Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dapo Abiodun na jam'iyyar APC ya yi tazarce a Ogun
Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar da da aka yi a ranar Asabar.
Babban jami'in zaɓen na jihar, Farfesa Kayode Adebowale ne ya bayyana sakamakon da yammacin Lahadi.
Abiodun ya lashe zaben da ƙuri'u 276,298, inda ya samu nasara a kan abokin hamayyarsa Ladi Adebutu na jam'iyyar PDP wanda ya samu ƙuri'u 262,383, sai kuma Biyi Otegeye na jam'iyyar ADC da yazo na uku.