'Aikinmu kawai kisa' - Yadda ƴan RSF ke kashe mutane a Sudan

- Marubuci, Merlyn Thomas, Matt Murphy & Peter Mwai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- Lokacin karatu: Minti 5
Gargaɗi: Wannan rahoto na ɗauke da bayanan kisan gilla da za su iya tayar muku da hankali.
Wasu mayaƙa na ta shewa yayin da suke tafe a cikin wata motar a-kori-kura, suna zabga gudu yayin da suka tarar da gawar mutum tara.
"Kalli wannan aikin. Kalli kisan ƙare-dangin nan," in ji ɗaya daga cikinsu.
Yana murmushi yayin da ya jiuya kyamarar kan sa da sauran mayaƙa abokan aikinsa sanye da kakin ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF): "Irin wannan mutuwar za su yi dukkansu."
Mutanen na murna ne game da kashe-kashen da suka yi wadda masu fafutikar kai kayan agaji ke fargabar sun kashe aƙalla mutum 2,000 a birnin El-Fasher a watan da ya gabata.
A ranar Litinin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta ce ta fara bincike kan ko RSF ta aikata "laifin yaƙi da cin zarafin ɗan'adam".
Garin El-Fasher na da muhimmanci ga RSF. Shi ne babban gari na ƙarshe da ke hannun dakarun gwamnatin Sudan a yankin Darfur tun bayan fara yaƙi a 2023.
An yi ƙiyasin cewa yaƙin ya kashe mutum 150,000 cikin shekara biyu, kuma ana zargin duka ɓangarorin da aikata laifukan yaƙi.
Birnin da ya rayu shi kaɗai
Bayan yi wa binrin ƙawanya kusan shekara biyu, tun daga watan Agusta RSF ta tsaurara hare-hare kan sauran yankunan da fararen hula suke.
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda dakarun ƙungiyar suka gina shingaye tare da toshe hanyoyin shiga da kayan agaji a garin. Zuwa watan Oktoba sun gama yi wa garin zobe.

Yayin da ƙawanyar ta tsananta, an kashe mutum 78 a harin RSF da ta kai kan wani masallaci ranar 19 ga watan Satumba, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an kashe ƙarin 53 a harin jirgi maras matuƙi kan wani sansanin 'yan gudun hijira a watan Oktoba.
Bidiyon da aka tura wa BBC Verify sun nuna cewa RSF ta so ta hana shigar da abinci da sauran kayayyaki. Wani bidiyo da aka ɗauka a watan Oktoba ya nuna wani mutum hannayensa a ɗaure ta baya kuma yana reto a jikin bishiya bayan ɗaure shi da ankwa. Mutumin da ke ɗaukar bidiyon na zargin sa da yunƙurin shigar da kayayyaki a asirce cikin garin da suka yi wa ƙawanya.
"Na ranste da Allah sai ka gane kurenka kare kawai," kamar yadda ya dinga faɗa wa ɗaurarren.
Harbe fararen hula
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Zuwa ranar 26 ga watan Oktoba RSF ta gama cin ƙarfin sojojin Sudan kuma suka ƙwace babban sansanin da birnin, wanda shi ne ofishin bataliyar 6th Infantry Division.
An ga sojoji na shewa yayin da suka shiga sansanin. Daga baya kuma sai aka ga kwamandan RSF Abdul Rahim Dagalo yana zagaya sansanin.
Kafin RSF ta ƙwace El-Fasher, ba a fiya samun wasu bayanai daga birnin ba tsawon watanni. Amma 'yan awanni baya ficewar sojojin sai bidiyon ɓarnar da RSF suka yi suka fara fitowa.
Ɗaya daga cikin bidiyon da BBC Verify ya nazarta ya nuna yadda aka karkashe mutane a ginin wata jami'a, inda gawarwaki suka fantsama ko'ina a jami'ar da ke yammacin birnin.
Wani dattijo na zaune shi kaɗai a tsakiyar gawawwakin, yana kallon wani ɗanbindiga da ke riƙe da kyamara kuma yana tunkaro shi. Nan take ɗanbindigan ya harbe shi. sauran 'yanbindigar da ke tare da shi sun hangi ƙafar wani ta yi motsi a cikin gawarwakin.
"Ya aka yi wannan bai mutu ba," in ji ɗaya daga cikinsu. "Harbe shi."
Wasu hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar 26 ga watan Oktoba sun nuna alamun an yi kisan gilla a kan titunan El-Fasher, kamar yadda rahoton cibiyar Yale Humanitarian Research Lab ya nuna.
Masu nazari a cibiyar sun fito da wasu "tudu tudu" da aka gani a hotunan waɗanda suka ce sun yi "daidai da girman jikkunan ɗan'adam waɗanda babu su a hotunan bab". Sun kuma fito da sauyi a launin ƙasar wurin, wanda suka ce akwai yiwuwar jinin ɗan'adam ne ya haifar da sauyin.
Wani mutum ya faɗa wa BBC cewa "an kashe 'yan'uwansa da yawa a kan idonsa - an tara su a wuri guda kuma aka harbe su".
Wani shaidain kuma ya ce ya ga yadda RSF suka "harbe wata mace a ƙirji bayan sun kwashe dukkan kayayyakinta".

