Bayani kan asalin rikicin Isra'ila da Gaza

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da bude wuta tsakanin Isra'ila da 'yan gwagwarmayar Falasdinawa bayan rikicin kwana uku wanda ya lakume ran akalla Falasdinawa 44.
Wannan shi ne rikici mafi muni tun bayan wani kamarsa da aka yi na kwana 11 a watan Mayu na 2021.
Masar, wadda ta saba shiga tsakani a rikicin na Isra'ila da Falasdinawa, ita ce a wannan karon ma ta jagoranci yarjejeniyar.
Isra'ila ce ta fara janyo wannan rikicin ta hanyar kai hare-hare a wuraren da ke Zirin Gaza, bisa hujjar cewa martani ne ga barazanar da wata kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa mai suna da Ingilishi Palestinian Islamic Jihad (PIJ).
Lamarin ya haddasa tashin-tashina ta tsawon kwanaki bayan da Isra'ila ta kama wani babban jami'in kungiyar ta PIJ a yankin Gabar Yammacin Kojin Jordan da Isra'ilar ta mamaye.
Batu ne na shekara 100

Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya ta kwace iko da wannan yanki da ake kira Falasdinu bayan da aka ci Daular Usmaniyya, wadda wannan yankin na Gabas ta Tsakiya ke karkashin ikonta a lokacin, a yakin duniya na daya.
A lokacin Yahudawa ne 'yan kadan da kuma Larabawa da ke da rinjaye ke zaune a yankin.
Rikici ya fara tashi a lokacin da manyan kasashen duniya suka bai wa Birtaniya ikon kafa abin da suka kira kasar Yahudawa a wurin.
Yahudawa sun ce kasar kakanninsu ta asali ne, kamar yadda su ma Larabawan Falasdinu ke ikirari suka kuma ki wannan shiri na kafa kasar Yahudawa a wurin.

Asalin hoton, Getty Images
Tsakanin shekarun 1920 da shekarun 1940 yawan Yahudawan da ke komawa can ya karu, inda yawancinsu suke gudu daga gallazawar da ake musu a Turai bayan kisan-gillar Yahudawa na yakin duniya na biyu.
Haka kuma tashin hankali tsakanin Yahudawa da Larabawa a kan kin yarda da mulkin Birtaniya ya karu.
A 1947 Majalisar Dinikin Duniya ta kada kuria'r raba yankin na Falasdinu biyu inda za a kafa kasar Isra'ila da kuma ta Larabawa, yayin da birnin Kudus zai kasance na duniya wato mallakar kasashen biyu.
Shugabannin Yahudawa sun amince da wannan tsari yayin da na Larabawa suka yi watsi da shi, inda aka kasa aiwatar da shi.

Asalin hoton, Getty Images
Kafa kasar Isra'ila da korar Falasdinawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lokacin da mahukuntar Birtaniya suka kasa shawo kan matsalar a 1948, sai suka fice suka tafi, daga nan sai shugabannin Yahudawa suka yi amfani da wannan dama suka kafa kasar Isra'ila.
Falasdinawa da dama suka ki yarda da hakan sai kawai yaki ya biyo baya.
Dakaru daga kasashen Larabawa masu makwabtaka sai suka shigo su ma suka yi mamaya.
Bayan da yaki ya yi yaki, dubban Falasdinawa sun tsere ko kuma an tilasata musu barin gidajensu a abin da suka kira Al Nakba.
Zuwa lokacin da aka gama yakin da yarjejeniyar dakatar da bude wuta a wannan shekara, Isra'ila ta kame mafi yawan yankunan.
Yankin da Jordan ta kama ya zama Gabar Yammacin Kogin Jordan, wanda Masar ta kama kuma ya zama Gaza.
An raba Kudus tsakanin sojojin Isra'ila a Yamma da kuma na Jordan a Gabas.
Kasancewar an kawo karshen yakin ne ba tare da wata cikakkiyar yarjejeniya ba an ci gaba da yakin daga lokaci zuwa lokaci inda kowane bangare ko dora wa daya bangaren laifi a gomman shekaru.
Taswira da iyakokin Isra'ila a yau

