Abin da ya hana sulhu tsakanin Ecowas da Nijar - Tuggar

Watanni huɗu bayan kakaba wa jamhuriyar Nijar takunkumi da ƙungiyar Ecowas ta yi, sakamakon juyin mulkin sojoji, har yanzu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗanɗana kuɗa da rayuwar ƙunci.

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi, saboda rufe iyakar ƙasar da Najeriya ta yi, da kuma yanke hulɗar kasuwanci da ƙasashen Ecowas suka yi da Nijar.

A hirarsa da BBC, ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo ƙarshen halin da ake ciki, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojoji da ke mulki a Nijar, sun ƙi amincewa da yunƙurin.

"Duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sun ce ba su amince ba. Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuɗɗan yin sulhu," in ji Yusuf Tuggar.

Ya ce babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi.

"Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?"

Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da Ecowas ta ƙaƙaba mata, da kuma shiga halin da take ciki.

Ya ce abin da suke buƙata shi ne a saki Shugaba Bazoum.

"Muna son sojojin su saki Bazoum ya fita, a kai shi wata ƙasa daban. Ba maganar dawo da shi kan mulki ake yi ba," in ji ministan.

Ya ƙara da cewa, duk wani yunƙuri da suka yi, sojojin sun ƙi ba da haɗin-kai ta kowanne yanayi, inda suka ce ba sa son a yi maganar ma kwata-kwata.

"Ta yaya za a yi sulhu a haka, mene ne sojojin za su yi saboda in ana son yin sulhu tsakanin mutane, gefe ɗaya zai ce ya haƙura da abu kaza, ɗaya gefen ma ya ce haka. To su kwata-kwata cewa suka yi, sai dai a yi musu abin da suke so," in ji Tuggar.

Ya ce Ecowas ba ta da matsala da ƴan Nijar kuma ba ta jin daɗin halin da suke ciki.

Ya ƙara da cewa matsalarsu ita ce sojojin da suka kama Shugaba Bazoum suka riƙe, duk da yake suna ganin akwai hanya mai sauƙi ta warware rikicin.

Ministan harkokin wajen Najeriyar ya ce dole ne idan mutane suka yi ba daidai ba a tsawatar musu. A cewarsa, sojojin ma ba yadda suka iya da junansu don kuwa, kowa na ƙoƙarin samun ƙarfin iko a Nijar, inda a gefe guda suka bar ƴan ta'adda na can suna cin karensu babu babbaka.

Matsayar gwamnatin sojin Nijar

Tun bayan juyin mulki a Nijar, sojoji sun bayyana cewa za su shafe aƙalla shekaru uku kafin miƙa mulki zuwa hannun zaɓabɓiyar gwamnatin farar hula.

Gwamnatin sojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdoulrahmane Tchiani ta ce manufar kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum ita ce, tabbatar da tsaro a ƙasar da ke fama da rikicin masu iƙirarin jihadi da kuma ƴan tawaye.

A hirarsa da BBC, Firamista Ali Lamine Zeine ya bayyana cewar takunkumin da ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasar babu adalci a ciki.

"Ba a taɓa yi wa wata ƙasa rashin adalci irin yadda aka yi mana ba, takunkumin da aka saka na hana shigo da magunguna, abinci, da yanke wutar lantarki ga al'ummarmu bai dace ba," in ji Firaministan.

An samu ƙarin munanan hare-hare daga masu iƙirarin jihadi tun bayan da sojoji suka kwace mulki a watan Yuli.

A halin da ake ciki dai, fararen hula a Nijar na ci gaba da fuskantar matsaloli sakamakon takunkumin Ecowas.