Yadda China ta lafta haraji kan kwaroron roba don bunƙasa haihuwa

A baby lying down on a patterned grey cloth while dressed in a red traditional Chinese outfit with gold linings. Some red flowers surround him.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Osmond Chia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
    • Marubuci, Yan Chen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Chinese
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan China sun su fara biyan harajin kashi 13 na magunguna da kayan hana ɗaukar ciki ne daga farkon Janairu, amma sai aka cire haraji kan kula da yara a asibiri a ƙasar China.

Wannan na ƙunshe ne a cikin sabon kundin harajin ƙasar da aka sanar a ƙarshen shekarar da ta gabata, inda a ciki aka yi gyara kan dokar haihuwar mutum ɗaya kacal da ƙasar ta ɗabbaƙa a shekarar 1994.

Sai dai kuma a sabuwar dokar an cire harajin kayayyaki a kan abubuwan da ake buƙata domin kula da dattawa da haraji na kayan aure.

China ta ɗauki wannan matakin ne domin magance matsalar da take fuskanta ta ƙaruwar dattawa a ƙasar.

Ƙasar ta ce hakan ne ya sa take ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar matasa su yi aure, su hayayyafa.

Alƙaluman hukuma sun nuna cewa mutanen China na raguwa ne a shekara uku da suka gabata a jere, inda jarirai miliyan 9.54 kawai aka haifa a ƙasar a shekarar 2024, kusan rabin haihuwar da aka samu a shekara 10 baya a lokacin da ƙasar ta sanar da dokar taƙaita haihuwa.

Amma duk da haka cire haraji na kwaroron roba da magungunan hana ɗaukar ciki ya haifar da ce-ce-ku-ce saboda fargabar da halin da masu ɗaukar cikin da ba su shirya masa ba za su shiga, da ma yiwuwar ƙaruwar cutar HIV. Wasu kuma sun bayyana cewa ƙara farashin kwaroron roba ba zai hana su taƙaita haihuwa ba.

Da wani dilllalin kwaroron roba ya yi magana kafofin sadarwa, inda kira ga mutane da su tara kwaroron roba kafin ya ƙara tsada, sai wani ya yi martani cikin raha cewa, "zan saya wanda zai ishe ni har ƙarshen rayuwata."

China na cikin ƙasashen da rainon yara ke da tsada sosai a duniya kamar yadda alƙaluman ƙididdiga cibiyar bincike ta YuWa Population Research Institute da ke Beijing ya nuna 2024.

Sannan tsadar ɗawainiyar yara na ƙaruwa ne da zarar sun fara zuwa makaranta, ga kuma ƙalubalen da iyaye mata suke fuskanta wajen haɗa raino da ko dai aiki ko karatu.

"Ina da yaro ɗaya kacal, kuma ya ishe ni," in ji Daniel Luo mai shekara 36, wanda ke zaune a gabashin lardin Henan.

Ya ce ƙarin farashin bai dame shi ba, "yanzu ƙarin da aka yi a kwalin kwaroron roba bai wuce yuan biyar ko kuma 10 ba, ko kuma ya kai yuan 20."

Matasan ma'aurata a China ba su cika burin samun haihuwa ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aurata a China ba su cika damuwa da samun haihuwa ba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma ƙarin farashin zai iya tasiri kan wasu, kamar Rosy Zhao, wadda ke zaune a birnin Xi'an na tsakiyar China.

Ta ce ƙara farashin magungunan hana ɗaukar ciki tamkar jefa rayuwar ɗalibai da marasa ƙarfi cikin tasku ne.

Masu sharhi sun samu saɓani kan muhimmancin yi wa harajin garambawul, musamman ƙara haraji kan kwaroron roba da kayan hana ɗaukar ciki.

Yi Fuxian na jami'ar Wisconsin-Madison ya ce tunanin wai ƙara farashin kwaroron roba zai rage haihuwar magana ce kawai.

Ya ce China na neman karɓar haraji ne kawai daga duk inda za ta samu.

Harajin VAT da China ke tarawa wanda ya kai kusan dala triliyan 1, wato kimanin fanm biliyan 742 ne kusan kashi 40 na harajin da ƙasar ke samu a duk shekara.

Yunƙurin karɓar haraji a kwaroron roba kawai magana ne, amma matakin zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar mutane su ƙara haihuwa, kamar yadda Henrietta Levin na cibiyar Center for Strategic and International Studies.

Babbar buƙatar China ita ce ƙarfafa gwiwar mutanen ƙasar China su hayayyafa, duk da cewa ƙasar za ta iya fuskantar ƙalubale daga mutane, in ji ta, inda ta ƙara cewa kamata ya yi haihuwa ta zama zaɓi na mutane.

A ƴan kwanakin nan, ana samun rahotanni cewa ana kiran wasu mata da ke wasu lardunan ƙasar ana tambayarsu yanayin al'adarsu da kuma neman mu'amala da su domin samun haihuwa.

China na cikin ƙasashen da ɗaiwainiyar yara ke da wahala

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, China na cikin ƙasashen da ɗaiwainiyar yara ke da wahala

Masu sharhi da mata sun ƙara da cewa yadda maza suka mamaye shugabanci da sauran madafun ido da ma rashin damawa da mata a cikin abubuwan ne ke haifar da matsalar, duk da cewa ba China kaɗai ba ce take fama da irin wannan matsalar.

Ƙasashen yamma da ma wasu ƙasashe masu maƙwabtaka da China irin su Koriya ta Kudu da Japan ma sun dage wajen ƙara yawaitar haihuwarsu saboda ƙaruwar dattawa a ƙasashen.

Wata matsalar ita ce ɗawainiyar yara, wadda a lokuta da dama ke komawa kan iyaye mata.

Mr Luo daga Henan ya yi nuni da ƙaruwar sayen robobin biyan buƙata a China, wanda a cewarsa, "mutane suna komawa amfani da robobin su gamsar da su da kore sha'awarsu ne," "ganin mu'amala tsakanin samari da ƴanmata yana zama wahala."

A cewarsa, "shiga intanet ta fi amfani kuma ta fi samar da jin daɗi, "domin jin daɗin na gaskiya ne."