Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe za a sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru?
Yayin da ake ci gaba da dakon Majalisar tsarin mulkin jamhuriyar Kamaru ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 12 ga watan Oktoban 2025, ana ci gaba da samun tankiya tsakanin ɗantakarar jam'iyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary da Paul Biya na jam'iyya mai mulki dangane da haƙiƙanin wanda ya samu ƙuri'u masu yawa a zaɓen.
Ko da a ranar Lahadin da ta gabata sai da Issa Tchiroma Bakary, ya fitar da sakamakon zaɓe daga wasu yankuna na ƙasar domin kare iƙirarin da yake yi na cewa ya lashe zaɓen.
Sai dai jam'iyya mai mulki ta CPDM ƙarƙashin shugaba Paul Biya ta yi watsi da iƙirarin, tana mai cewa ba gaskiya ba ne cewa kaso 80 na masu zaɓe suna cikin waɗannan yankuna 18.
Duka waɗannan na faruwa ne a daidai lokacin da ƴan jamhuriyar ta Kamaru ke jiran sakamakon zaɓen da Majalisar Tsarin Mulki za ta sanar.
Tambayar da jama'a musamman ƴan ƙasashen waje ita ce yaushe ne za a ayyana sakakamon zaɓen da aka gudanar kwanaki takwas da suka gabata?
Yadda ake sanar da sakamakon zaɓen Kamaru
Saɓanin sauran ƙasashen Afirka da hukumomin zaɓen kasashe ke sanar da sakamako, jamhuriyar Kamaru na da nata tsarin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, inda Majalisar Tsarin Mulki ta ƙasar ke ayyana mutumin da yi nasara.
Majalisar tsarin mulki wadda ke da alhakin sanar da sakamakon zaɓen tana da kwanaki 15 daga ranar zaɓe kafin ta sanar da sakamakon na ƙarshe.
A ranar 12 ga watan Oktoba ne dai aka gudanar da zaɓen kuma abin da hakan yake nufi shi ne dole ne a sanar da zaɓen kafin ranar 27 ga watan na Okotoban wato kwanaki 15 bayan kaɗa ƙuri'a.
Bisa tsarin mulkin ƙasar, Majalisar da ke da alhakin sanar da sakamakon zaɓen dai
Tun dai ranar 16 ga watan na Okotoba ne Hukumar zaɓen jamhuriyar ta Kamaru, Elecam ta kafa wani kwamitin ƙasa wanda zai yi ƙidayar ƙarshe ta ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen.
Shugaban hukumar, Dakta Enow Egbe wadda ta sanar da kafa kwamitin ta ce kwamitin zai yi duba da tabbatar da inganci da yawan ƙuri'un da aka kaɗa a shiyyoin ƙasar gabanin sanar da sakamakon a hukumance.
Kuma wannan ne mataki na ƙarshe kafin ayyana mutumin da ya lashe zaɓen jamhuriyar, kafin daga bisani hukumar zaɓen ta tattara dukkan sakamakon ta kuma miƙa shi ga Majalisar tsarin mulkin jamhuriyar domin sanarwa ga ƴan ƙasa.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne kuma hukumar ta fara sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen na shugaban ƙasa da manufar warware su gabanin miƙa sakamakon ƙarshe ga Majalisr Tsarin mulkin ƙasa domin ayyana mutumin da ya lashe zaɓen.
Sakamakon zaɓen shiyyoyin Kamaru a taswira
Ku taɓa kan yanki ko shiyyar da kuke son sanin samakonsa a wannan taswira. BBC tana sabunta sakamakon zaɓen na shiyya-shiyya da zarar hukumar zaɓe ta sake shi.
Sai dai kuma Majalisar tsarin mulkin jamhuriyar Kamaru ce kawai ke da damar sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen.
Kwamitin ƙidayar ƙuri'un dai ya ƙunshi alƙalan majistare da wakilan gudanarwa da wakilan hukumar zaɓe da kuma wakilan ƴantakarar 12 da suka fafata a zaɓen ranar 12 ga watan na Okotoban 2025.
Yayin da ake ƴan jmahuriyar ta Kamaru na ci gaba da zumuɗin jiran sanin mutumin da ya lashe zaɓen, su kuwa manyan ƴan takarar guda biyu, Tchiroma Bakary da Paul Biya na ta tankiya dangane da sakamakon.
Iƙrarin Tchiroma Bakary
Dan takarar jam'iyyar adawar ta jamhuriyar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya fitar da sakamakon zaɓe daga wasu yankuna na ƙasar inda yake nuna cewa shi ne mutumin da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba.
Tchiroma, mai shekaru 76, ya wallafa takardun sakamakon a shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, inda ya yi iƙirarin cewa ya yi nasara a manyan yankuna 18 daga cikin yankuna 58 na ƙasar, waɗanda a cewarsa suna wakiltar kusan kashi 80 cikin 100 na masu zaɓe.
Ya ce, "da nasarar da muka samu a waɗannan yankuna 18, tabbas mun yi nasara a ƙasa baki ɗaya, domin nauyin zaɓe na yankunan nan shi ke ƙayyade sakamakon ƙarshe."
Tchiroma ya kuma kira al'ummar Kamaru da su "kare nasarar su", yana mai tabbatar musu da cewa zai ci gaba da tsaya musu.
Da ma dai jagoran masu hamayyar ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen tun washegarin kaɗa ƙuri'a.
"Ina son bayyanawa cikin girmamawa da nutsuwa cewa al'ummar Kamaru sun yi zaɓinsu, don haka ya kamata a martaba zaɓinsu......Haƙiƙa wannan nasara ba tawa kaɗai ba ce ni kaɗai, ta kowa ce,'' i in ji Bakary, a wani bidiyo da ya yi da harshen Ingilishi.
A makon da ya gabata ne wasu masu zanga-zanga suka fito kan tituna suna nuna ɓacin rai kan abin da suka kira maguɗin zaɓe, inda suka ƙone gine-gine da lalata hotunan yaƙin neman zaɓen shugaba Biya.
Martanin jam'iyyar adawa
Jam'iyya mai mulki ta a jamhuriyar Kamaru wato CPDM ƙarƙashin shugaba Paul Biya wanda ya yi takara tare da Issa Tchiroma Bakary da sauran mutum bakwai, ta yi watsi da iƙirarin Bakary cewa ya yi nasara a manyan yankuna 18 daga cikin yankuna 58 na ƙasar, waɗanda a cewarsa suna wakiltar kusan kashi 80 cikin 100 na masu zaɓe.
CPDM ta ce iƙrarin ba gaskiya ba ne inda ta ce kaso 80 na masu zaɓe na cikin waɗannan 18.
"Ya kamata a bi ta yadda doka ta tanada kafin a bayyana sakamakon ƙarshe," in ji jam'iyyar CPDM.
Fiye da mutum miliyan takwas ne masu kaɗa ƙuri'a a jamhuriyar Kamaru ne suka kaɗa ƙuri'a ga ƴantakara 11 da suka fafata domin ƙalubalantar shugaba mai ci, Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 43 yana mulki.
Zaɓen ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin hauhawar farashi da rashin aikin yi tsakanin matasa da matsalolin tsaro da rashawa da cin hanci.