Man United: An karɓe mukamin kyaftin daga wajen Maguire

Harry Maguire ya ce Erik ten Hag ya karɓe mukamin kyaftin ɗin Manchester United daga wajensa.

Ole Gunnar Solskjaer ne ya naɗa Maguire a Janairun 2020, wata biyar tsakani da United ta sayo mai tsaron bayan daga Leicester City kan fam miliyan 80.

Mai tsaron bayan tawagar Ingila ya ce bai ji dadi kan wannan hukuncin ba, amma zai ci gaba da bayar da gudunmuwa kamar yadda ya saba a United.

Mai shekara 30, wanda ya yi wasa takwas a kakar Premier League ta 2022/23, ana alakanta shi da zai koma West Ham da taka leda.

Maguire ya buga wa United karawa 31 daga 62 da kungiyar ta yi a kakar da ta wuce, inda Bruno Fernandes ke daura kyallen kyaftin idan Maguire bai yi wasa ba.

Maguire yana da yarjejeniya tare da kungiyar Old Trafford da za ta kare a karshen kakar 2025.

Maguire ya ce ''Ina mika godiya mai tarin yawa ga magoya bayan United kan yadda suka maramin baya a lokacin da nake kyaftin din kungiyar.

''Tun daga ranar da aka bani kyaftin din United shekara uku da rabi da ta wuce, martaba ce a waje na, domin jan ragamar 'yan wasan kungiyar da ta yi fice a duniya a tamaula - har yanzu ban mance da ranar ba''.

Manchester United wadda ta yi ta uku a Premier League a kakar 2022/23 za ta buga Champions League a bana, bayan karawa a Europa League a bara.