Bellingham na son janye Arnold daga Liverpool, Arsenal da Man U na son Tickle

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan Bournemouth Antoine Semenyo na jan hankali, Kevin de Bruyne zai iya komawa Saudi Arabia, yayin da Liverpool ke fatan ci gaba da rike Trent Alexander-Arnold.

Real Madrid na kara kaimi wajen zawarcin Alexander-Arnold amma Liverpool na fatan za ta shawo kan dan wasan mai shekaru 26 ya ci gaba da zama. (Football Insider)

Dan wasan bayan na Liverpool Arnold, mai shekara 26, zai iya barin Anfield don komawa Real Madrid a kyauta, yayin da amininsa Jude Bellingham ke ta kokarin gamsar da shi ya yi hakan. (Sun)

Dan wasan gaban Bournemouth Antoine Semenyo, mai shekara 24, yana jan hankalin Liverpool, da Newcastle United da Tottenham bayan dan wasan na Ghana ya fara taka leda a kakar wasa ta bana. (Give Me Sport),

Kulob din Al-Nassr na Saudiyya yana da kwarin gwiwar sayen dan wasan tsakiyar Manchester City na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33, lokacin da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana. (Team Talk)

Liverpool ta bayyana dan wasan gaban Eintracht Frankfurt dan kasar Masar Omar Marmoush, mai shekara 25, da dan wasan Borussia Dortmund na Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 22, a matsayin wadanda za su maye gurbin dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 32.(Give Me Sport)

Fatan Manchester United na sayen dan wasan tsakiya na Colombia Richard Rios na kara karfi, inda Palmeiras ke son siyar da dan wasan mai shekaru 24 a kan Yuro miliyan 20 (£16.7m) a watan Janairu. (Caught Offside),

Arsenal da Manchester United na zulama wajen zawarcin golan Wigan Athletic dan kasar Ingila Sam Tickle mai shekaru 22 a duniya, a kokarin da suke na kara karfafa ragarsu. (Team Talk)

Shugabannin Southampton na shirin ganawa domin tattauna makomar kociyan kungiyar Russell Martin a kungiyar. (Football Insider)

Dan wasan Paris St-Germain na Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 25, zai iya barin kungiyar a watan Janairu amma zakarun Ligue 1 din na son a saye shi a kan akalla Yuro miliyan 70 (£59m). (AS - in Spanish)

Dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, mai shekara 21, yana sha'awar komawa Bayern Munich a bazara mai zuwa. (Sky Germany)

Newcastle United na ci gaba da sa ido kan dan wasan gaban Lille dan kasar Canada Jonathan David, mai shekara 24, don dauakrsa a watan Janairu. (Football Insider)