Yadda ƙarin kuɗin fetur ya shafi masu ƙananan sana'o'i a Najeriya

Asalin hoton, Nura Usman
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana cigaba da tattaunawa kan yadda ƙarin farashin man fetur a Najeriya ya shafa mutanen ƙasar, inda mutane da dama suka koma tafiya a ƙafa, sannan ma'aikata da dama suka rage kwanakin zuwa aiki, wasu ma suka ajiye aikin saboda yadda albashinsu yake ƙarewa a sufuri da abinci.
Sai dai a lokuta da dama, an fi mayar da hankali ne a kan yadda ƙarin yake shafar wasu ɓangarorin mutane, musamman waɗanda ake ganin suna da alaka ta kai-tsaye da fetur ɗin.
Abin tambaya a nan shi ne ta yaya ƙarin farashin man ke shafar masu ƙananan sana'o'i a Najeriya? BBC ta tattauna da wasu masu ƙananan sana'o'in kamar haka:
Kanikawa suna cikin wani hali - Nura bakanike

Asalin hoton, Getty Images
Nuraddeen Shehu, bakanike ne da ya daɗe yana sana’ar gyarar motoci, inda yake tafiye-tafiye domin gyara da ɗauko motoci daga wasu jihohin zuwa wasu.
Ya bayyana cewa yanzu komai ya tsaya cak, inda suka koma rayuwar samu na hannu baka hannu ƙwarya.
“Wannan al’amari na ƙarin kuɗin man fetur gaskiya muna fuskantar ƙalubale. Za ka samu duk wanda zai saya mota daga wani gari, idan ya lissafa kuɗin da zai kashe a gyara da man da za a sha idan za mu ɗauko masa motar, zai ga ta yi tsada sosai,” in ji shi.
Nura ya bayyana wa BBC yadda ya je Warri ya ɗauko mota ya kawo Kaduna, amma maimakon riba, a ƙarshe sai shi ne ya yi ciko da kuɗinsa.
“Dubu 100 aka ba ni domin in sha mai, sannan in ci abinci. Amma a kwana uku, sai da kuɗin ya ƙare a kuɗin mai da abinci. A da idan na yi irin wannan tafiyar, ina cin abin da nake so a can, sannan in dawo da riba sosai. Wannan ma kafin wannan ƙarin na ƙarshe ke nan.”
Nura ya ƙara da cewa a wajen gyara kuma ba a kawo musu motoci. “Yanzu duk wani ƙaramin ma’aikaci ya ajiye motarsa. Sannan masu hawa kuma yawanci sun koma ƙananan mota wadda ba ta shan mai sosai,” in ji Nura, inda ya ƙara da cewa a cikin kashi 10 da suke kawo masa gyara, yanzu bai fi kashi biyu ne suke kawo masa gyara.
“Ai duk wanda mota ba ta zama masa dole ba, ajiye ta yake yi. Mutane da dama sun ajiye mota a gida. Kuma sai ana hawa ne za a yi gyara. Duk wanda ya auna ya ga yana takura sai ya daina hawa motarsa. Dama tamkar iyali take mota. To yanzu ga tsadar rayuwa ga mota, da wanne mutun zai ji.”
Nura ya ce yanzu yawancinsu suna haɗa wa da wata sana’ar ce, wasu kuma sun nema wata sana’ar, “amma lallai waɗanda sana’ar kanikanci kaɗai suke yi yanzu suna rayuwa ne cikin ƙunci da damuwa.”
A ƙarshe ya buƙaci abokan sana’arsu su nema wa kansu mafiya ta hanyar neman wasu sana’o’in domin cigaba da rayuwa.
'Leburori sun daina zuwa aikin gini'

