Matan Iran da ke zanga-zangar ƙin jinin tilasta sanya Hijabi

Mata a Iran sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsauraran ka'idojin sanya hijabi a kasar, inda suka riƙa cire gyalensu a bainar jama'a tare da yaɗa hotunan a shafukan sada zumunta.

"A'a ba mu amince da tilasta mana sanya hijabi ba! Na tuƙa mota har zuwa aiki ba tare da sanya ko gyale ba yau don na nuna ƙin amincewa da wadannan dokoki.

"Burinmu shi ne mu samu 'yancin zaɓar abin da za mu saka", kamar yadda wata mata da aka naɗi bidiyonta aka saka a intanet ke cewa.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun bukaci mata a fadin kasar su rika yaɗa bidiyon da suka ɗauka suna cire hijabi ko mayafai don yaɗawa a intanet.

Domin ya zo daidai da ranar 12 ga watan Yuli, wato ranar Hijabi da tsafta ta kasa a kalandar ƙasar Iran.

Mutane da dama ne suka amsa kiran, duk da haɗarin da ke tattare da hakan.

Mata a sassa daban-daban na kasar sun yi ta yin bidiyon ɗauki-da-kanka, wato selfie a wuraren shakatawa, da titunan birnin har ma da bakin teku, inda suke nuna kansu ba tare da hijabi ba, wasu suna sanye da rigar shan iska ta bazara da gajeren wando.

A wani bidiyo da dubban mutane suka yada, ana iya ganin wata mata tana tafiya a kan hanyar ruwa, sannan ta cire hijabinta, ta bar shi ya fadi kasa, sannan ta shure shi ta tafi.

A dai wannan rana, hukumomi sun shirya taron jama'a ga mata masu sanye da hijabi don murnar "kariyar da Musulunci ya ba su".

Gidan talbijin din kasar ya nuna bikin da aka gudanar da ya nuna dumbin mata sanye da hijabai da dogayen fararen riguna.

Wasu matan sun yi Allah-wadai da mazan da suke rike da madafun iko da suke daukar wadannan matakai da suke kallo a matsayin tauye musu damarmakinsu.

Wata mata a Iran da ke cikin masu nuna kin amincewa da wadannan sabbin dokoki ta ce da yawan irin wadannan maza na kallonsu a matayin mutanen da ba su sanciwn kansu ba, mutanen da ba su da wani ƴanci, da za a iya musu duk shan kan da aka so.

An kama kamar mata biyar da suka yaɗa bidiyonta tana wadannan kalamai.

Ba wannan ne karon farko da aka saba irin wannan zanga-zanga ba a Iran, inda mata ke son ganin ana ba su damar sanya irin tufafin da suke so.

Sai dai wani mataki na baya-bayan nan da 'yan sanda a Iran suka dauka kan mata da ake zargi da kin bin ka'idojin tufafi ya sa masu adawa da manufar yin kira da a dauki mataki.

Tun bayan juyin juya halin Iran a shekara ta 1979, aka fara tilasta wa mata sanya tufafin "Musulunci".

Wasu mazan Iran ma suna goyon wannan fafutuka a shafukan sada zumunta, suna fitowa a bidiyo tare da matan da ke zanga-zangar.

An yi yada hoton da ke nuna katangar wani masallaci a birnin Tehran da ke dauke da sakon cewa: "yanci, zabar suturar da mutum ke so, shi ne dai-dai

Shugaban hukumar shari'a ta Iran, Gholamhossein Mohseni Ajeei, ya ce wasu kasashen waje ne ke da hannu a fafutukar, inda ya umurci hukumomin leken asirin da su gano masu hannu.

Shugaban kasar Ebrahim Raisi ya kuma yi alkawarin murkushe ayyukan cin hanci da rashawa a fadin kasar, a wani abu da ake kallo a matsayin habaici ga mas zanga-zangar.

Sai dai mata da dama sun kuduri aniyar ci gaba da zanga-zangar duk da barazanar da ake fuskanta.

"Za ku iya kama mu, amma ba za ku iya dakatar da fafutukarmu ba, " in ji wata mata a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

 "Ba mu da wani abu da za mu yi nasara, mun rasa 'yancinmu shekaru da suka wuce, kuma muna da'awar dawowa."