Abin da ake nufi da kisan kare-dangi

Danna hoton da ke sama domin kalon bidiyon:

Shugaban Amurka Joe Biden ya zargi Rasha da aiwatar da kisan kare-dangi sakamakon yakin da ta kaddamar a Ukraine.

Sai dai gwamnatin Moscow ta yi watsi da wannan zargi.

Amma me ake nufi da kisan kare-dangi, shin an taba hukunta wani ko wasu sakamakon aikata kisan kare-dangi?