Yadda yaran Gaza suka daina tsoron mutuwa da tashin bama-bamai
Daga Anna Foster

Asalin hoton, Family
Hala ba ta san haɗarin da ke fuskantar su ba lokacin da ta ɗauki ‘yarta zuwa bakin ruwa.
‘Yarta Layan mai shekara tara ta nemi ta yi wasa a kan yashi don ta ɗan sarara a kusa da ruwa.
Yayin da iyalin suke tafiya a cikin babur mai ƙafa uku, sun wuce wani sansanin soja na mayaƙan ƙungiyar Falasɗinawa ta Palestinian Islamic Jihad (PIJ). A daidai lokacin ne kuma dakarun Isra’ila suka kai wa wurin hari.
Ɓaraguzan makamin ya ɓula wuyan Layan, kuma nan take ta faɗi a ƙasa cikin jini. Mako guda da aka shafe ana jinyarta a wani asibiti da ke Isra’ila bai iya ceto ranta ba.
“A ɗimauce nake,” kamar yadda ta faɗa min. “Ya kamata a ce na zama mai ƙarfin hali saboda ni uwar yarinyar da ta yi shahada ce, amma tashe-tashen hankali da na gani sun girgiza ni tare da dangina. Waɗannan abubuwa sun sa na ji na tsani zama a Gaza.”
Tana riƙe da wata ‘yar-cana a hannunta lokacin da muke magana. Kyauta ce ta musamman da aka bai wa ‘yar tata saboda nasarar da ta yi a wata gasar rawa ta Falasɗinawa.
Na tambaye ta ko tana ganin mutuwar Layan za ta sauya wani abu. “Ba na tunanin haka, saboda an kashe wasu da yawa kafinta kuma babu abin da ya sauya,” in ji ta. “Irin wannan bai taɓa girgiza zuciyar mahukunta ba a nan. Abin ya bi jiki.”
Bayan gwabzawar da aka yi, an kashe mutane a birnin Gaza. Wannan karon Ma’aikatar Lafiya a Gazan ta ce an kashe farar hula 35.
Firaministan Isra’ila Yair Lapid ya ce sai sun yi da gaske suke iya kauce wa kai hari kan fararen hula.
“Isra’ila ba za ta nemi afuwa ba don ta yi amfani da ƙarfi wajen kare ‘yan ƙasarta,” in ji shi, “amma kashe fararen hula, musamman yara, abin takaici ne.”
Rundunar Sojan Isra’ila ta ce “ta kaɗu da kisan Layan da sauran fararen hula”.
Na bi jana’izar Layan tun daga wani masallaci har zuwa maƙabarta. Dandazon mutane ɗauke da tutocin ƙungiyar gwagwarmaya na harba bindigogi.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai irin wannan ƙaramin ƙabarin a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia.
Wannan karon na wasu ƙananan yara ne biyar da ke wasa a wata maƙabarta lokacin da wani abu ya fashe. Isra’ila ta zargi cewa makamin roka ne da mayaƙan Palestinian Islamic Jihad suka harba ya faɗa wurin.
‘Yan gwagwarmyar sun zargi Isra’ila da kai harin.
Ɗaya daga cikin mai suna Mohammed na da shekara 17. Burinsa ya zama ɗan sanda, kamar yadda mahaifiyarsa ta faɗa min.
“Yara ne kawai suke wasansu. Kawai sai muka ji fashewar. Iyayensu maza ne suka isa wurin a guje suka ɗauke matattun yaran nasu,” a cewarta.
"Ƴa’yanmu sun saba da ganin kashe-kashe da ƙarar bama-bamai. Sun bambanta da sauran yara a faɗin duniya, waɗanda suke zaune cikin kwanciyar hankali suna zuwa wuraren shaƙatawa – ba maƙabartu ba – don su yi wasa.”
‘Yan awanni bayan faruwar lamarin a maƙabartar, wani bidiyo ya karaɗe shafukan zumunta, musamman a Tik Tok, na Khalil Alkahlout wanda ya ruga don duba nasa yaran.
Yayin da ake tsaka da zaƙulo gawarwakin yaran, sai ya fara ihu yana dukan ƙirjinsa. Wani abokinsa da ke gefe sai ya fara ɗaukarsa a waya.
“Duka wannan don a faranta wa Islamic Jihad,” a cewar Khalil cikin fushi. “Me ya sa? Kawia saboda tana son a saki Bassem Saadi, shi ne kuma ake kashe mana ‘ya’yanmu ƙanana.”
Mutumin da ya ambata – Bassem Saadi – jagora ne na ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad da sojojin Isra’ila suka kama a Gabar Yamma da Kogin Jordan, kuma abin da ya jawo fafatawar ke nan ta baya-bayan nan.
Bidiyon Khalil ya burge mutane da dama a shafukan zumunta, inda dubbai suka nuna sha’awarsu. Sai dai da kyar za ka ji ana sukar ‘yan gwagwarmaya a Gaza.
Ya ce: “Bidiyona ya burge mutane. Ya girgiza mutane saboda ba sa son yaƙi, ba sa son mutuwa, ba sa son a kashe yara.
“Idan na yi magana nakan ce lokacin bai dace da na tsokana ba. Duk wanda ya gan ni a titi sai ya ce na faɗi abin da ke cikin zuciyarsu wanda ba za su iya faɗa ba. Sukan jinjina min, su ce ‘ka yi daidai’.”
Isra’ila ta fara kai hare-haren ne da yammacin Juma’a saboda abin da ta kira cewa shirin da ƙungiyar ta masu jihadi ke yi na kai hare-hare kan ‘yan Isra’ila. Ta kashe jagororin ƙungiyar biyu a hare-haren.

