Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna sane da matsalolin duba sakamakon zaɓe ta intanet – INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce tana sane da irin ƙalubalen da ake fuskanta a ƙoƙarin duba sakamakon zaɓen da hukumar ke ɗorawa a shafinta na intanet.
INEC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Tuwita inda ta ce shafin da ake kira IReV na ɗaukan ƴan mintuna kafin ya nuna sakamakon zaɓen.
Hukumar ta kuma nuna takaicinta kan irin koma-bayan da ake samu musamman la'akari da muhimmancin shafin a tsarin bayyana sakamakon zaɓen ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba.
INEC ta alaƙanta hakan ga yunƙurin da ake na inganta shafin ta yadda za a iya ganin sakamakon babban zaɓe.
A cewar hukumar, lamarin ba shi da wata alaƙa ga ƙoƙarin yi wa shafinta kutse. Ta kuma ce ma'aikatanta sun duƙufa domin magance duka matsalolin da ake fuskanta.
Ta kuma ba da tabbacin cewa shafin nata ba ya fuskantar wata barazana inda kuma INEC ɗin ta ce "masu amfani da shafin za su iya lura da irin ci gaban da aka samu daga daren jiya zuwa yanzu."
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Festus Okoye, ɗaya daga cikin kwamishinonin hukumar, ta sake tabbatar da cewa duka sakamakon zaɓen da aka ɗora a shafin na da sahihanci kuma idan aka samu banbanci a sakamakon da yake jikin na'urar BVAS da shafin IReV, hukumar za ta tantance ta kuma yi nazari a kai bisa tanadin sashe na 65 na dokar zaɓen 2022.