Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jami'ai sun hana 'yansanda kama shugaban Koriya ta Kudu da aka dakatar
Tawagar 'yansanda a Koriya ta Kudu ta dakatar da shirin kama shugaban kasar da aka tsige, Yoon Suk Yeol.
Ayarin masu bincike da 'yansandan sun yi kokarin shiga fadar gwamnati domin kamo shugaban, sai dai sun fuskanci turjiya daga jami'an tsaron da ke kare fadar.
Sun ce zai yi wahala su iya kama shugaban saboda gumurzun da suka yi da sojoji.
Wakiliyar BBC ta ce masu zanga-zanga sun kewaye fadar gwamnati tun bayan fitar da sammancin kama shi.
Sannan an tura dubban 'yan sanda fadar gwamnatin.
Tun a watan da ya gabata ake neman Mista Yoon domin amsa tambayoyi kan yunkurin da ya yi na sanya dokar soji a kasar.
A yanzu jami'an sun ce za su koma su yi shawara kan matakin da za su dauka na gaba.
Wata kotu ce dai ta bayar da sammacin kama Mista Yoon a farkon makon nan bayan da ya ki bayyana a gaban jami'ai da ke bincike a kansa.
Lauyoyin Mista Yoon sun ce sammacin ya saba doka kuma suka ce za su kalubalance shi.
A ranar 14 ga watan Disamban da ya wuce ne aka dakatar da shi daga mulki bayan da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada kuri'ar tsige shi, to amma a bisa doka tsigewar za ta tabbata ne idan kotun tsarin mulki ta tabbatar da tsigewar.
Tun da farko jam'iyyar hamayya ta kasar ta Koriya ta Kudu wadda ke da rinjaye a majalisar dokoki ta gargadi jami'an tsaron fadar shugaban kasar da su bada hadin kai, su gu ji hana kama shi.
Tun da farko an girke dubban 'yansanda a yankin da gidan shugaban yake, yayin da 'yan jarida suka yi wa wajen tsinke, su kuma magoya bayan Mista Yoon suka kasa suka tsare a wajen gidan, suna ta jinjina da koda gwanin nasu.
Duk da cewa an dakatar da Shugaba Yoon tare da raba shi da iko, to amma har yanzu jami'an tsaron fadar shugaban kasa ne da kuma sojoji ke kare shi.
Kuma sojojin su ne ke da alhakin kare babban birnin Seoul, hadi da gidan shugaban kasar.
Kasancewar sai ranar 6 ga watan nan na Janairu wa'adin sammacin zai kare ba a san abin da zai biyo baya ba yanzu.
Watakila hukumar binciken ta sake jarraba wata rana domin kama shi.
Wannan ba shi ne karon farko da hukumomi ke kasa kama wani dan majalisar dokoki ba, a kasar, inda ko a baya 'yan jam'iyya da magoya baya kan hana 'yansanda irin kamen har wa'adi ya kare.