Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko yajin aikin Pengassan zai haifar da ƙarancin man fetur a Najeriya?
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Rikici ya rincabe tsakanin matatar man fetur ta Dangote da ƙungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin iskar gas da fetur, inda lamarin ke ƙara daukar sabon salon da tasirinsa zai iya shafar gwamnati da dukkan 'yan Najeriya kai-tsaye.
Ƙungiyar Petroleum and Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENGASSAN) ta sanar da fara yajin aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Dangote na korar wasu ma'aikatanta kimanin 800.
A cewar sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, yajin aikin ya ƙunshi katse duk wata hanya da matatar ke samun ɗanyen mai da kuma iskar gas domin tacewa.
A nata bangaren, matatar Dangote cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana matakin a matsayin “rashin aiki da doka da kuma zagon-kasa ga Najeriya da al’ummarta".
Matatar ta bukaci al’umma da gwamnatin Najeriya su bijire wa umarnin PENGASSAN
Tun kafin haka wani ɗan kwamatin zartarwa na ƙungiyar, Injiniya Dauda Adamu Ali, ya faɗa wa BBC cewa sun umarci mambobinsu a kamfanonin da ke haƙo mai da sarrafa gas da su hana tura wa Dangote makamashin.
Yanzu kuma ƙungiyar ta umarci mambobin da su dakatar da aiki gaba ɗaya a dukkan kamfanoni da ma'aikatu.
"Dukkan mambobin PENGASSAN da ke aiki a ofisoshi, da kwamatoci, da wuraren haƙo makamashi da za su jingine aiki daga ranar Lahadi 28 ga watan Satumba," a cewar Mista Okugbawa.
"Sannan kuma za a shirya taron addu'o'i a lokaci guda," in ji shi.
Umarnin ya ce su kuma ma'aikatan da ke aiki a ofisoshi da ma'aikatun gwamnati za su dakatar da aiki ne daga safiyar Litinin 29 ga wata.
Ko yajin aikin Pengassan zai haifar da ƙarancin fetur?
Game da ko yajin aikin ma'aikatan ƙungiyar Pengassan zai sanya a samu ƙarancin man fetur a Najeriya, shugaban ƙungiyar Pengassan Festus Osifo ya ce ayyukan ƴaƴan ƙungiyar bai haɗa da rarraba man fetur a faɗin ƙasa ba, saboda haka nan ba za a samu ƙarancin man fetur nan take ba.
"Mafi yawan aikin Pengassan na faruwa ne a wurin haƙowa da sarrafa man fetur da gas. A yanzu haka akwai matatar Dangote da kuma sauran manyan tankunan adana man fetur akwai isasshen man fetur da zai iya wadatarwa har na tsawon kwana 30.
"Saboda haka ba zai shafi wannann ɓangaren ba," in ji Osifo a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a yammacin ranar Lahadi.
Aukawa cikin duhu da hana gwamnati kuɗin shiga
Sai dai ɗaya daga cikin mummunan tasirin da rikici tsakanin ɓangarorin biyu zai yi a Najeriya shi ne jefa ƙasar cikin duhun lantarki.
Jaridar Punch ta ruwaito sakatariyar ƙungiyar masu kamfanonin samar da lantarki a Najeriya ta Association of Power Generating Companies (APGC) tana sanar da cewa masu samar musu da gas sun sanar da dakatar da jigilar gas ɗin zuwa tashoshin samar da lantarki masu amfani da gas, abin da ka iya jefa 'yan Najeriya cikin duhu.
"Kamfanonin samar da lantarki a tashoshin da ke aiki da gas sun samu sanarwa daga masu samar mana da gas cewa sun dakatar da aiki saboda yajin aikin da PENGASSAN ta kira," a cewar Joy Ogaji cikin wani saƙo a dandalin WhatsApp ranar Lahadi.
A cewar rahoton, Ogaji ta bayyana cewa kamfanin da ke kula da harkokinsu na Nigerian Gas Infrastructure Company ya umarci kamfanoninsu da ake kira GenCos su bi umarnin ƙungiyar PENGASSAN.
Najeriya na da tashoshin samar da lantarki kimanin 20 da ke amfani da iskar gas, kuma su ne ke samar da kusan kashi 80 cikin 100 na lantarkin da ake rarrabawa a duka faɗin ƙasar.
