Kenya ta haramta fasa-kaurin bishiyoyin kuka zuwa kasashen waje

Asalin hoton, Getty Images
Kenya ta soke lasisin da ta bai wa wani kamfanin kasar waje na cirewa da kuma fitar da bishiyoyin kuka zuwa kasashen ketare daga yankin da ke gabar teku bayan mutane sun rika korafi.
Kamfanin da ke kasar Georgia ya sayi manyan bishiyoyin kuka takwas daga wurin manoma.
Masana harkokin muhalli sun bayyana shirin fitar da bishiyoyin da "fasa-kauri".
Ministan muhalli ya ce masu cire bishiyoyin kukar ba su samu izinin yin hakan kamar yadda ya dace ba. Kuka dai kan kwashe fiye da shekaru 2,500 years kafin ta mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu manoma a Kilifi suna so a cire dukkan bishiyoyin da ke yankin domin su samu damar shuka masara.
Sun sayar da bishiyoyin kukar a kan $800 (£670) zuwa $2,400, a cewar jaridar Guardian.
Babu cikakken bayani game da yawan shekarun bishiyoyin, amma hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda ake cire rassa da gangar jikin bishiyoyin na kuka.
"Mun amince cewa ba za a fitar da bishiyoyin kuka kasashe waje ba har sai an kulla yarjejeniya tsakanin bangarorin da ke da ruwa da tsaki a kansu," kamar yadda Ministan Muhalli da Gandun Daji Soipan Tuya ya bayyana ranar Litinin.
Sanarwar da ministan ya fitar ba ta bayyana ko an cire dukkan bishiyoyin kukar takwas ba, sai dai ta kara da cewa za a dauki mataki kan jami'an da suka bayar da umarnin sayar da bishiyoyin.
A watan Oktoba shafin intanet na jaridar UK Guardian ya rawaito cewa an saka bishiyoyin kukar da aka yi gunduwa-gunduwa da su a cikin wasu keji a Kilifi sannan aka sanya masu gadi suna gadinsu kafin a fitar das su kasashen ketare.
Bayanai sun nuna cewa ana kai bishiyoyin wani dakin bincike kan bishiyoyi da ke Georgia
Kazalika ana kasuwancin bishiyoyin kuka a Australia da Afirka ta Kudu. Ana fargabar cewa cire bishiyoyin kuka zai yi mummunan tasiri kan kwari da tsuntsaye da dangin kadangaru.
Bishiyoyin kuka suna da sinadaran vitamin C, calcium, potassium da faiba.
Kazalika ana amfani da bawonsu wajen yin maganguna da kayan kwalliya.











