Me ya kawo ƙarancin takardun kuɗi a Najeriya?

Tsoffin takardun kuɗi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Mazauna birane da ƙauyukan Najeriya, a 'yan makonnin nan suna kokawa kan ƙarancin takardun kuɗi a na'urorin cirar kuɗi na ATM da wuraraen masu sana'ar aikawa da cire kuɗi ta POS, wani abu da ke ƙara haifar da fargaba a zukatan al'umma.

Masu sana'ar ta POS na kokawa kan yadda suka ce ba su samun kuɗaɗe da yawa a bankunan idan suka je cira, saɓanin yadda suka saba samu a baya.

Wannan ne ma dalilin da ya sa wasu masu sana'ar a Abuja suka haƙura da ita ko suka rufe saboda rashin garin kuɗin.

Sannan ga waɗanda ake samun kuɗin a wajensu, ba a samu da yawa, sannan kuma sun ƙara yawan kuɗin da suke cazar mutane.

A wasu sassan Abuja, masu sana'ar na karɓar naira 400 kan kowace naira 10,000, saboda yadda suka ce suna shan wahala wajen samo kuɗaɗen.

Wata mai sana'ar POS a Abuja mai suna Esther Nwanna, ta shaida wa BBC cewa yanzu kullum sai ta je bankuna aƙalla biyar da take hulɗa da su kafin ta iya samun 100,000 da za ta fito wajen sana'ar tata da safe.

''Da safen nan sai da na je bankuna biyar, kuma dukkansu ba a kusa da juna suke ba, amma wallahi da kyar na samo naira N100,000 da zan fito in fara da ita'', a cewarta.

Shi ma Abubakar Jibril mai irin wannan sana'a, ya ce sai da ya je bankuna huɗu kafin ya samo N70,000.

''Bankunan da na je ba a kusa da juna suke ba, dole sai na hau abin hawa zuwa kowanne, sannan na dawo wurin sana'ar tawa. Ka ga ai dole na ƙara kuɗi ni ma in dai ina so in ci gaba da sana'ar," a cewarsa.

''A baya banki guda nake zuwa kuma ko nawa nake so za su ba ni domin gudanar da harkokina, amma yanzu abubuwa sun sauya, bankin ma babu kuɗaɗen balle su ba mu."

Me ya janyo matsalar?

Sabbin takardun kuɗi

Asalin hoton, CBN

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani ma'aikacin banki da BBC ta tattauna da shi wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce abin da ke faruwa shi ne ana tattara tsofaffin takardun kuɗi ne a wani ɓangare na shirye-shiryen daina amfani da su.

''Idan ba ka manta ba, a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari an sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, kuma aka saka wa'adin daina amfani da su, amma saboda ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar aka ɗaga zuwa wani lokaci na gaba'', in ji shi.

A shekakar 2022 ne Muhammadu Buhari ya ba da umarnin sauya fasalin takardun kuɗi na N1,000 da N500 da kuma N200, tare da saka wa'adin daina amfani da tsoffin zuwa ƙarshen shekarar 2022.

Sai dai bayan wasu gwamnonin ƙasar sun garzaya kotun ƙolin ƙasar don ƙalaubalantar taƙaitaccen lokacin da aka bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin, kotun ta bayar da umarnin cigaba da amfani da su har zuwa shekara guda, inda daga baya ta yi hukuncin cewa a ci gaba da amfani da su ba tare da iyakance lokaci ba.

Takardun kuɗi

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai ma'aikacin bankin da BBC ta tattauna da shi ya ce bisa tsarin doka ba zai yiwu a ci gaba da amfani mabambantan takardun kuɗi ba.

Amma ya ce za a yi hakan ne cikin hikima ba tare da sanya razani ko fargaba a zukatan 'yan ƙasa ba.

''Ana ƙoƙarin kawo ƙarshen amfani da tsoffin takardun, amma kuma cikin hikima, ba a so su haifar da fargaba a zukatan 'yan ƙasa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa a maimakon gwamnati ta saka sabon wa'adi na daina amfani da tsoffin takardun kuɗi, sai ta riƙa bi da shi cikin hikima ba tare da haifar da fargaba ba.

"Abin da ake yi shi ne idan waɗannan tsofaffin kuɗin suka shiga banki, to ba za a sake bari su fito ba''.

''Inda za ka lura mafi yawanci sababbin kuɗi ne suke yawo, ana ƙoƙarin maye gurbin tsofaffin takardun kuɗin ne.'' in ji ma'aikacin bankin.

Sabbin takardun kuɗi

Asalin hoton, Presidency

Rage kuɗin da ke yawo a hannun mutane

Ma'aikacin bankin ya kuma ce wani ƙarin dalilin shi ne rage yawan kuɗin da ke yawo a hannun mutane, wanda ke ɗaya daga cikin tsare-tsaren gwamnati kan tattalin arziki.

A cewarsa: ''Ya kamata a ce kuɗaɗen nan a banki suke, don haka wannan ma na daga cikin dalilan ƙarancin kuɗin da ake gani yanzu.''

Don haka ne ya ce idan an shigar da tsoffin takardun kuɗi banki, ba lallai ne ma a buga adadin kuɗin da ya kai su yawa ba.

''Misali idan an shigar da naira biliyan ɗaya banki na tsoffin takardun kuɗi, to ba za a ce dole sai an buga naira biliyan ɗaya na sabbin kuɗi ba, a maimakon haka za a rage adadin da za a buga domin su zagaya a hannun mutane,'' a cewarsa.

Ya ƙara da cewa wannan su ne manyan abubuwan da suka janyo ƙarancin garin kuɗi a tsakanin al'umma.

Me ya sa masu POS ba su samun kuɗi da yawa a banki?

Mai sana'ar POS

Ma'aikacin bankin ya ce a tsarin doka akwai adadin kuɗin da mutum zai iya cire wa a kowace rana idan ya shiga banki.

''To kuma bisa wannan tsari na rage yawan kuɗin da ke yawo a hannun jama'a, dole su ma a rage adadin kuɗin da ake ba su''.

''Shi kansa bankin babu isassun kuɗin a cikinsa ballantana ya bai wa kwastomominsa'', kamar yadda ya bayyana.

Ma'aikacin bankin ya kuma ce su dama masu sana'ar POS ai ba cire kuɗi ne kawai sana'arsu ba.

''Suna tura kuɗi, sannan kana iya zuwa ka sayi katin waya ko na lantarki ko biyan kuɗin talbijin ko hulɗar cinikayya tsakanin mai saye da mai sayarwa da sauran abubuwa''.

Don haka ne ma ya hore su, da su faɗaɗa sana'arsu ta yadda za ta dace da sabon tsarin tattalin arziki da ƙasar ke son ɓullowa da shi, na rage yawan kuɗin da ke zagayawa a hannun jama'a.