A wani yakin kuma na 1967, Isra'ila ta mamaye Gabashin Isra'ila da Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma yawancin Tuddan Golan hadi da Gaza da kuma tsibirin Sinu na Masar.
Yawancin 'yan gudun hijirar Falasdinu suna zaune a Gaza da Gabar yamma da kuma yankunan kasashen Jordan da Syria da kuma Lebanon.
Tun daga sannan Isra'ila ta hana wadannan Falasdinawa ko 'ya'aynsu komawa su zauna a yankunans.
Isra'ila ta kafe a kan haka ne da cewa za su mamaye kasar, wanda hakan zai zama barazana ga wanzuwar kasar Yahudu.

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Isra'ila ce ke mamaye da Gabar Yamma, kuma duk da cewa ta fice daga Gaza, Majalisar Dinkin Duniya tana daukar wannan yankin a matsayin wanda Isra'ila ta mamaye.
Isra'ila na ikirarin cewa dukkanin Birnin Kudus babban birninta ne yayin da Falasdinawa ke cewa Gabashin Birnin shi ne zai kasance babban birnin kasarsu idan aka kafa ta.
Amurka ce kasa daya tilo daga cikin 'yan kalilan din da suka amince da birnin a matsayin babban birnin Isra'ila.
A cikin shekara 50 da ta gabata Isra'ila ta gina gidajen Yahudawa a wadannan yankuna inda a yanzu ake da Yahudawa sama da 60,000.
Falasdinu na cewa wannan ya keta ka'idar dokokin duniya kuma tarnaki ne ga zaman lafiya, amma kuma Isra'ila na musanta hakan.
Me yake faruwa yanzu?

Asalin hoton, Getty Images
Yawanci ana zaman dar-dar da samun tashin hankali a tsakanin Isra'ila da Falasdinawan da ke zaune a Gabashin Birnin Kudus da Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Kungiyar gawgawramayar Falasdinawa ta Hamas wadda a lokuta da dama take yakar Isra'ila ita ce ke mulkin Gaza.
Hukumomin Isra'ila da na Masar na tsananta iko da iyakar Gaza domin hana makamai kaiwa ga Hamas.
Falasdinawan da ke zaune a Gaza da Gabar Yamma na kokawa da mawuyacin halin da suka ce suna ciki saboda matakin Isra'ila na tsaro a iyakar.
Ita kuwa Isra'ila na cewa tana yin hakan ne domin kare kanta daga abin da ta kira tashin hankalin Falasdinawa.
Yunkurin korar wasu Falasdinawa daga Gabashin BIrnin Kudus ma na tayar da rikici.

Asalin hoton, Getty Images
Wadanne ne manyan matsalolin?
Shi dai wannan rikici ba abu ne da ake ganin za a iya magance shi ba nan da wani dan lokaci.
Shirin wanzar da zaman lafiya na baya-bayan nan da Amurka ta samar a lokacin mulkin Donald Trump wanda tsohon Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yaba da shi bai samu karbuwa ba wajen Falasdinawa, saboda sun bayyana shi da cewa ya fifita bangare daya
Saboda haka duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi nan gaba dole ne ta samu karbuwa wajen bangarorin biyu.
Editan BBC na yankin Gabas ta Tsakiya Jeremy Bowen, ya ce rikicin watan Mayu na 2021 shi ne yaki na hudu mafi girma tsakanin Hamas da Isra'ila tun 2008.
Editan ya ga yaki da dama da ya kare kamar wannan a baya, inda kowa ne bangare ke ikirarin samun nasara.
Amma kuma nan da nan sai a dasa dan-ba na wani sabon rikicin.
Ya ce, ''Ina tabbatar ma da cewa in dai ba a sauya tsarin da ake ciki ba a yanzu, to ba shakka wani yakin zai sake barkewa.''