Asalin hoton, Musa Magini
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Suma magina ƙarin ya shafe su sosai, inda sukan yi dogon tafiya domin aikin ginin, kuma yawanin aikin na buƙatar cin abinci.
Musa Umar wanda aka fi sani da Ɗan Umma, magini ne a Kaduna, ya bayyana wa BBC cewa yanzu lamarin sai dai addu’a.
“Ƙarin kuɗin mai ya taɓa aikinmu sosai. Yanzu haka maganar da muke da kai gamu nan mu goma a zaune a gida sai hira kawai muke yi.
“Wani lokacin ana biyan lebura 2,000 shi kuma mesin 4,000. A dubu 4 da ake ba mesin ɗin nan na mesin, in sha Allah ya dawo da kuɗi sosai ne ya dawo gida da 1,500. Idan aka yi la’akari da yanayin tsadar rayuwa, idan mutum ya dawo gida 1,500 ga iyali, ta yaya zai iya ciyar da su?”in ji shi.
Musa ya ce yanzu dole wasu leburorin sun daina zuwa aiki, “saboda mutum ya je an biya shi 2,000, kuma 1,000 ya ƙare a kuɗin mota, ga abinci kuma. Shi ya sa suka daina zuwa aikin, dole mu ne muke aikin lebura yanzu saboda sun gwammace su zauna a gida kawai saboda wasun su suna da iyali, idan sun fita ma kuɗin yana ƙarewa ne a kuɗin mota da abinci a can, iyali kuma suna jira a gida.”
A ƙarshe Musa ya yi kira ga gwamnati ta kalle su da idon rahama domin su samu sauƙi.
Dole za mu ƙara ƙudin mota - Isa direba
Direbobi dama su a zahiri yake yadda lamarin ya shafe su, kasancewar dole sai da fetur suke amfani, wanda dole tsadarsa ya shafe su.
Malam Isa direba ne da yake tuƙi daga Kano zuwa Abuja ya ce a da yana sawu uku a mako, amma yanzu idan a tasha yake jiran layi, bai fi ya yi lodi sau ɗaya a makok ba.
Ya ce lamarin yana shafar harkokin tafiyar da gida a wajensu, “a da shayi da madara nake sha, amma yanzu tuwo ake dafawa a ci da dadddare, sannan a yi ɗumame da safe.”
Ya ce dole yanzu sun ɗauko fasinjoji a tsohon farashin, "amma yau (Juma'a) za a zauna a Abuja domin ƙara farashin. Ina tunanin za a mayar da farashin naira 17,000 daga naira 15,000 da muke ɗauka."
Malam Isa ya ce zaman da suke yi a daɗe ba tare da an samu fasinjoji ba yana shafarsu baki ɗaya, "sai dai nakan yi sa'ar akwai waɗanda suke kirana ina ɗaukarsu ko saƙo zuwa Abuja lokaci bayan lokaci."
Kuɗin fetur ya shafi masu ɗinki
A nasu ɓangaren, masu sana'ar ɗinki kuka biyu suke yi: tsadar fetur da suke amfani da shi a injin ɗinki, da kuma tsadar kasancewar wasu sai sun ci, sun ƙoshi ne za su yi ɗinki.
Abdulhamid Ahmed wani tela ne da ke sana’arsa a Kaduna, ya bayyana wa BBC cewa, “ƙarin kuɗin fetur ya taɓa sana’armu sosai. Kayan aiki sun ƙara tsada, sannn ga rasin wuta. Dole mutum ya saya man fetur saboda ya yi aiki.”
Abdulhamid ya kara da cewa, “wani lokacin za ka karɓa aikin mutum ka masa alƙawarin ranar da zai zo ya karɓa, amma sai rashin wuta ya hana ka aikin. Dole ka saya fetur domin ka cika alƙawari ko da kuwa kun yi ciniki ne a kan farashin amfani da wutar lantarki.
Abin da ya kamata masu ƙananan sana'o'i su yi - Masani
Domin ganin yadda waɗannan masu ƙananan sana'o'in za su yi domin rage zafi, BBC ta tuntuɓi Dokta Kabiru Jabo, malami a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, masanin tattalin arziki, inda ya ce akwai wasu matakan da ya kamata su ɗauka.
Ya bayar da wasu shawarwari guda uku da ya kamata su yi amfani da su domin rage raɗaɗin da suke ciki domin su saƙaƙa wa kansu.
- Masu amfani da fetur su nemi wani makamashin daban ko kuma su haɗa hannu su samu hanya ɗaya da masu sana'a da dama za su riƙa amfani da shi a tare.
- Su fito su nuna wa gwamnati damuwarsu ko a ƙungiyance. Duk duniya gwamnati na ba irin su tallafi ko rangwame. Su haɗa ƙungiyoyi su nemi ƴan majalisunsu da sauran ƴan siyasa su nema musu sauƙi a gwamnatance.
- Su ƙara huɓɓasa wajen aiki. Idan mutum na aikin awa ɗaya ne, ya ruɓanya saboda dole ne a ci abinci a sha.











