Yadda mutum huɗu suka mallaki rabin dukiyar Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ousmane Badiane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
- Lokacin karatu: Minti 5
An kiyasta cewa kuɗin da wasu ƴan Afirka huɗu ke da shi ya kai dala biliyan 57.4, sama da ɗaukacin duƙiyar ƴan Afirka miliyan 750, ko kuma rabin duƙiyar al'ummar nahiyar.
Wasu za su yi mamakin jin haka, sai dai hakan gaskiya ne kamar yadda rahoton da ƙungiyar agaji ta Oxfam ta fitar a watan Yulin 2025 ya bayyana.
A cewar wasu wannan ya faru ne sakamakon ɓullo da wasu tsare-tsaren tattalin arziki da suka fifita masu kuɗi, wanda ya yi watsi da masu aikin gwamnati da kuma yaƙi da cin hanci.
Oxfam ta yi kiran samar da daidaito a ɓangaren haraji domin rage rashin daidaito da samar da kuɗi ga ɓangaren ilimi, lafiya da kuma ruwan sha.
Amma su waye ne waɗannan hamshaƙan masu kuɗin, waɗanda suka fi mutum kusan biliyan ɗaya kuɗi kuma ta yaya suka samu arzikinsu?
Aliko Dangote, Nijeriya (dala biliyan 23.3)

Asalin hoton, Getty Images
Aliko Dangote, ɗan kasuwa ne a Najeriya wanda aka haifa ranar 10 ga Afrilun 1957 a jihar Kano.
Ana ɗaukarsa a matsayin waɗanda suka fi samun tagomashi a ɓangaren kasuwanci a Afirka.
Shi ne wanda ya kafa kamfanin Dangote group, kuma shi ne mutum mafi arziki a nahiyar Afirka.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Aliko Dangote ya shahara a ɓangarorin kasuwanci da dama waɗanda suka haɗa da: sumunti, gishiri, fulawa, taki da kuma fetur da iskar gas.
Ya fito ne daga iyali masu kuɗi, inda ya samu nasarar ɗorawa kan abin da aka fi sanin iyalinsu na harkar kasuwanci.
Dangote ya fara harkar kasuwanci ne a jihar Legas a 1977, lokacin yana ɗan shekara 20, bayan da ya karɓi bashi a wurin kawunsa. Ya fara shigo da shinkafa da siga da kuma sumunti - inda ya riƙa sayar da su a Najeriya.
Kasuwancinsa ya haɓaka nan take saboda kyakkyawar alaƙa da yake da ita da jama'a da kuma iya kasuwanci.
Dangote ya yanke shawarar zuba jari don fara samar da abubuwa a cikin gida a shekarun 1990 zuwa 2000.
Daga nan ya fara kamfanonin siga da kuma gishiri da kuma fulowa.
Ya zama na farko wajen samar da sumunti a yankin Sahara na Afirka.
Tun 2010, kamfanin Dangote ya fara faɗaɗa kasuwancinsa ta hanyar ɓullo da sabbin tsare-tsare a ɓangarori da dama da suka haɗa da: kafa ɗaya daga cikin matatar fetur mafi girma a duniya wanda aka kaddamar a 2023, da samar da taki da kuma zuba jari a fannin noma da kuma sufuri.
ya kuma faɗaɗa kamfaninsa zuwa wajen Najeriya, inda ya gina kamfanonin samar da sumunyi a Senegal, Habasha, Tanzaniya da kuma Afrika ta Kudu.
Johann Rupert, Afrika ta Kudu (dala biliyan 14.2)

