Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan gwagwarmayar Myanmar da aka zartar wa hukuncin kisa: Phyo Zeya Thaw da Ko Jimmy
A ranar Litinin ne ƴan Myamar suka wayi gari da labarin cewa gwamnatin mulkin sojan kasar ta zartar da hukuncin kisa kan wasu masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya hudu da suka hada da tsohon dan majalisa Phyo Zeya Thaw da kuma tsohon madugun 'yan adawa Ko Jimmy.
BBC ta yi magana da 'yan uwansu da abokansu makonni kafin a kashe mutanen biyu.
"Ina son kallon taurari. Ya fahimce su sosai.
"A wannan lokacin, na san sararin samaniya ne kawai hanyar da za mu iya sadarwa juna sako," in ji Thazin Nyunt Aung, yayin da ta tuna da daren 3 ga watan Yuni lokacin da ta gano cewa sojoji za su zartar wa wanda take shirin aura Phyo Zeya Thaw hukuncin kisa, wanda aka yanke masa a watan Janairu.
Yana daya daga cikin masu fafutuka hudu, Ko Jimmy, wanda ainahin sunansa Kyaw Min Yu, da Hla Myo Aung da Aung Thura Zaw, wadanda aka tabbatar da hukuncin kisa a kansu a ranar.
An kashe su ne a a karshen makon da ya gabata duk da ba a san ranar ba, kafin daga bisani wata kafar yada labarai ta kasar ta bayar da rahoton mutuwarsu a safiyar ranar Litinin.
Amma makonnin da suka gabata, Thazin Nyunt Aung, ta yi fatan samun wani sakamako na daban.
Ta dogara ne da cewa Myanmar ba ta kashe kowa ba fiye da shekaru talatin, karo na karshe shi ne a 1988.
Daga wakar gambara zuwa turjiya
Phyo Zeya Thaw na daga cikin mutane fiye da 120 da aka yanke wa hukuncin kisa tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabrairun bara tare da kama shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.
An kama shi bayan watanni tara, a watan Nuwamba, kuma an zarge shi da kitsa jerin hare-haren da aka kai wa gwamnatin mulkin soja.
Da ta samu labarin hukuncin kisan da aka yanke masa, ta ce idanuwanta sun kada sun yi ja, jikinta ya yi ta ɓari, ta fice daga gidan ba tare da ta san inda za ta je ba.
Don ta kwantar da hankalinta, sai ta kalli sararin samaniya, ta karanta addu'o'in addininta na Buddah ga Phyo Zeya Thaw.
"Na aika masa da soyayyata, na kuma sha alwashin ba za mu ja da baya ba ko kadan, za mu yi yaki har zuwa karshe," in ji ta.
Phyo Zeya Thaw, mai shekaru 41, dan majalisa ne daga jam'iyyar National League for Democracy (NLD), wacce ta mulki Myanmar kafin juyin mulkin.
Ya kuma kasance na hannun daman hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi.
Yana yi mata rakiya kusan dukkan tafiye-tafiyenta zuwa kasashen waje daga 2015 zuwa 2020.
Kafin juyin mulkin, ya yanke shawarar cewa ba zai tsaya takara ba saboda yana so ya koma wakarsa ta gambara.
Thazin Nyunt Aung ya ce "Ya so rubuta sabbin waƙoƙi sannan ya ci gaba da halartar taruka da bukukuwa don nishadantar da jama'a".
Sojojin Myanmar sun yi zargin cewa an tabka magudi a zaben da jam'iyyar NLD ta samu nasara, zargin da jami'an zaben suka musanta.
"Zeya Thaw ya kyamaci mulkin kama-karya da rashin adalci tun daga farko," in ji abokinsa kuma wanda ya kafa Generation Wave, Min Yan Naing.
"Imaninsa na kawo karshen mulkin kama-karya na soji ya kasance mai karfin gaske ta yadda a ko da yaushe a shirye yake ya fuskanci duk wani hadarin da zai iya fuskanta."
"Suna son ta'addanci da tsorata mutane. Amma kamar ko da yaushe, Zeya Thaw bai wani damu da hukuncin kisa ba.
"Ko da yake zai iya dan damuwa, amma ba zai taba nuna musu ba."
