Abubuwan da al'ummomin duniya ke yi a lokacin cikar wata

    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Cikar wata da za a gani a ranar Litinin, shi ne na farko a shekarar 2025.

Wannan ne zai kasance rana ta farko a bikin addinin Hindu na Kumbh Mela a India - wani bikin addini da ake shafe kwana 45 ana yi a birnin Prayagaj, inda ake sa ran mutum miliyan 400 za su halarta.

Cikar wata na faruwa ne bayan duk kwanaki 29, lokacin da rana ke haska ɗaukacin ɓarin wata daga ɗaya ɓangaren na duniya, lamarin da ke sa mu ga cikakken wata na ƙyalƙyali.

Irin waɗannan kwanaki na taka muhimmiyar rawa a al'adun al'ummomi a faɗin duniya.

Mun duba wasu abubuwa da al'umma ke yi a faɗin duniya a irin wannan lokaci.

Waɗanne al'adu ake yi idan wata ya raba?

Ana son Musulmai su Azumci ranaku uku na tsakiyar wata. Ranakun da ake kira da Al-Ayyam al-Bid. Annabi Muhammad {SAW} ya azumci ranakun domin yin godiya ga Allah.

Addinin Kiristanci, ana bikin Esther a Lahadin farko bayan cikar wata.

A Mexico da sauran wasu ƙasashen Latin Amurka, ana yin bikin al'adun Amurkawa inda mata ke fitowa tsakiyar wata domin yin rawa da bauta na tsawon kwana uku.

Ta yaya wata a lokacin cikarsa ke shafar rayuwar mutane?

Wasu sun yi imanin cewa a lokacin da wata ya kai tsakiya bacci ba ya yin daɗi.

Bincike da aka gudanar ya nuna cewa a lokacin da wata ya raba, mutane ne na ɗaukan lokaci mai tsawo fiye da yadda suka saba kafin su yi bacci.

Haka nan ya nuna cewa mutane ba su cika samun bacci mai nauyi ba, kuma ba su yin bacci da tsawo kamar yadda suka saba saboda ƙarancin sinadarin 'melatonin' a cikin jiki.

Waɗanda suka gudanar da binciken sun bayyana cewa ba su samun bacci gamsasshe koda sun kwanta a ɗaki mai natuswa sosai.

Haka nan wani binciken da aka gudanar a Birtaniya, cikin shekara ta 2000, ya nuna cewa dabbobi sun fi kai wa mutane farmaki a lokacin da aka samu cikakken wata.

Nazarin ya nuna cewa tsakanin shekarun 1997 zuwa 1999, yawan mutanen da ke zuwa asibiti sanadiyyar cizon dabbobi ya fi yawa a lokutan tsakiyar wata.

Sauran al'adun da addinai ke yi a tsakiyar wata

A China ana bikin Zhongqui Jie, wanda ake kira da bikin 'al'adun wata', wanda ake yi a ranar Girbi, kuma ranar hutu ce. An kwashe shekaru 3,000 ana yin bikin wanda ake yi domin samun amfanin gona mai yawa.

Haka kuma ana yin bikin al'ada na Chuseok wanda ake kwashe kwana uku ana yi, inda iyalai kan taru domin yin bikin murnar Girbi da kuma tunawa da magabatansu.

A addinin Hindu, ranakun fitowar cikakken wata, suna kiran su da Purnima, inda ake azumi da addu'o'i a watan Nuwamba, wata mafi tsarki a cikin jerin watannin Hindu, saboda a watan ne abin bauta Shiva ta samu nasara kan abin bauta Tripurasura. Kuma a watan ne aka fara samar da zanen abin bauta Vishnu.

Sauran al'adun da ake yi akwai wanka a kogi da kuma kunna wuta.

Kumbh Mela wanda aka fara a lokacin cikar wata na faruwa sau guda a cikin shekaru 12.

Masu bin addinin Buddha sun yi amannar cewa an haifi Buddha ne a lokaci cikar wata, shekaru 2,500 da suka gabata. Sun kuma yi imanin cewa ya mutu ne a lokacin cikar wata. Wadannan bukukuwan ana kiran su da Buddha Purnima, wadanda ake yi ranar cikar wata a watan Afrilu ko Mayu.

A Sri Lanka, ana hutu ne a duk ranar cikar wata, kuma ana kiran ranakun da Poya, wadanda aka haramta sayar da barasa da kuma nama.

A Bali, ana kiran ranakun da Purnama, a matsayin ranakun da aka yi amannar ababen bauta maza da mata suka sauko ƙasa domin sanya albarka ga mabiya. Lokaci ne da ake addu'o'i da sadaka da kuma shuka ƴaƴan itatuwa a lambuna.

Tatsuniyoyi da tarihihi game da cikar wata

A Turai, tun zamanin baya, ana tunanin cikar wata zai haifar da hauka ga wasu mutane. Kalmar 'Lunacy', wato rashin hankali ta samo asali ne daga 'Luna', kalmar da ke nufin wata a harshen Latin.

Shaci-faɗin cewa wata a lokacin cikarsa na haifar wa mutane ɗabi'un da ba za su iya sauyawa ba, shi ne ya haifar da imanin cewa wasu mutane na rikiɗewa zuwa dabbobi dangin kyarkeci - waɗanda ke addabar al'umma ba tare da son ransu ba.

A cikin ƙarni na huɗu kafin zuwa annabi Isa, wani masanin tarihi na Girka ya yi rubutu game da wata ƙabila da ake kira Neuri, wadda ya yi iƙirarin cewa mutanenta na rikiɗewa zuwa kyarkeci tsawon wasu kwanaki a kowace shekara.

Haka nan a tsakanin ƙarni na 15 zuwa na 17 an gurfanar da mutane da dama a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin rikiɗa zuwa kyarkeci.