Ranar Hijabi ta Duniya: 'Abin da hijabi ke nufi a wurinmu'

Ku latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyo

A kowace ranar 1 ga watan Fabrairu, mata Musulmi a duniya na bikin ranar a matsayin ranar sanya Hijabi ta duniya.

Matashiyar Musulma, Nazma Khan 'yar Amurka ce ta kirkiro wannan rana a shekarar 2013, bayan da aka kai harin 9/11 a Amurka.

Tun bayan harin ne matashiyar da sauran 'yan uwanta Musulmai suka shiga cikin tasku sakamakon kyamar Musulmi da ta karu a tsakanin Amurkawa.

Yanzu haka dai ana bikin ranar ta Hijabi a kashe 140 daga cikin kusan 200 a fadin duniya.

Mai rahoto: Khadijah Nasidi

Mai daukar hoto: Abdulsalam Usman