Hotuna 12 da suka fi jan hankali a 2025

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

A nan za mu kawo muku hotuna 12 da suka fi ɗaukar hankali a wannan shekarar ta 2025.

1. Mutane suna bauta - Thailand

Hoton wasu suna addu'o'i a ƙarƙashin babbar hasumiyar zinare na Wat Phra Damakaya a lokacin bikin Makka Pocha na shekara-shekara a watan Fabrairun da ya gabata. Abu ne mai ban sha'awa. Dubban sufaye da almajirai, da yawa ɗauke da fitilu, sun taru don tunawa da babban koyarwar Buddha na farko. Wannan abin kallo mai ban sha'awa ya na nuni ne da rubutun Burma na ƙarni na 19 wanda ke nuna wa'azin farko na Buddha a cikin lambun barewa, waɗanda sufaye da dabbobi ke kewaye da shi a cikin wani yanayi mai ban sha'awa.

...

Asalin hoton, Guillaume Payen/Anadolu via Getty Images

2. Jerin gwano cikin ruwa - Venice

Hoton yana nuna wani jibgegen ɓera da aka yi da takarda mai launuka daban-daban yayin da yake tafiya ta cikin Grand Canal a lokacin tattakin jerin gwanon ruwan da ya buɗe bikin Venice a watan Fabrairun da ya gabata, wani abin kallo mai ƙayatarwa. Wannan ɓera da ya rikiɗe ya zama tauraron abin kallo, da alama ya fito ne daga magudanar ruwa na birnin, wanda ya ƙunshi bangarensa na ban dariya da ke ɓoye. Launin ɓeran ya bambanta da sauran launukan da suka kewaye shi, kamar wani mayafi mai haske wanda ya lullube Venice a cikin zane-zane marasa adadi, irin su zanen Paul Signac da ya yi a shekrar 1905 mai suna "The Entrance to the Grand Canal."

Venice Film Festival

Asalin hoton, Stefano Mazzola/Getty Images

3. Ƙabarin Fafaroma Francis – Rome

Wani hoton da aka ɗauka a watan Afrilu ya nuna ƙabarin Fafaroma Francis da ke birnin Rome - karo na farko da aka binne wani Fafaroma a wajen fadar Vatican a cikin sama da ƙarni guda - kuma farar fure guda ɗaya aka ajiye akan kabarin, abin kallo mai matuƙar taɓa zuciya. Hoton mai ban sha'awa yana haifar da zurfin tunani, mai tunawa jama'a da aikin J.M.W Turner na 1798 na kabarin Cardinal Morton a Canterbury Cathedral. Duka hotunan suna nuna yadda mutuwa ba ta da tabbas.

Tomb of Pope Francis II

Asalin hoton, Bernat Armangue/AP

Bayanan hoto, Kabarin Fafaroma Francis II

4. Ma'aikaci ɗan ci-rani - Chandigarh, Indiya

Hoton, da aka ɗauka a watan Afrilu, na wani ma'aikaci ɗan ci-rani da ya tsaya da aikinsa don ya sha ruwa a lokacin girbin alkama a wajen garin Chandigarh. Ya ɗaga kofi sama ga kuma lauje mai ƙyalli a hannunsa. Wannan hoto ya na tunawa mutane da da yanayin girbi guda ɗaya a cikin zanen Winslow Homer na 1865 "The Veteran in a New Field." A cikin wannan zanen, wani tsohon sojan Tarayyar Turai ya na amfani da lauje a cikin gonar alkama, lamarin da ke nuni da wani lokaci na rikicin ƙasa bayan yaƙin basasar Amurka.

Manomi yana shan ruwa.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Manomi yana shan ruwa a lokacin girbin alkama.

5. Hannun mutum-mutumi - Beijing

Hoton da aka ɗauka a yayin wani rangadi da manema labarai suka yi a "World of Robots" da aka yi a birnin Beijing a watan Afrilu, ya nuna wata budurwa ta kai hannu don taɓa wani katon yatsa na mutum-mutumi da ke bayyana a hankali. Yadda aka haskaka ɗakin da baƙaƙen tufafin yarinyar sun haɗu don rage nuna kamanninta na ɗan adam: A kallo na farko, wannan kusancin na iya tunawa mai kallo da "The Creation of Adam" na Michelangelo, ko watakila mafi daidai, aikin MC. Escher mai suna "Hands Drawing Hands" (1948).

...

