Wace irin rundunar tsaro Ganduje ke son kafawa a Kano?

Lokacin karatu: Minti 3

Ana ci gaba cece-kuce dangane da sanarwar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi cewa zai kafa rundunar tsaro wadda za ta yi gogayya da hukumar Hisba a jihar ta Kano.

Tuni dai aka kaddamar da tsarin shiga sabuwar kungiyar ta Independent Hisbah fisabillilah, amma masu fafutuka suna ci gaba da nuna cewa tsarin yana da hadari.

Rahotanni sun nuna cewa an riga an fara nema da cike fom na shiga ƙungiyar, tare da taron ƙaddamarwa da ya ja ɗimbin mutane daga kananan hukumomi 44 na jihar, inda suka nuna goyon bayansu ga sabon tsarin da bangaren Ganduje ya fito da shi.

Wannan yunkurin dai yana ci gaba da fuskantar caccaka musamman daga gwamnatin Kano, inda suke bayyana cewa kafa Hisbar mai zaman kanta ya sabawa doka.

Yaya tsarin rundunar zai kasance?

Sunan rundunar Indifenda Hisba Fisabilillah kuma za ta ƙunshi dakaru ne waɗanda za su rinƙa gudanar da ayyukan taimakon al'umma, kamar yadda tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya shaida wa BBC.

"Magana ake yi ta ƴan agaji.Yadda batun yake shi ne mutanen da dama sun so shiga aikin Hisba to amma kasancewar sun yi yawa sai muka ware mutum 5,600 muna ba su alawus a lokacin gwamnatinmu to amma wannan gwamnatin ta ce ta soke su kuma ba za ta yi amfani da su ba."

Tsohon kwamishinan na Ganduje ya ce zuwan da mutanen 5,600 suka yi ga tsohon gwamna ne ya sa aka tunanin taimakon su.

"Shi ne suka zo suka sami tsohon gwamna, Umar Ganduje cewar suna son ci gaba da aikin agaji musamman ga gidauniyarsa ta Ganduje Foundation domin yin aikin Allah kamar a masallatai. Idan za a buɗe masallatai za a gan su."

Dangane kuma da ko tsarin zai zama kishiya ga rundunar Hisba a jihar ta Kano, sai Muhammad Garba ya ce:

"Ba wai so ake a fito da wata ƙungiyar da za ta yi karo da Hisbar da ake da ita a Kano ba. Gaskiya ba haka ba ne. Ina ganin akwai rashin fahimta. Muna tabbatar wa da al'ummar jihar Kano cewa duk wani abun da zai kawo rashin jituwa da tashin hankali a jihar Kano, maigirma Abdullahi Umar Ganduje ba zai yi shi ba"

"Kuma yana jin kiraye-kirayen da ake yi. Idan har ya tabbatar da cewa abin da ake son yi zai haifar da matsala a Kano na tabbatar da cewa shi tsohon gwamna zai tsaya ya sake dubawa..."

Wane ne zai rinƙa biyan rundunar albashi?

BBC ta tuntuɓi wani jami'i wanda da shi ake shawarwarin samar da wannan Hizba inda kuma ya shaida wa kafar cewa " gaskiya ba mu kai ga wannan magana ba tukunna. Muna ma tunanin dakatar da al'amarin a yanzu sakamakon yadda batun ke ci gaba da janyo rashin fahimta."

Martanin gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci a kama tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje bisa zargin yin kalaman da ka iya tayar da hankali game da tsaron jihar.

Gwamnatin ta yi kiran ne yayin zaman majalisar zartarwa na jihar, wanda ya yi nazari kan maganganun Ganduje da na mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, game da yunƙurin kafa rundunar tsaro ta musamman mai suna Khairul Nas.

Kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce irin waɗannan kalamai suna iya raunana kokarin gwamnati wajen tabbatar da tsaro, musamman ganin cewa bayan fitar kalaman an samu harin ƴan bindiga a wasu yankuna.

Gwamnatin Kano ta jaddada cewa ba za ta yarda da kafa kowace rundunar tsaro ta haramtacciyar hanya ba, tare da kira ga shugabannin siyasa su guji kalaman da za su iya haddasa tashin hankali.

Me Shari'a ta ce?

Masana harkar shari'a da masu fafutuka suna ci gaba da nuna cewa tsarin yana da hadari.

"Shi wannan abu idan ka duba a dokance ba shi da tushe. Babu inda doka ta bai wa wani ɗan ƙasa shi kaɗai damar haɗa wata rundunar tsaro da sunan yin aiki irin na hukuma," in ji lauya mai zaman kansa a Kano, Sadiq Sabo Kurawa.

"Na farko idan ka duba sashe na 227 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya fito ƙarara ya yi hani. Sannan sashe na 5 na tsarin mulkin Najeriya na1999 ya bai wa gwamna damar aiwatar da hakan. Sannan idan ka ƙara dubawa sashe na 14 na kundin ya ce gwamnati ce ke da alhakin samar da tsaron al'ummarta."

"Sannan idan ka duba cewa mutanen nan korar su aka yi daga aiki saboda haka idan ka damu da su kamata ya yi ka tafi kotun shari'ar ƙwadago. Amma sai ka ce za ka ɗauke su aiki, a wannan babbar barazana ce."