BBC ta bankado yadda sojojin Myanmar suka azabtar tare da kashe mutane da dama

    • Marubuci, Daga Rebecca Henschke and Kelvin Brown
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Sojojin Myanmar sun azabtar da farar hula a watan Yuli, lamarin da ya kai ga mutuwar akalla maza 40, kamar yadda binciken BBC ya gano.

Ganau da wadanda suka kubuta sun ce sojojin, wasu daga ciki 'yan shekara 17, sun yi wa mutanen kauyen kawanya, suka ware maza da mata tare da kashe mazan. A cikin hotuna da bidiyon da suka nuna abin da ya faru, an ga yadda aka zabtar da wadanda suka mutu, sannan suka haka katon rami aka binne su baki daya.

Lamarin ya faru ne a watan Yuli, a kuma wurare daban-daban har guda hudu a garin Kani, yankin da 'yan adawa a gundumar Sagaing da ke tsakiyar Myanmar ke da karfi.

Farar hula sun bijire wa sojoji tun bayan karbe iko da kasar a watan Fabrairu lokacin da suka yi juyin mulki, tare da hambarar da gwamnatin Shugaba Aung San Suu Kyi.

BBC ta zanta da mutum 11 da suka ga abin da ya faru a Kani, inda ta tattara shaidun da aka samu na hotuna da bidiyo tare da baza su domin tantance abin da ya faru wanda wata kungiya mai zaman kanta mai mazauni a Birtaniya ta yi cikakken bincike kan Myanmar.

Kashe-kashen da suka fi muni sun faru ne a kauyen Yin, inda aka azabtar da akalla maza 14, da lakada musu duka daga nan aka kashe su aka kuma jefar da gawawwakin a daji.

Wadanda suka shaida lamarin a Yin, da muka sauya sunayensu saboda dalilai na tsaro, sun shaida wa BBC an daure mazan da igiya, aka lakada musu duka sannan aka kashe su.

"Mun gagara tsayawa kallo, sai muka sunkuyar da kawunanmu kasa muna ta kuka," in ji wata mace da dan uwanta da dan 'yar uwarta da kuma kanin mjinita ke cikin wadanda aka kashe.

"Mun yi ta rokonsu kada su aikata hakan. Ba su damu ba sam. Sai suka tambayi matar, 'Akwai mijinki a cikinsu ne? idan akwai shi, kawai yi bankwana da shi '."

Wani da ya tsere wa kashe-kashen, ya ce sojojin sun ci zarafin mutanen fiye da tunani na tsawon awowi kafin su kashe su.

"An daure su, suka dinga dukansu da bindiga da duwatsu, sun sha azaba ta kwana guda," in ji shi.

"Wasu daga cikin sojojin matasa ne 'yan shekara 17 zuwa 18, wasu kuma tsofaffi ne sosai. Akwai wata mace a cikinsu."

An gano gawawwakin mutum 12 da aka gundulewa hannaye da kafafu, a kusa da kauyen Zee Bin Dwin, a karshen watan Yuli, an binne gawwawakin ne a wani katon rami, ciki har da wata gawa karama da ake kyautata zaton dan karamin yaro ne, an kuma ga gawar wani mai lalurar nakasa.

An samu gawar wani tsoho da ake zaton ya haura shekara 60, an daure shi a jikin bishiya a kusa da wurin. Nazarin hotunan gawar mutumin da BBC ta yi, ya nuna karara an azabtar da shi. 'Yan uwansa sun ce dansa da jikansa sun tsere da kauyen a lokacin da sojojin suka shiga kauyen, amma shi sai ya tsaya tunanin tun da shi tsoho ne za su tausaya masa.

Kashe-kashen sun nuna cewa na daukar fansa ne da kuma horas da mutanen kauyukan kan hare-haren da ake zargin farar hula sun kai wa sojojin da ke yankin. Fada tsakanin sojoji da dakarun 'yantar da yankin da kungiyoyin masu dauke da makamai ya munana a yankin cikin watannin da suka gabata, ciki har da taho-mu-gama da aka yi tsakaninsu a kusa da Zee Bin Dwin.

Bayanai da shaidun da BBC ta tattara, ciki har da jawabai, sun nuna sojojin sun mayar da hankali ne a kan mazan yankin, kamar yadda aka taba ganin hakan a kauyukan Myanmar, inda suke azabtar da su.

Iyalan wadanda saka kashe, sun kafe cewa mazajen ba sa cikin wadanda suka kai wa sojojin hare-hare. Wata mace da aka kashe dan uwanta a kisan kiyashin da aka yi a kauyen Yin, ta ce sai da ta dinga rokon sjojin tana cewa dan uwanta "ko danko ba zai iya harbawa ba bare bindiga".

Ta ce sojojin sun mayar da martani da cewa, "Kar ki kara cewa uffan. Mun gaji. Za mu kashe ki."

'Yan jaridar kasashen waje an haramta musu aiki a Myanmar tun bayan juyin mulkin da aka yi, an kuma rufe yawancoin gidajen radiyo da talbijin masu zaman kansu, lamarin da ke janyo matukar wuya kafin samun bayanai.

BBC ta tattara bayanan dukkan zarge-zargen da labaran cin zarafin da ake zargin sojojin Myanmar da aikata ga mukaddashin ministan yada labarai na Myanmar Janaral Zaw Min Tun. Kuma bai musanta sojojin sun aikata kashe-kashen ba.

"Za ta iya faruwa," in ji shi. "Idan suna kallon mu a matsayin makiya, muna da 'yancin kare kanmu."

A bangare guda kuma Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da bincike kan zarge-zargen take hakkin dan adam da aka aikata a Myanmar da wanda sojoji suka yi.