Asalin hoton, Pedro Pardo/AFP/Getty Images

6. Cibiyar tafiya ta wucin gadi - Buganda

Hoton da aka ɗauka a watan Mayu, ya nuna wata yarinya ƴar gudun hijirar Kongo zaune a kan lilo a wata cibiyar sufuri da ke kusa da Buganda, farin cikinta ya zarce wahalhalun da take fuskanta: ruwan sama, lalatattun kayayyakin aikin da aka yi watsi da su, da kuma kujerar da ta karye a gefenta. Ko da yake ta na ɗaya ne daga cikin mutane sama da 70,000 da suka tsallaka zuwa Burundi tun daga watan Janairu, tana da matuƙar ƙwarin gwiwa duk da yanayin da take ciki. Ana iya kwatanta wannan hoton da shahararren zanen Jean-Honoré Fragonard na 1767 mai suna "The Swing,"

...

Asalin hoton, Getty Images

7. Tarwatsewar taurari – Inverness, California

Hoton da aka ɗauka a ranar 6 ga watan Mayu yana nuna yadda taurari ke tarwatsewa a sararin samaniya a yankin Inverness, na California, inda ya ke haifar da wani lamri mai matuƙar ban sha'wa. Ana iya kwatanta wannan lamari da aikin Adam Elsheimer mai suna "The Flight into Egypt," wanda aka zana a shekarar 1609.

Taurari.

Asalin hoton, Tayfun Coskun/Anadolu/Getty Images

8. Idanun da aka rufe da mai - Landan

A watan Mayun da ya gabata, wata mai fafutukar yaƙi da gurɓata yanayi daga ƙungiyar ''Fossil Free London'' ta tsaya da idanunta a rufe a wajen ofishin kamfanin Shell a wata zanga-zangar da ta yi. Wannan matakin dai ya kasance martani ne ga yadda kamfanin Shell ya sayar da kadarorinsa na man da ke gaɓar teku a Najeriya, wanda masu zanga-zangar ke ganin wani yunƙuri ne na kaucewa alhaki da bala'o'i a yankin Neja Delta. Shell ya musanta aikata laifin. Hoton da ke da idanun da aka lullube na kamanceceniya da aikin George Frederick Watts mai suna "Hope," wanda aka zana a shekara ta 1886, wanda ke nuna wata mata da idonta a rufe ta na zaune a saman wani wuri mai ban mamaki, tana wasa da garaya.

...

Asalin hoton, Luis Tato/AFP/Getty Image

9. Mai ninƙaya – Singapore

Hotunan wani mai ninƙaya na ƙasar China Tianchen Lan a lokacin da ake gudanar da wasannin motsa jiki na ruwa a gasar wasan ruwa ta duniya da aka yi a ƙasar Singapore ranar 20 ga watan Yuli, ya dauki wani yanayi mai ban sha'awa na nutsewa a tsakiyar wani dandali mai launin shudi. Ana iya kwatanta wannan lamari da aikin Yves Klein na shekarar 1960 mai suna ya haifar da inuwa mai tsananin gaske "International Klein Blue" da shigarwar sa na 1960 "Leap into the Void," wanda ke da nuna kamar wani na faɗowa daga wani bene da ke birnin Paris.

...

Asalin hoton, Maddie Meyer/Getty Images

10. Ɗaliban rawar Ballet – Thembisa, Afirka ta Kudu

Hoton da aka ɗauka a watan Yulin da ya gabata na wasu ƴan mata biyu ƴan shekara biyar, Philasande Ngkobo da Yamehle Gwapapa, da suka fito a gaban wata makarantar koyar da raye-raye da ke Tembisa, a ƙasar Afirka ta Kudu, abin burgewa ne kuma mai sanya tunani.

...

Asalin hoton, Phill Magakoe/AFP/Getty Images

11. Yaron da ke fama da matsananciyar rama saboda yunwa - Gaza

Wasu jerin Hotunan da suka ratsa jiki, na yara ƙanana da suka tagayyara saboda yunwa da iyayensu ke kwance da su a birnin Gaza a watan Yulin da ya gabata ya girgiza duniya. A cewar ƙwararru da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka ana fuskantar mummunan yanayi na yunwa a Gaza. Hotunan da aka ɗauka a Gaza ba su kamanceceniya da wani a zane ko sassaka da aka taɓa yi saboda tsananin munin halin da ake cikin.

Yaro a Gaza

Asalin hoton, Getty Images

12. Yi wa tunkiya aski- Patras, Girka

A yayin da hayaki mai kauri ke fitowa daga gobarar dajin da ta addabi birnin Patras na ƙasar Girka a watan Agustan da ya gabata, an ga wani mutum a kan babur yana ceto wata tunkiya, wadda ta maƙale masa da dukkan ƙarfinta. Wannan yanayi yana kamanceceniya da hotuna na Makiyayi mai suna ''Good Shephard'' da ake gani a ginin Romawa na ƙarni na biyu da na uku, inda Almasihu ya ɗauki dabba mai rauni a kafaɗunsa.

Tinkiya

Asalin hoton, Thanassis Stavrakis/AP