An faɗa wa kotu jami'an gwamnatin Isra'ila na goyon bayan a ruguza Gaza

An faɗa wa Kotun Duniya (ICJ) cewa ''ƙasar Isra'ila'' da kanta ne ta kuduri aniyar ''wargaza'' Gaza.

Lauyoyin Afirka ta Kudu ne da ke wakiltar ƙasar a shari'ar zargin kisan kare-dangi da take yi wa Isra'ila suka faɗa wa kotun ta ICJ.

Afirka ta Kudun ta kuma buƙaci kotun ta uamrci Isra'ila ta dakatarr da ayyukan sojinta a Gaza.

Ira'ila - wadda za ta kare kanta a ranar Juma'a - ta yi watsi da zarge-zargen tana mai cewa ''ba su da tushe''.

Kotun - wadda al'ummar duniya suka sanya wa idanu - za ta yanke hukunci ne kawai kan zargin kisan ƙare-dangi.

Tembeka Ngcukaitobi, wani lauya a babbar kotun Afrika ta Kudu, ya shaida wa kotun cewa za a fahimci aniyar kisan ƙare-dangin Isra'ila, ''daga hare-haren soji da take ƙaddamarwa''

"Kuma hukumomin ƙasar ne suka kitsa shirin wargaza Gaza'', in ji shi.

"A kowace rana abubuwa ƙara rincabɓewa suke yi, ana rasa rayuka masu yawa, da lalata dukiyoyi da toshe ayyukan jin-ƙai kan Falasɗinawa,'' in ji Adila Hassim, wadda ita ma ke wakiltar Afirka ta Kudu a lokacin da take faɗa wa kotun.

"Babu abin da zai dakatar da waɗannan wahalhalu da suke ciki, in ba umarnin wannan kotu ba."

A cikin wata shaida da ta aika wa kotun gabanin fara sauraron shari'ar, Afirka ta Kudu ta ce ayyukan Isra'ila sun nuna cewa ''tana shirin wargaza wani wagagen ɓangare na ƙasar Falasɗinawa da ƙabila da kuma al'ummar Falasɗinawa''.

A ranar Juma'a ne Isra'ila za ta kare kanta a gaban kotun, to amma a baya ta sha cewa tana da hujjar ayyukan sojinta a Zirin Gaza saboda tana mayar da martani ne kan mummunan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba.

Amma yayin da yake magana a gaban kotun ranar Alhamis, ministan shari'ar Afirka ta Kudu Ronald Lamola ya ce babu harin ''da za iya kafa hujjar aikata shi ko kuma domin kare keta yarjejeniyar hana kisan-ƙare dangi.

Isra'ila na daga cikin ƙasashen da suka rattaɓa hannu a yarjejeniyar kisan-kiyashi ta 1948, wadda ta yi magana kan kisan kiyashi tare alƙawarta hana aikata shi.

Kotun ta ICJ ita ce babbar kotun MDD, wadda ke da matsuguni a birnin Hague na ƙasar Netherlands. Bisa tsarin doka dole ne ƙasashen - da suka amince da samuwarta, ciki har da Isra'ila da Afirka ta Kudu - su yi biyayya ga hukuncinta - to amma ba za a iya tilasta wa ƙasa ta bi hukuncin ba.

A shekarar 2022, kotun ta umarci Rasha ta ''gaggauta dakatar da mamayar soji'' a Ukraine, wani umarni a Moscow ta ki yin biyayya gare shi.

A ƙarƙashin dokokin duniya kisan ƙare-dangi na nufin aikata wani abu ko abubuwa da nufin ruguza gaba ɗaya ko wani ɓangare na ƙasa ko ƙabila da gungun wasu mutane da wani addini.

An samu dandazon mutane a harabar ginin kotun, da aka fi sani da fadar "Peace palace'', yayin da 'yan sandan Netherlands suka yi ta yunƙurin raba magoya bayan Falasɗinawa da da na Isra'ila.

Daruruwan mutane ne da suka taru a harabar kotun suka riƙa ɗaga tutar Falasɗinawa tare da kiran tsagaita wuta.

