'Shugabanni ko a jikinsu': Ran ƴan Najeriya ya ɓaci game da ƙarin kuɗin man fetur

Litar man gfetur a Najeriya
Bayanan hoto, NNPCL ya ƙara kuɗin fetur din ne bayan sanar da cewa yana fama da matsalolin kuɗi a farkon makon nan
    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Alamu na nuna cewa ƴan Najeriya sun fara gajiya da nuna ɓacin rai kan ƙarin kuɗin man fetur da suka saba gani, a madadin haka sun koma yin shaguɓe game da ƙarin farashin da gwamnati ta yi na baya-bayan nan.

Sanarwar da kamfanin man fetur na NNPCL ya fitar ranar Talata cewa ya ƙara farashin litar man fetur daga naira 617 zuwa 897 ta zo ne a ranar da ya kamata ƴan ƙasa su ji ƙwarin gwiwa ko ma murna saboda labarin da ke cewa matatar mai ta Dangote na dab da fara sayar da man fetur a cikin gida.

Sai dai ma'abota shafukan sada zumunta na can na ɗebe wa juna kewa da kalamai iri-iri da suka shafi ƙarin kuɗin man fetur ɗin.

Ƙarin abin da ya ta'azzara lamarin shi ne yadda labarin ya same su cikin mawuyacin hali na tsadar kaya, da kuma wahalar da ake sha wajen samun man fetur ɗin a faɗin ƙasa.

"Cire tallafin mai zai saukar da farashinsa kuma ya sa a daina wahalarsa. Kuɗin da aka adana daga tallafin za a zuba su a harkar lafiya, da ilimi, da more rayuwa. Jamhuriyar Wahala ke nan," kamar yadda wani da ya kira kansa K-Kay a dandalin X ya yi shaguɓe.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Sabon ƙarin na zuwa ne kwana ɗaya bayan NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya suka yi hasashen yana koƙarin sanar da sabon farashi ne.

Farashin fetur a Najeriya ya yi tashin gwauron zabi ne tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2023 - lokacin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin da gwamnati ke biya.

Nan take litar mai ta koma sama da naira 500 daga ƙasa da naira 200, inda daga baya ta koma sama da naira 600, kafin yanzu ta koma 897 a hannun NNPCL. Tun kafin yanzu farashin litar man fetur ɗin ta zarta naira1,000 a wasu jihohin arewacin Najeriya.

'Shugabanni ko a jikinsu'

Jim kaɗan bayan sanarwar ƙarin kuɗin man ne kuma aka fara yaɗa labarin cewa gwamnatin Najeriya ta umarci NNPCL ya ƙara kuɗin, zargin da ma'aikatar man fetur ta musanta.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce "ma'aikatar man fetur ba ta taɓa ba kuma ba za ta taɓa saka baki game da matakan da NNPCL ke ɗauka ba, ciki har da yanka farashi".

Sai dai, hakan bai hana wasu ƴan Najeriya zargin gwamnatin da hannu wajen ƙara kuɗin ba, musamman ganin cewa da wuya a ɗauki babban mataki irin wannan ba tare da sanin shugaban ƙasa ba.

Wani mai suna Abdu Hashimu a Facebook ya ce: "Fetur na ta ƙara kuɗi. Yunwa na cigaba da azabtar da al'umma. Shugabanni ko a jikinsu. Najeriya ke nan."

Kauce wa Facebook, 1
Ya kamata a bar bayanan Facebook?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

A gefe guda kuma, ƙarin bai zo wa wasu da mamaki ba saboda da ma can suna sayen man a kan farashin da aka ƙara a yanzu.

"Sai yanzu wasu jihohi ke alhinin tashin farashin fetur zuwa N950," a cewar wani mai suna Kabiru Shehu Doma - kodayake bai faɗi daga wace jiha yake ba.

Kauce wa Facebook, 2
Ya kamata a bar bayanan Facebook?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2

Sai dai akwai yiwuwar za su fuskanci ƙari kan abin da suka saba sayen saboda ƴan kasuwar man fetur ɗin na cigaba da ƙorafin cewa suna samun man ne a hannun dillalai ƴan kasuwa a maimakon NNPCL.

Wasu kuma sun yi amfani da wannan damar wajen yin shaguɓe ga masu cewa yi wa shugabanni zanga-zanga haramun ne. "To ina mafita?" in ji shi.

Kauce wa Facebook, 3
Ya kamata a bar bayanan Facebook?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 3

"In Allah ya yarda sai man fetur ɗin Najeriya ya ƙare," kamar yadda wata da ta kira kan ta Aishat Aliyu Rano ta nuna nata ɓacin ran a Facebook.

Kauce wa Facebook, 4
Ya kamata a bar bayanan Facebook?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 4

Wasu kuma sun bayyana lamarin a matsayin "zalunci".

Kauce wa Facebook, 5
Ya kamata a bar bayanan Facebook?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Facebook suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Facebook da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 5

Injinanku ba za su sake fuskantar matsala ba - Dangote

Aliko Dangote

Asalin hoton, Dangote Group

Bayanan hoto, Aliko Dangote (tsakiya) ɗauke da samfurin man fetur da matatarsa ta fara tacewa ranar Talata

Sugaban kamfanin matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa da zarar kamfaninsa ya kammala wasu muhimman abubuwa da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), man fetur ɗin kamfanin nasa zai shiga kasuwa.

Dangote ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa za su iya sa ran samun man fetur mai inganci da daɗewa.

"Ba za ku ƙara fuskantar matsalolin da injinan motoci ke ba ku ba," in ji Dangote.

“Man fetur ɗinmu zai yi daidai da na kowace ƙasa a duniya; babu wanda zai wuce mu ta fuskar inganci."

Masana da masu sharhi sun yi tunanin shigowar fetur na dangote kasuwa za ta iya taimakawa wajen sauƙaƙa farashi da kuma wahalarsa da aka saba yi a Najeriya, sai dai da wuya hakan ta samu ganin yadda ake yawan ƙara kuɗinsa akai-akai.