Tashoshin da ke amfani da ruwa kuma uku ne kacal, waɗanda ke samar da kashi 20 cikin 100 kacal na lantarkin ƙasar. Su ne Kainji, da Jebba, da kuma Shiroro - duka a jihar Neja.
A ɓangaren gwamnati kuma, lamarin zai iya jawo wa tattalin arzikin Najeriya babban cikas.
Duk da cewa gudummawar da fannin man fetur da makamashin gas ke bayarwa wajen juyawar arzikin cikin gida a Najeriya ba ta da yawa, shi ne ɓangare mafi girma da gwamnati ta dogara da shi wajen samun kuɗin shiga.
Bayanai daga ƙungiyar da ke sa ido kan fannin haƙo ma'adanai ta ƙasa da ƙasa Extractive Industries Transparency Initiative (EITI) sun nuna cewa ɗanyen mai da gas ne ke samar wa gwamnatin Najeriya kusan kashi 65 cikin 100 na kuɗaɗen shiga, da kuma sama da kashi 85 cikin 100 na kayayyakin da take fitarwa ƙasashen waje.
Wani sharhi da cibiyar nazarin harkokin tattalin arziki da zamantakewa ta Najeriya Nigerian Institute Of Social And Economic Research (Niser) ta wallafa ya ce ɓangaren mai da gas ne zai samar wa gwamnatin Najeriya kashi 56 cikin 100 na kuɗaɗen da za ta kashe a kasafin kuɗinta na 2025.
Idan wannan yajin aiki ya ɗore lallai gwamnatin Najeriya za ta yi asarar miliyoyin dala a kowacce rana.
Kazalika, akwai yiwuwar yajin aikin ya shafi harkokin sayar da man fetur a gidajen mai, kasancewar ƙungiyar PENGASSAN ce babbar ƙungiyar ma'aikatan da ke aikin turawa da saukewa da lodin tataccen man.
Sai dai babu tabbas kan ko mambobin ƙungiyar na da tasirin da za su iya shafar samuwar mai a ɗaiɗaikun gidajen mai da ke faɗin Najeriya.
Musabbabin rikici tsakanin Dangote da PENGASSAN
A ranar Alhamis ne rahotanni suka fara ɓulla cewa matatar ta Dangote da ke Legas ta sallami ma'aikata fiye da 1,000 bisa zargin shiga ƙungiyar ta PENGASSAN, wadda ta ƙunshi ma'aikatan kamfanonin mai da iskar gas ta Najeriya.
Bayanai da BBC ta samu daga wasu ma'aikatan da aka kora sun nuna cewa kamfanin ya kore su ne saboda sun ce za su shiga ƙungiyar.
"Sun ce sun kore mu ne saboda mun shiga ƙugiyar PEGASSAN. Sanarwar da suka fitar cewa wajen ma'aikata 3,000 za su ci gaba da aiki kuma wai suna yi wa kamfanin garambawul ne, ƙarya ce kawai. Suna so ne kawai su samu tausayi daga al'umma, kuma babu maganar ko za a biya nu kuɗin sallama," kamar yadda wata daga cikin ma'aikatan da aka kora ta faɗa wa BBC.
Sai dai cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, kamfanin na Ɗangote ya musanta dalilin da suka bayar, inda ya ce ya yi korar ne bisa tuhumar su yi wa matatar zagon ƙasa.
Sanarwar ta ƙara da cewa har yanzu akwai ma'aikata fiye da 3,000 da ke ayyukansu a kamfanin.
Wata majiya daga matatar ta shaida wa BBC cewa mafi yawan mutanen da kamfanin ya sallama wadanda suka shiga ma'aikatar ne a matsayin masu neman horo wato trainee bayan zaɓo su daga jami'o'i daban-daban, kuma suka zama ma'aikata daga baya.
"Yawancin ma'aikatan sun fara aiki ne a kamfanin tun daga fitowarsu daga jami'a. Mafi yawansu ɗalibai ne da suka fi hazaƙa bayan sun fita da sakamako mafi kyawu," In ji wani ma'aikacin da bai so a ambaci sunansa ba.