Ana zargin Ɗan China da kashe budurwarsa Ƴar Kano

.

Asalin hoton, Abdullahi Kiyawa

Ƴan sanda a Najeriya sun kama wani mutum ɗan ƙasar China bisa zarginsa da kashe wata budurwarsa a Jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa BBC cewa suna tsare da mutumin inda suke ci gaba da yi masa tambayoyi.

Ana zargin Ɗan Chinan da zuwa har gidan su budurwar tasa mai suna Ummukulthum Sani ranar Juma'a da dare inda ya yi amfani da wuƙa ya yanke maƙogoron marigayiyar.

An kama mutumin da ake zargin bayan mazauna gidan sun ankarar da sauran jama'a abin da ke faruwa.

Kanwar mahaifiyar Ummukulthum ta shaida wa BBC cewa suna zaune sai suka ji ana ƙwanƙwasa ƙofa, sai marigayiyar ta ce kada a buɗe ta san ko wane ne.

Ta bayyana cewa bayan shafe kusan sa'a ɗaya yana ƙwanƙwasa ƙofa sai mahaifiyar marigayiyar ta tambaya wa ke ƙwanƙwasa ƙofa sai aka gaya mata ko wanene, ko da ta buɗe ƙofar sai ya ture ta ya shiga gidan.

Ta bayyana cewa daga nan ne ya bi ta har cikin ɗaki ya caccaka mata wuƙa.

Wannan lamari dai ya ja hankalin jama'a da dama a shafukan sada zumunta a Najeriya sakamakon ba kasafai aka cika samun irin waɗannan lamura.