Yayin da mayaƙan RSF suka kutsa cikin garin, wasu mayaƙan daban sun ja tunga a wajen gari inda suka dinga kashe mutanen da ba su ɗauke da makamai.
An yi hakan ne akasari a wani wuri mai nisan kilomita takwas daga El-Fasher. Hotuna sun nuna gawawwaki masu yawa sanye da kayan fararen hula - wasu ma mata ne - kwance a cikin wani kwazazzabo na shingen da RSF ta kakkafa.
Wani babban mai aika-aika da BBC Verify ta gano shi ne kwamandan RSF mai suna Abu Lulu a intanet. An gan shi yana kashe mutanen da suka yi garkuwa da su cikin wani bidiyo, shi kuma wani shaida ya faɗa wa BBC cewa "kwamandan ya bayar da umarnin kashe wasu mutane da ba su yi wa kowa laifi ba, ciki har da yara".
Wani bidiyo ya nuna sojan RSF na yunƙurin ceton wani mutum lokacin Abu Lulu ke shirin kashe wani mutum da ya ji rauni kuma yake roƙon afuwa: "Na san ka. Na kira ka 'yan kwanakin da suka wuce."
Abu Lulu ya yi watsi da magiyar da mutumin ke yi yana cewa: "Ba zan taɓa yi maka afuwa ba. Aikinmu shi ne kawai kisa." Nan take danbindigan ya sakar wa mutumin ruwan harsasai.

Wani bidiyon daban ya nuna shi yana kashe wani rukunin mutum tara da aka yi garkuwa da su. Daga baya wani bidiyon ya bulla wanda ya nuna an bar mutanen idan aka kashe su, a jere kan layi cikin yashin sahara irin na yankin Darfur.
Da yawan waɗanda suka aikata kisan na sanye ne kakin RSF, cikinsu har da rukunin da suka yi murnar abin a matsayin "kisas ƙare-dangi".

Ihu bayan hari
'Yan kwanaki bayan kashe-kashen, shugaban RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya amince cewa dakarunsa sun aikata ba daidai ba kuma ya ce za su bincika.
Wani babban jami'in MDD ya ce RSF ta bayyana cewa sun kama wasu mayaƙansu kan aikata laifuka.
Cikin waɗanda aka tsare har da Abu Lulu bayan BBC Verify ya wallafa rahoton aika-aikar da ya yi. Wani bidiyo da RSf ta wallafa a shafinta na Telegram ya nuna ana saka shi cikin wani gidan yari a wajen garin El-Fasher.

A gefe guda kuma, RSF da ƙawayenta sun fara wallafa bidiyon mayaƙansu na raba wa fararen hula kayan tallafi, da kuma nuna kamar suna mutunta fursunonin soja da suka kama.

Duk da ƙoƙarin wanke kan su a shafukan sada zumunta, kashe-kashen da suka aikata a El-Fasher sun girgiza duniya.
BBC Veryfiy ya nemi ji daga bakin RSF ɗin game da zarge-zargen da aka yi musu a wannan rahoton. Amma ba su ce komai ba.







