Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa bakwai da suka kamata ku sani kan shayar da nonon uwa
- Marubuci, Efrem Gebreab
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Alƙaluman baya-bayan nan na UNICEF sun nuna cewa, rashin isasshen shayar da nonon uwa ne ke haifar da kashi 16 cikin 100 na mace-macen yara a kowace shekara.
Dangane da magance wannan matsalolin, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira da a ƙara tallafi ga iyaye mata masu shayarwa daga al'ummomi da dama da kuma ƙwararrun masana kiwon lafiya a duniya.
Wannan ya haɗa da kafa tsarin kula da shayarwa, da kiyaye haƙƙin mata wajen shayar da nono a kowane lokaci da kuma a ko'ina, da kuma haɓaka tallafin al'umma.
Taken wannan shekarar ta makon shayarwa na duniya, wanda yake gudana a farkon makon Agusta na kowace shekara shi ne "Cike giɓin: Tallafin Shayarwa ga kowace mace."
Duk da fa'idojin shayarwa, mata na fuskantar ƙalubale da matsalolin da ke hana su shayarwa a wasu wuraren da suke tsintar kansu.
Saboda har yanzu akwai shaci-faɗi kan shayarwa da ke hana mata ƙoƙarin shayar da jariransu a wasu wuraren da suka samu kansu.
Dalilin haka ne ya sa muka tuntuɓi masana biyu: Catriona Waitt, Farfesa a harkar kiwon lafiya a Jami'ar Liverpool kuma mai bincike a Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jami'ar Makerere a Kampala, Uganda; da Alastair Sutcliffe, farfesa a fannin ilimin yara a Jami'ar University College da ke Landan.
Shanci-Fadi na 1: An saba cewa shayarwa na raunata kan nonon uwa
Ferfesa Waitt ta ce ba wani abu ba ne idan mace ta fara jin rashin jin dadi ko zafi da kuma ciwo kan nononta da zarar ta fara shayarwa kamar al`adace har ta saba ya bi jikinta.
Amma kuma ta ce idan zafin ya wuce gona da iri, zai iya yiwuwa kan nonuwan sun kamu da wata cuta ne ko kuma jaririn ba ya shan nonon yadda ya kamata.
Shaci-faɗi na 2: Mace ba za ta iya shayarwa ba idan ba ta fara nan take ba
Ferfesa Sutcliffe ya ce duk wani abu da za tallafawa uwa wajen shayar da jaririnta a duk inda ta samu kanta na da kyau ga lafiyar ɗan‘adam.
Ya ƙara da cewa duk wani abu ko al`amari da zai hana uwa shayar da ɗanta saboda wani shaci-faɗi, ba a kimmiyance ba ne. Amma akwai fa'idoji sosai wajen dora jariri kan nonon uwa da zarar an haife shi.
Gina jikin jariri da ƙara kuzari na ɗaya daga cikin fa’idojin, shayarwa na kuma taimakawa wajen magance matsalolin da ke tattare da mahaifa, kamar hana ko rage zubar jini na mahaifa bayan haihuwa.
Har ila yau, a cikin 'yan kwanaki na farko bayan haihuwa, jikin uwar na samar da wani takamaiman sinadari mai gina jiki mai suna colostrum wanda ke da matukar amfani idan jariri ya fara da shi.
Shaci-fadi na 3: Mace mai shayarwa ba za ta iya shan wani magani ba
Ferfasa Waitt ta ce tambaya ta farko da uwar da shayarwa ke yi shine, ko za ta iya shan ko wane irin magani kuma ba zai yi wa jarirnta illa ba?
Maganar gaskiya a nan in ji ferfesar shine duk wani magani da uwa ta sha zai shafi jaririnta ko da a yanayi mafi ƙanƙanta ne. Saboda haka idan likita ya bai wa uwa magani, ta tambaye shi ko zai yi wa jaririnta illa, duk da cewa dai likitoci ba za su bai wa uwa mai shayarwa maganin da zai cuci jaririnta ba idan har sun san tana shayarwa.
Ferfesar ta ce abin da jariri ke buƙata shine uwa mai lafiya
Shaci-faɗi na 4: Uwar da ke shayarwa ta guji abinci mai yaji kafin bai wa jariri nono
Ferfesa Waitt ta ƙara da cewa babu wani abincin da aka haramtawa uwar da ke shayarwa ci, sai dai kuma yanayin ruwan nono uwa ya dangantane da irin abubuwan da take ci wanda zai nuna mata alamun sun karɓi jaririn da kuma waɗanda ba su ƙarbi jaririn ba.
Shaci-fadi na 5: Kada uwa ta yi amfani da wani abincin jariri ban da ruwan nono
Ferfesa Waitt ta ce wannan ba dole ba ne amma kuma samar da nono yana aiki ne a kan tsarin samarwa da kuma buƙatu. Jikin uwa yana samar da isasshen ruwan nono dangane da yadda jaririnku yake shan nonon.
Idan uwa tana shayar da jariri ba yadda ya kamata ba, to samar da ruwan nono na iya raguwa saboda jikinta yana samun ƙarancin sigina ba kamar yadda ya kamata ba.
Yin amfani da sauran nau’ukan abincin jariri a lokaci-lokaci ba zai hana shayarwa ba amma kuma zai takaita samar da isashen ruwan nono ga uwa.
Shaci-faɗi na 6: Kada uwa ta shayar da jaririnta idan ba ta da lafiya
Ferfesa Sutcliffe ya ce wannan shaci-faɗi ne. Babban yanayin da zai hana uwa shayar da jaririnta shi ne idan tana da cutar HIV ko ciwon hanta, su ma kuma saboda cuttutuka ne da ɗan zai iya kamuwa da su.
Amma a lokuta da dama, uwa za ta iya ci gaba da shayar da ɗanta idan ba ta da lafiya saboda jikinta na samar da sinadiran da za su kare jaririn.
Ya ce yana da wahala a ga cutar da jariri ya kamu ta ita ta hanyar shan ruwan nono.
Shaci-faɗi na 7: Yana da wahala a yaye yaro daga shan nono idan aka shayar da shi sama da shekara ɗaya
Ferfesa Waitt ta ce Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta bayar da shawarar shayar da jariri nono zalla har tsawon watanni shida sai daga nan a fara ba shi wasu nau’ukan abinci, amma kuma uwa za ta iya ci gaba da shayar da yaronta har tsawon yadda take so. Babu wani takamaiman lokacin da aka ce uwa ta dakatar da shayar da yaronta.
A wasu ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziƙi kamar Birtaniya, ana yaye jarirai yawanci daga shekara ɗaya zuwa biyu, amma kuma a sauran ƙasashen da ba su da ƙarfin tattalin arziƙi kamar Uganda, ana yaye yaro daga shekara biyu zuwa uku.
Sai dai kuma babbar matsalar da ƙasashe da dama ke fuskanta ita ce rashin isassun ranakun hutun haihuwa daga wajen aiki da zai bar iyaye mata su shayar da jariransu ta yadda WHO ta bayar da shawara.