Na haura ta saman rufin madafar Samir da aka lalata don na yi magana da shi. Sai ga jikarsa mai suna Tuta ‘yar shekara uku tana yawo cikin ginin da aka yi kaca-kaca da shi.
Ya faɗa min yadda sojojin Isra’ila suka kira shi suka ce masa ya tattara kayansa da na maƙwabta su fice daga wurin saboda za a kawo hari. Sun koma bakin ruwa kuma daga can suka dinga jin bam na sauka a wurin.
Lokacin da Samir ya koma ya tarar da wani ɓangare a ɗaiɗaice.
“Baki ɗayanmu muna fama da matsala a ƙwaƙwalwarmu,” a cewarsa. “Zaman lafiya muke so, ba ma son yaƙi.”
Samir bai san yadda za a yi ya sake gina gidansa ba. Abu ne da aka daɗe ana fama da shi a Gaza.
Da ƙyar ake samun kayayyakin gini a birnin saboda Isra’ila ta datse shiga da su yankin saboda tsoron ‘yan gwagwarmaya za su iya amfani da su wajen kai hare-hare.

Ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad ce ta harba dukkan makaman zuwa Isra’ila, wata ƙaramar ƙungiya maras manyan makamai. Da yawa daga cikin rokokin sun faɗa kan Gaza maimakon Isra’ilar inda suka dinga haddasa mutuwa da raunata mutane.
Kasancewar ƙungiyar Hamas ba ta shiga yaƙin ba, hakan na nufin rikicin na yanzu ba mai girma ba ne, kwana uku kacal aka kwashe kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Da a ce ta shiga faɗan, da abin ya zarta haka, ko kuma ma ya haifar da sabon yaƙi.
To me ya sa Hamas ba ta shiga ba a wannan karon?
“Ina ganin ya kamata mu koyi darasi daga wannan faɗan,” a cewar Ghazi Hamad, mai magana da yawun ƙungiyar.
“Ina ganin muna da haɗin kai da Islamic Jihad, mun yi tattaunawar fahimta da su. Ya kamata mu yi aiki tare a matsayin ƙungiyoyin Falasɗinawa.
"Saboda haka ina ganin za mu iya rage yawan kura-kurai , mu rage wahalhalun da da Falasɗinawa ke ciki.”
Na tambaye shi game da makaman rokar da Hamas take harbawa kan fararen hula na Isra’ila waɗanda kasar take cewa saboda haka ne take kare kanta.
Ya ba da amsa da cewa: “Ba ma yaƙi da kowa, mamaya kawai muke yaƙa. Isra’ila na da damar da za ta guje wa kashe farar hula, amma ina ganin idan tana son wani ɗan gwagwarmaya sai ta kashe dukkan mutanen da ke tare da shi don ta kashe shi.”
Bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya, Mista Lapid ya ce yana so “ya yi magana kai-tsaye da mazauna Zirin Gaza don ya faɗa musu cewa: Za a iya bin wasu hanyoyin”.