Magoya bayan Isra'ila sun yi ta nuna hotunan mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.

An girke tarin jami'an 'yan sanda a harabar ginin kotun, a wani yunuri na kwantar da tarzomar da ka iya tashi a lokacin sauraron shari'ar.

A cikin kotun kuwa, wakilan Isra'ila sun saurari lauyoyin Afirka ta Kudu yayin da suke gabatar da zarge-zargen da suke yi wa dakarun Isra'ilar na aikata kisan kare-dangi a Gaza.

Ana san ran wakilan Isra'ila za su gabatar da 'yancin ƙasar na kare kai ƙarƙashin dokokin duniya.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ba ta da niyyar raba mutanen Gaza da muhallansu ko mamaye musu yankunansu.

Saɓanin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC, ita Kotun Duniya ta ICJ ba za ta tuhumi wani mutum shi kaɗai ba da irin wannan zargi na kisan ƙare-dangi, amma hukuncinta na da ƙarfi a Majalisar Dinkin Duniya da sauran cibiyoyin duniya.

A ranar Laraba, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce ''rashin amincewarmu kan kashe-kashe da ake yi wa al'ummar Gaza ne ya sa muka garzaya Kotun Duniya''

Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya kira zarge-zargen da ''wata aika-aika ce da ta saɓa wa hankali''.

"Za mu je Kotun Duniyar, kuma za mu gabatar da hujjarmu na kare kai... a karƙashin dokokin duniya,'' in i shi.

Ya ƙara da cewa sojojin Isra'ila ''na aiki ne ƙarkashin wani yanayi mai wahala, inda suke kutsawa cikin Gaza da nufin tabbatr da cewa ba su cutar da fararen hula ba''.

Caroline Glick, wani tsohon mai bai wa firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce wannan ''ta ci karo da ɗa'a da batun da hankali zai yarda da shi''

Zane Dangor, Babban darakta a ma'aikatar kula da lamuran ƙasashen waje na Afirka ta Kudu ya shaida wa BBC cewa zarge-zargen kisan kiyashi da ake yi wa Isra'ila ''manyan zarge-zarge ne''.

Ya bayyana ƙarar da Afirka ta Kudun ta shigar a matsayin ''wani babban abin la'akari''. Inda ya yi Allah wadai da harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai wa Isra'ila, yana mai cewa babu '' wata hujja da za a dogara ta ita wajen kashe-kashen'' da ake aikatawa a Gaza.

Koun ICJ za ta iya gaggauta yanke hukunci kan bukatar Afirka ta Kudu ta na buƙatar Isra'ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa Gaza, amma hukuncin ƙarshe na cewa ko Isra'ila ta aikata kisan ƙare-dangi zai iya ɗaukar shekaru.

Mece ce ƙarar kisan ƙare-dangi da aka shigar da Isra'ila?

Afirka ta Kudu ta shigar da ƙara ne a gaban Kotun Duniya tana zargin Isra'ila da 'ayyukan kisan ƙare-dangi'.

Afirka tana matuƙar sukar lamirin hare-haren da sojojin Isra'ila suke kai wa Gaza, kuma jam'iyyar ƙasar mai mulki ta ANC tana da dogon tarihin goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa.

Tana kallon kamanceceniya da gwagwarmayar da ta yi a kan mulkin wariyar launin fata - wata manufar gwamnati ta ware mutane saboda launin fatarsu da kuna nuna bambanci wadda gwamnatin tsirarun fararen fata ta yi amfani da ita a Afirka ta Kudu a kan baƙaƙen fata masu rinjaye, kafin zaɓukan dimokraɗiyya na farko a 1994.

A Gaza, an kashe mutane sama da 23,350 - akasari mata da ƙananan yara, in ji ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon Hamas, tun da aka fara yaƙin bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba a kudancin Isra'ila. A hare-haren, an kashe mutum aƙalla 1200 - akasari fararen hula - sannan an kwashi ƙarin mutum 240 don yin garkuwa da su.