Juyin juya halin da ba a gama ba
Kyaw Min Yu, wanda aka fi sani da Ko Jimmy, shi ma ba bako ba ne a gidan yari.
Mai shekaru 53, wanda ya taba shafe fiye da shekaru ashirin a gidan yari, ya taba kiran idan yari da "gidansa na biyu".
An kama shi kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a yarin, da kuma aiki tukuru.
An sake kama shi a watan Oktoban shekarar da ta gabata kuma ana zarginsa da kasancewa daya daga cikin wadanda suka kitsa kashe masu bai wa sojoji bayanai.
Sannan ana zargin sa da kai hare-hare a tashoshin wutar lantarki da gine-ginen gwamnati, zargin da matarsa ta musanta.
Ko Jimmy ya kasance shugaban kungiyar dalibai yayin zanga-zangar 1988, inda dubban daruruwan 'yan kasar suka yi tawaye ga mulkin kama-karya na lokacin Ne Win na shekaru 26.
A nan ne ya yi wa wata yarinya ‘yar makarantar sakandare ganin farko sanye da fararen kaya, kamar yadda ya shaida wa NPR shekaru bayan haka a shekarar 2014.
Shekaru da yawa bayan haka, an aika wannan yarinyar zuwa kurkukun da yake don shirya zanga-zanga, a nan ne Ko Jimmy ya fara rubuta wa Nilar Thein wasia, daga nan soyayyarsu ta fara ƙarfi.
Ya nemi aurenta, duk da cewa ba za su iya yin aure ba a kurkuku.
An saki ma’auratan a shekara ta 2004 bayan Ko Jimmy ya yi shekara 15 a gidan yari, ita kuma shekara tara.
A shekara ta 2007, lokacin da Myanmar ta fada juyin juya halin Saffron, ma'auratan sun sake jagorantar zanga-zangar.
A lokacin 'yarsu ba ta wuce watanni ba, aka kama Ko Jimmy. Nan da nan Nilar Thein ta ɓuya, tana ta faɗi tashi daga nan zuwa can da jaririnta.
Kafin a kama ta ita ma, ta yi nasarar barin jaririnta a hannun danginta.
Ma'auratan sun sake haduwa bayan an sake su bisa afuwar da aka musu a shekarar 2012.
"A cikin shekaru talatin na juyin juya hali, Jimmy ya fuskanci mafi munin yanayi a ciki, da wajen gidan yari.
"Dukanmu dole ne mu shawo kan wanannan yanayi" in ji Min Zeya, wani dattijon dan gwagwarmaya. Shugaban "88 Generation".
Bayan kame na baya-bayan nan, da dama sun yi fatan cewa gwamnatin mulkin sojan ba za ta zartar da hukuncin kisa ba, wani abu da kasashen duniya ke ta matsin lambar a guji aikatawa.
Min Zeya ya ce "A shekarar 1988, an yanke wa mutane da yawa hukuncin kisa saboda adawa da masu mulkin kama-karya na soji.
Har ma na shafe wani lokaci tare da wadancan mutanen a gidan yari. Amma ba a kashe kowa ba kuma an saki da yawa daga baya," in ji Min Zeya.
Labarin hukuncin kisa ya kasance mai ban tsoro musamman saboda jami'an sun shirya wani taron tattaunawa tsakanin masu fafutuka da iyalansu a ranar Juma'a.
Mai magana da yawun sojojin ya musanta jita-jitar kisan da ake yi, yana mai cewa ba za su faru cikin gaggawa ba.
Nilar Thein ya ki yin magana da BBC, saboda dalilai na tsaro.
Amma kullum sai ta rika yin rubutu a Facebook, tana kirga kwanakin da ta yi Ba tare da mijinta ba.
A ranar Litinin, bayan da aka samu labarin zartar da hukuncin, ta rubuta cewa: “Masoyana, ku kasance raye, dole ne juyin juya halinmu ya yi nasara''.
Sa'o'i bayan haka, ta sake wallafa wani sako, inda ta ce matsawa ban ga gawar Jimmy ba, to kuwa ba zan yi bakin ciki ba''.
Babu tabbas ko har yanzu an kona gawarwakin masu fafutukar hudu.
Amma Nilar Thein da Thazin Nyunt Aung sun tsere wa sojojin da ke rike da mulki, don haka ba za su iya binne tokar gawarwakin 'yan uwansu ba.