Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Isra’ila ta kai mummunan hari a birnin Rafah
Isra’ila ta yi luguden wuta ta sama a kan garin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Falasɗinawa fiye da miliyan ɗaya ke neman mafaka.
Mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa an kai hari ta sama aƙalla sau 50, a tsakiyar dare.
Kakakin rundunar sojin Isra’ilan ya ce sun kuma kuɓutar da biyu daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gazar, a yayin hare-haren.
Rahotannin da suka fara fitowa daga yankin sun ce an kashe mutane fiye da ashirin.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce a yanzu ta ɗan dakata da hare-haren nata, bayan abin da ta kira gagarumar nasarar da ta samu a cikin dare.
Dama dai akwai gargadin da ƙungiyoyi da ƙasashe suka yi cewa Isra’ilan tana shirin kai hari kan birnin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wani waje da ke da tabbacin tsaro ga Falasdinawa, waɗanda yanzu haka suka tattaru a gefe guda na kudancin yankin su.
A ranar Lahadi, shugaban Amurka Joe Biden ya ja hankalin Firaiministan Isra’ila a game da kai hare-hare Rafah ba tare da ɗaukar matakan kare fararaen hula ba.
Fadar White House ta ce a yayin wata hira, Mr Biden ya buƙaci Benjamin Netanyahu ya yi tanadi mai inganci da zai tabbatar da tsaron fararen hula fiye da miliyan ɗaya da ke zaune a birnin.
Shugabannin biyu sun tattauna ta waya ne bayan Mr Biden ya nuna shakku kan halin da fararen hula ke ciki a yankunan da dakarun Isra’ila ke luguden wuta.
A gefe guda kuma, hukumomin Hamas a Zirin Gaza sun ce akwai yiyuwar hare-haren sun kashe dubban Falasɗinawa, kuma sun yi gargadin cewa ci gaba da kai harin zai kawo cikas ga tattaunawar sakin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
A ranar Lahadi, ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce jimillar mutum 28,100 ta tabbatar Isra’ila ta kashe a Gazar, ta kuma raunata wasu 67,500.
Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare a kan Gaza ne, bayan wani hari da Hamas ta kai kudancin Isra’ilan a ranar 7 ga watan Oktoban bara, inda ta kashe mutane fiye da 1,200, ta kuma yi garkuwa da wasu 240.