Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Silame: 'A kan idona iyayena da ƙannena uku suka ƙone har suka mutu'
Cikin shessheka, tana kuka tamkar rayuwarta za ta fita, da ƙyar Hauwa'u ta iya faɗa wa wakiliyar BBC sunanta.
Daga nan ta sake fashewa da kuka yayin da al'umma ke ƙoƙarin kwantar mata da hankali kan mummunan ibtila'in da ya afka mata da asubahin ranar Talata.
Wani harin jirgin yaƙi, da ake zargin na sojojin Najeriya ne ya hallaka mutum 10 da raunata wasu guda shida a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto, ta arewa maso yammacin Najeriya.
Cikin waɗanda suka mutu akwai mahaifi da mahaifiyar Hauwa'u da kuma ƙannenta huɗu.
Duk da cewa ya zuwa lokacin da aka yi jana'izar mutanen 10 da yammacin Laraba - kamar yadda wakiliyar BBC ta shaida - rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba, kuma babu wani jami'in soja da ya halarci jana'izar, wannan ba shi ne karon farko ko na biyu ko ma na uku da sojojin Najeriya ke kai harin 'kuskure' kan fararen hula ba.
Ɗaya daga cikin harin da sojojin suka kai na baya-bayan nan wanda har yanzu raunin da ya haifar a zukatan ƴan Najeriya bai warke ba, shi ne harin da jirgin soji maras matuƙi na rundunar sojin Najeriyar ya kai kan masu ibada a ƙuyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Hukumomi a jihar ta Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum 85 harin da aka kai kan masu taron Maulidi, domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a ranar 3 ga watan Disamban 2023.
Buhari - jihar Yobe a 15 ga watan Satumban 2021
Sai kuma harin da rundunar sojin saman Najeriya ta ce jirginta ya kai bisa kuskure kan ƙauyen Buhari da ke Yunusari a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya a watan Satumban 2021.
Shaidu sun ce harin jirgin saman ya kashe aƙalla mutum goma, baya ga gommai da suka jikkata, cikinsu har da mata da ƙananan yara.
A watan Janairun 2017 ma, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai hari a wani sansanin ƴan gudun hijirar rikicin Boko Haram da ke garin Rann - jihar Borno, a arewa maso gabashin ƙasar.
'Ina ganinsu suna ci da wuta'
Duk da ƙoƙarin kwantar mata da hankali da mutanen da ke kusa suka yi, iyakar abin da Hauwa'u ta ƙara iya wa BBC shi ne "ina ganin su suna ci da wuta, uwata da ubana da ƙannaina guda uku".
Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen da suka zanta da BBC, Usman Manuga ya ce lamarin ya faru ne bayan sallar Asubahin ranar ta Laraba.
"Bayan mun yi sallah mun fito, na je na gaida iyayena, sai na ji ana cewa ga jirage, ga jirage, na fito na gan su da idanuna.
"Ina nan sai na guda daga cikinsu ya buge mu."
Baya ga mutum 10 da suka mutu, da kuma waɗanda suka samu raunuka, akwai kimanin dabbobi 100 da aka ƙiyasta cewa harin ya kashe su.
Daga cikin dabbobin da harin ya kashe akwai raƙuma da shanu da kuma tumaki da jakuna.
An yi ne bisa kuskure - Ahmad Aliyu
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu wanda ya halarci jana'izar mutanen da suka rasu a harin ya ce harin an kai shi ne 'bisa kuskure'.
Wannan yanayi kaddara ce, su waɗannan jami'ai sun yi ne bisa kuskure, kuma sun yi ne domin bayar da kariya ga wannan al'umma"
"Kuna da labarin akwai wasu mutane da suka shigo wannan ƙasa, kuma ba wannan ne karo na farko da su(sojoji) suka kai musu farmaki ba, sun kai na farko, sun kai na biyu kuma sun kai na uku, kuma duk sun samu nasara, saboda haka wannan yana a matsayin kaddara, kuma a matsayinmu na Musulmi yana da kyau muna ɗauki kaddara, mai kyau ko akasin haka."
"Za mu haɗa kai da duk hukumomin da abin ya shaf domin mu ga an yi bincike an gano musabbabin abin da ya faru da kuma duba halin da za a bi domin kare sake afukwar hakan."
Gwamnan ya bayyana cewa ya kai wa al'ummar da lamarin ya rusta da ita tallafin abinci kimanin buhu 100 da kuma kuɗi kimanin naira miliyan 20.
Hari ta sama da ta ƙasa
A tattaunawarsa da BBC, Abubakar Muhammad ya ce "Tun da safe aka kira ni aka shaida min cewa an ji saukar bama-bamai, inda na bincika na tabbatar da faruwar hakan."
Shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya bayyana cewa shi da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na daga cikin waɗanda suka yi jana'izar mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin harin, ya ce "jirgin yaƙi guda biyu ne suka saki bama-bamai" a kan ƙauyukan.
"Wani wuri ne da ake kira Gidan Bisa da kuma Runtuwa waɗanda ke a mazaɓata."
"Hare-hare ne babu ƙaƙautawa," waɗanda Abubakar ya bayyana cewa sojojin ba su tsaya da kaiwa ba har sai da gwamnatin jihar ta sanya baki.
Ya ƙara da cewa "Sojojin sama ne da na ƙasa suka kai harin, sojojin sama sun shiga yankin da manyan tankokin yaƙi."
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce baya ga mutum 10 da suka mutu, akwai kuma mutum shida da suka samu raunuka.
Ƙauyukan na kusa da jejin Surame da ake ganin maɓuyar mayaƙan ƙungiyar Lakurawa da ta ɓulla a ƙasar a baya-bayan nan.
Wannan shi ne hari irinsa na tara a Najeriya
Wannan ba shi ne karon farko da sojojin Najeriya ke kai irin wannan hari ba da suke cewa na kuskure ne a kan farar hula.
Irin wannan hari na baya-bayan nan shi ne na daren ranar Lahadi, 3 ga watan Disamban, 2023, inda wani jirgi mara matuki na sojojin Najeriya ya kai hari har sau biyu kan dandazon mutane da ke halattar taron Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Lamarin da sojoji suka ce sun yi ne bisa kuskren cewa taro ne na 'yan ta'adda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100 da kuma raunata wasu masu dimbin yawa.
Har zuwa wannan lokaci akwai wasu da yawa da suka ji rauni a harin na Tudun Biri da suka bayyana wa BBC cewa an ma daina yi musu magani na raunukan da suka ji, wanda kuma har yanzu suna jinya.
Wani bincike da BBC ta yi ya nuna cewa sojojin Najeriya sun kai irin wannan harin kan farar hula, da suke dangantawa da kuskure guda takwas inda wannan ya kasance na tara a lokuta daban-daban, daga shekarar 2022 zuwa ranar da aka kai wannan na ƙauyukan ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto - Laraba, 25 ga watan Disamban 2024.