Asalin hoton, Getty Images
Johann Rupert ɗan kasuwa ne da ya fito daga Afirka ta Kudu - an haife shi a watan Yunin 1950 a Stellenbosch, da ke Afirka ta Kudu.
An fi saninsa a matsayin shugaban Richemont Group, ɗaya daga cikin kamfanoni masu arziki a duniya.
Johann Rupert ɗa ne ga Anton Rupert, wani hamshaƙin ɗan kasuwa a Afirka ta Kudu wanda ya kirkiro da kamfanin Remgro, wanda a farko yake samar da taba kafin daga baya ya sauya alkibla.
Johann ya gaji wani ɓangare na duƙiyarsa, inda ya taka rawa wajen faɗaɗa ta.
A 1988, Johann Rupert ya kirkiro da Richemont Group a Switzerland.
Richemont ya zama hamshakin mai kamfanonin kayan ƙawa, inda ya mallaki kamfanonin haɗa kaya kamar Cartier, Van Cleef & Arpels, Montblanc, Piaget, IWC da kuma Vacheron Constantin.
Kamfanin ya mayar da hankali wajen samar da agoguna da sarkoki da sauran kayan alatu, wanda wani ɓangare ne da ke ƙara girma a duniya.
A lokaci guda, Rupert ya ci gaba da jagoranta da kuma haɓaka kamfaninsa na Remgro, inda ya zuba jari a fannoni daban-daban: fannin kuɗi, lafiya, abinci da kuma sadarwa.
A cewar mujallar Forbes a 2025, Johann Rupert ya kasance ɗaya daga cikin mafiya tattalin arziki a Afirka, inda aka kiyasta cewa duƙiyarsa ta kai kusan dala biliyan 15.
A wani lokaci, ya taɓa zarta gaban Aliko Dangote a matsayin mafi arziki a nahiyar Afirka.
Nicky Oppenheimer, Afirka ta Kudu (dala biliyan 10.2)

Asalin hoton, Getty Images
Nicky Oppenheimer, wanda aka haifa 8 ga Yunin 1945, ya kasance biloniya ɗan Afirka ta Kudu - kuma ɗaya daga cikin mafiya shahara a masana'antar zinare.
Iyalinsa sun gina arzikunsu ne daga kasuwancin zinare - suna da kamfani mai suna De Beers wanda shahara wajen haƙar zinare.
Ya yi karatu a makarantar Harrow da ke Birtaniya da kuma Christ Church a birni Oxford - inda ya samu digiri a ɓangaren siyasa, tattalin arziki da kuma falsafa.
A shekarun 1970, Nicky ya shiga cikin harkar kasuwanci da iyalansa ke yi har ya girma, inda ya zama shugaban kamfanin De Beers.
Karkashin jagorancinsa, De Beers ya faɗaɗa daga kamfanin da ke haƙar zinare zuwa wasu fannonin, inda ya mayar da hankali kan saye da sayarwa.
A 2012, ya kafa wani tarihi bayan da ya sayar da hannun jarinsa a cikin kamfanin wanda ya kai kashi 40 ga wani kamfani a Amurka kan dala biliyan 5.1.
Duk da cewa ya yi ritaya daga kamfanin De Beers, Mista Oppenheimer ya cigaba da zama jigo a harkar kasuwanci a duniya. Tuni ya mayar da hankali kan lura da arzikin iyalansa ta hanyar zuba jari a fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, yawon buɗe ido da sauransu.
Nassef Sawiris, Masar (dala biliyan 9.4)

Asalin hoton, Getty Images
An haife shi a ranar 19 ga watan Janairun 1961, ya kasance ɗan kasuwa kuma biloniya daga ƙasar Masar kuma ɗaya daga cikin masu arziki a Afirka da ƙasashen Larabawa.
Shi karamin ɗa ga Onsi Sawiris, wanda ya kirkiro da kamfdanin Orascom.
Ya samu digiri a fannin tattalin arziki daga jami'ar jihar Chicago a Amurka, inda ya zama mai ƙarfin faɗa a ji a zuriyar Sawiris. Ƴan uwansa sun haɗa da Naguib Sawiris da Samih Sawiris.
Kamfaninsu na OCI (wanda aka fi sani da Orascom a baya) ya shahara wajen samar da taki da sauran magunguna da kuma ɓangaren gine-gine.
A 2023, OCI ya haɗa aikace-aikacensa na samar da taki a Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka da kamfanin ADNOC.
Shi ne wanda ya fi hannun jari a kamfanin samar da kayayyakin kwallon kafa na Adidas AG na Jamus, inda yake da kusan kashi 10
Ana ci gaba da ɗaukarsa a matsayin mutum mafi arziki a Masar, kuma ɗaya daga cikin mafiya arziki a Afirka da ƙasashen Larabawa.
An kiyasta cewa duƙiyarsa ta kai dala biliyan takwas zuwa tara zuwa 2024/2025.
Ya fi samun kuɗinsa daga kamfanin OCI/ADNOC Fertiglobe da kuma Adidas AG.
Ya bayar da tallafin dala miliyan 20 ga jami'ar Chicago (inda ya yi karatu) domin taimakawa ɗaliban Masar wajen yin karatu.











