Mun gaji da gafara 'sa' kan matsalar tsaro — NLC

Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar ƙwadado ta NLC a Najeriya, ta ce za ta gudanar da zanga-zangar lumana ta gama-gari, a fadin ƙasar saboda abin da ta kira ƙara tabarbarewar lamuran tsaro a ƙasar.

NLC ɗin ta ce ta na son ganin gwamnati ta ƙara ɗaukar matakan tsaro, domin dakile wannan lamarin na tsaro a ƙasar baki ɗaya .

Comrade Nasiru Kabiru, shi ne sakataran tsare-tsare na ƙungiyar ta NLC, ya shaida wa BBC cewa za su yi zanga-zangar ce saboda nuna bacin ransu akan yadda ɓangaren tsaro ya taɓarɓare.

Ya ce," Idan kaje arewacin Najeriya tun daga jihohi Borno da Yobe da Zamfara da Sokoto da Kebbi, dukka dai yawancin waɗannan wurare na fama matsalar tsaro, haka idan kaje kudancin Najeriya ma haka lamarin ya ke."

"Mun yi ta kiraye-kiraye akan gwamnatin tarayya ta tashi tsaye a kan wannan matsala ta tsaro tun da ana kashe dumbin ma'aikatanmu da 'yan Najeriya dama talakawan ƙasar, to amma shiru kake ji babu wani abu da ya sauya." In ji shi.

Comrade Nasiru Kabiru, ya ce," wajibi ne gwamnati ta bawa al'umma tsaro saboda hakki ne da ya rataya akanta."

Ya ce," Idan har Najeriya na da jami'na tsaron da za su je Jamhuriyar Benin don dakatar da juyin mulki, me zai hana su jami'na tsaron su fara magance ta su matsalar data addabi ƙasarsu, domin batun magance matsalar tsaro a Najeriya ai ya fi batun dakile juyin mulki a wata ƙasa."

" A don haka dole ne mu nuna wa gwamnati bacin ranmu kuma wannan shi ne karo na shida da muka fito muke zanga-zanga akan matsalar tsaro, ƙasar da za ace wai ɗan ta'adda na karɓar haraji ai babu gwamnati." In ji shi.

Sakataran tsare-tsare na NLC a Najeriya, ya ce," Mu babban abin da muke so gwamnatin Najeriya ta yi akan wannan matsala ta tsaro shi ne ta ayyana dokar ta baci akan tsaro, sannan kuma a kawo shi kashen matsalar cikin gaggawa sannan muna so mu gani a kasa na kawo karshen matsalar tsaron data addabi ƙasar."

To sai dai a cikin daren jiya shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya yi wata ganawa da shugabannin ƙwadagon a cikin daren jiya a fadarsa inda a karshenta shugaban ƙungiyar NLCn Joe Ajaero ya shaidawa manema labarai cewa za su tattauna da sauran rassan ƙungiyar domin duba ko za yi zanga-zangar ko a'a.