Me ya sa Amurka ta ƙi kiran hamɓarar da Bazoum, juyin mulkin soja?

Some Nigerien soldiers mounting an armoured vehicle

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojoji sun ƙwace iko a Nijar cikin watan Yuli kuma tun lokacin ne suke tsare da Shugaba Bazoum Mohamed

Idan ya kasance tamkar juyin mulki, tafiyarsa irin ta juyin mulki haka ma ƙararsa, to ya zama juyin mulki ke nan ko kamar yadda ake faɗi.

Waɗanda suka san juyin mulki a Afrika sun san tsarinsa.

Bayanin da wasu taron sojoji suka yi a gidan talabijin na ƙasar ya kawo ƙarshen jita-jita da kuma tabbatar da cewa sun ƙwace iko, abin da ya haifar da murna a kan manyan tituna.

Daga nan an yi ta samun martani daga ƙasashen duniya - mafi yawa tir da Allah wadai da juyin mulkin tare da kiran a mayar da iko ga shugabannin dimokuraɗiyya.

Wannan ita ce matsalar da Nijar ta samu kanta ciki tun bayan da sojoji suka kifar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli tare da tsare shi.

Ƙungiyar ECOWAS da Tarayyar Turai da Faransa duka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin tare da ɗaukar matakai masu tsauri domin magance matsalar.

Amurka ma ta yi tir sai dai ta kiyaye sosai wajen amfani da kalmar juyin mulki.

Maimakon hakan, sai ta riƙa amfani da kalmar "yunƙurin juyin mulki" da kuma "yunƙurin ƙwace mulki da ƙarfi" daga shugaban siyasa da aka zaɓa Mohamed Bazoum, tana cewa ba za ta iya jurar ganin ana tafiya ba kan tsarin da ya saba wa kundin tsarin mulki.

"Har yanzu Bazoum ne shugaban ƙasar", in ji Vedant Patel mataimakin kakakin ma'aikatar cikin gida ta Amurka. "Bai yi murabus ba har yanzu."

Yadda Amurka ke zaɓar kalmomin da take amfani da shi yana da matuƙar tasiri.

Da Bazoum zai yi murabus a hukumance ya kuma miƙa mulki ga waɗanda suka yi ƙoƙarin juyin mulki, hakan zai sa Amurka ta ƙulla alaƙa da sojojin.

Salon mulkin dimokuraɗiyya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun daga nan sojojin suka yi umarnin sake sabuwar jakadiyar Amurka a Nijar ɗin Kathleen FitzGibbon, tana barazanar kan alaƙar da ke tsakaninsu.

Tun daga 2012, Amurka ta kashe aƙalla dala miliyan 500 a Nijar, wajen taimaka mata a yaƙin da take yi da masu iƙirarin jihadi a ɓangaren Sahel, inda aka tabbatar ƙungiyoyin da ke kai hare-hare a yankin suna da alaƙa da al-Qaeda da kuma IS.

Nijar ita ce ƙasar da ta fi samun taimakon sojin Amurka a Yammacin Afrika, kuma ita ce ƙasa ta biyu mafi girma a yankin Sahel.

Akwai sansanin sojin Amurka na sojin sama da ake kira Air Base 201 a Nijar da ke Agadez da ke arewacin ƙasar, Sai kuma na Air Base 101 da ke Yamai babban birnin ƙasar.

Wannan ya sa sojojinta suka kai 1,100 a ƙasar.

Amurka ta kai kayan aikin soji da jirgin yaƙi a ƙasar tare da bayar da horo ga sojojinta.

Washington na ganin ƙimar da ta dace ga ƙawarta a Yamai, wanda hakan ya sa aka fahimci matakin barazanar da Amurka ke jura a yankin.

A watan Maris, Anthony Blinken ya zama Sakataren harkokin wajen Amurka na farko da ya ziyarci Nijar, inda ya bayyana ƙasar a matsayin "sabuwar fuskar dimokuraɗiyya a yankin da ke fuskantar matsaloli a yanzu."

Wannan wata hujja ce ba wai tsantsar ingancin dimokuraɗiyyar da ake da ita ba a Nijar, ko kuma ta-zarce abin da ake da shi a ƙasa.

Zaɓen Shugaba Bazoum da ya karɓi mulki a hannun wanda ya gada Mahamadu Issoufou a 2021, shi ne na farko a tarihin dimokuraɗiyyar Nijar da farar hula ya miƙa wa farar hula mulki.

Za a ga kamar ba wani abun a yaba ba ne, amma idan aka yi la'akari da tsarin yankin da kuma Nijar abin a yi guɗa ne.

A ƙasashen Guinea da Mali da Burkina Faso da Chadi da kuma Sudan dukkan su sojoji ne ke mulki.

Da yawa daga cikin waɗannan ƙasashen na fuskantar matsalar masu iƙirarin jihadi, wanda hakan ne dalilin zuwan sojojin Amurka a Nijar, kuma shi ne dalilin atisayen da take yi irin na su Flintlock, wani shiri na musamman da yake bai wa dakaru daga ƙasashen Afrika 30 horo.

Amurka na buƙatar abokan hulɗa na kusa domin daƙile yawa da kuma ci gaba da yaɗuwar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da wannan ɗabi'a da ke barazana a yankin da kuma mutanen Amurka da muradun yankin.

A watan Maris, jami'an tsaron Amurka tare da takwarorinsu na Najeriya suka yi aiki tare domin kuɓutar da Jeffery Woodke, wani ma'aikacin agaji na Amurka wanda aka tsare shi a wani mtsallacin Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wani sansanin al-Qaeda da ke yankin.

An sace Woodke a gidansa da ke Nijar a 2016, kuma shi ne ɗan Amurka na uku da aka yi garkuwa da shi cikin shekara uku a ƙasar.

Amma dai Amurka na shan suka saboda tasirin da wataƙila matakin nata zai iya yi a yankin.

Cikin waɗanda suke fafutukar ƙwace mulkin ya koma wajen sojoji a Yammacin Afirka har da ɗaliban da Amurkan ta horas.

Janar Abdourahmane Tchiani, shugaban sojin da suka yi juyin mulki a Nijar, wanda a 2009 aka zaɓa domin samun horo kan yadda za a magance matsalar 'yan ta'adda.

Mamady Doumbouya da Assimi Goïta waɗanda su ne shugabannin juyin mulki a Guinea da Mali, su ma sun samu horo daga sojojin Amurka.

Juyin mulkin Nijar - ko ma dai duk yadda Amurka ke son kiran shi - ya bayyana irin matsalar da Amurka ke fuskanta ta ƙoƙarin tallata dimokuraɗiyya a Afrika.