙasa da shekara biyar na fama da rashin girma - girmansu bai kai na masu shekaru irin nasu ba- a Afghanistan.
Ɗan Robina, Mohammed mai shekara biyu bai fara iya tsayawa ba amma a halin yanzu ya yi gajarta fiye da yadda ya kamata.

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
“Likita ya ce idan ya samu magani na tsawon wata uku zuwa shida, zai samu lafiya. Amma ko abinci ba mu iya ci . Ta yaya za mu iya biyan kuɗin maganin?” in ji Robina.
Ita da danginta sun bar Pakistan ne a shekarar da ta gabata kuma yanzu suna zaune a wani matsuguni mai ƙura, a yankin Sheikh Misri, wanda ba shi da nisa daga Jalalabad.
"Ina fargabar zai zama naƙasasshe kuma ba zai taɓa iya tafiya ba," in ji Robina.
“A Pakistan ma mun fuskanci rayuwa mai wahala. Amma akwai aikin yi. Anan mijina, wanda lebura ne, baya samun aiki cikin sauki. Da har yanzu muna Pakistan da za mu iya yi masa magani.”

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
Unicef ta ce rashin girma yadda ya kamata na iya haifar da mummunar illa ga yanayin jiki da kuma kaifin ƙwaƙwalwar yara, wanda hakan zai iya yin tarihi har tsawon rayuwar mutum.
Mohammed zai iya tsira daga wannan mummunan halin idan an yi masa magani kafin lokaci ya ƙure.
Amma shirye-shiryen abinci mai gina jiki na al'umma da hukumomin agaji ke gudanarwa a Afganistan sun gamu da tazgaro - yawancinsu sun sami kashi ɗaya cikin huɗu ne kawai na tallafin da ake buƙata.

Asalin hoton, BBC/Imogen Anderson
A sassa daban daban na Sheikh Misri mun haɗu da iyalai da ke da yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.
Sardar Gul yana da ’ya’ya biyu masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki – Umar ɗan shekara uku da Mujib ɗan wata takwas, ƙaramin yaron da ke riƙe da shi a cinyarsa.
''Wata guda da ya gabata nauyin Mujib ya sauka ƙasa da Kilogiram uku. bayan mun iya yi masa rajista da wata hukumar bayar da agaji, muka fara samun tallafin abinci. ba ƙaramin taimaka masa suka yi ba,'' in ji Gul.
Yanzu nauyin Mujib ya kai kilogiram shida, duk da haka dai nauyinsa bai kai yadda ake buƙata ba, amma dai an sami ci gaba.
Wannan lamarin na nuni da cewa samun irin tallafin da ake buƙata a kan lokaci na iya ceto yara daga mutuwa da kuma masifar naƙasa.











